← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 144

Sashe 103

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kawai sai naji kamar ba Duniyan da muke ciki nake ba wasu surutai nake ji a sanan kaina kamar kaina zai Fashe Wata gigitaciyar Dariya ta kara firgitani kamar ana yinta acikin Bangon Falon,Sai naji Hayaniyar tv ta rikice ta koma Dariya da ihu wani irin ihu mara Dadin da Har Abada bana Fatan ko makiyina ya ji sa ba ballatana Masoyina,shure shure nake ina so na Kira sunan wasila na kasa ji nayi kamar kuma an shake ni an yi sama Dani ina Lilo tsakanin Sama da kasa Numfashina na barazanar barin gangar jikina Dariya nake ji wata irin Muguwar Dariya da wata murya da jinta ma tashin Hankali ne da kunnena naji sanda muryan tayi mgana mganar daga Lokacin ban kara sanin inda kaina yake ba Ji nayi ana fadin.

"Kin cika Taaurin kai...Ki tafi cikin Salama kin ki tafiya..Zaki Mutu..Zaki Muuuutuuuu...!

Daganan sai naji kamar an yi cilla dani na Daki bango na Dawo na Zube a kasa sama sama kuma naji Muryan Wasila tana Fadin"Anty kina ina..?

Duhu yayi yawa sun Dauke wuta ne..?

Daganan sai naga gilmawar Haske a Idona da kuma kara mganar Wasila tana Fadin"Eyy Nepa sun maido wuta"
Daganan idanuwana da jina suka Dauke gabadaya sai Farkawa nayi na ganin a saman gado na wasila na gefe daga ganinta taci kuka har ta koshi a Zabure na farka naji bayana da kuguna da Hannayena suna ciwo ammh ban damu ba mikewa nake shirin yi wasila ta rikeni tana Fadin"Anty kin farka..?

Kallonta nayi da jajayen idanuwana Cikin Fitan Hayyaci kafin nace"Wasila kema kin ganta ko..?

Wlh in bamu bar gidan nan sai ta kashemu gabadayan mu"
Na fada cikin yanayin da kana gani zaka san bana cikin Hayyacina.

Wasila ta fashe da kuka tana Fadin"Anty ni fa ban ga kowa ba kawai na fito ne saboda an dauke wuta ina ta kiranki baki amsa ba sai gashi nepa sun dawo da Wuta ina Dubaki sai na ganki chan gefe kwance kin suma ruwa na yayyafa miki kika Farfado kadan na samu na kamaki kika mike na shigo dake ciki"
Sai alokacin komai ya rika Dawomin cikin kaina Tabb
as wannan karon a zahiri komai ya faru ba kamar baya da nike ganin kamar a mafarki ba.

Mikewa nayi da karfi sai alokacin na Kalli madubin dake gabana goshina ya Kumbura,sumtum sannan wuyana ga Shedar a kaifa nan da suka shiga Cikin Fatata,Jikina ya fara rawa na Fara Dube duben jikina ina Fadin"Wasila kin gani ko..?wlh zata kasheni itace tamin wannan Tabon fa..?

Na fada ina nuna mata tasowa tayi tana kallona kafin tace"Ni fa ban ga komai ba Anty"Sai na Dankare na kara bin kaina amadubi da kallo na kuma ga Ciwon da na samu na kara kallon wasila ina Fadin"Kikace baki ga komai ba..?

Kai ta gyadamin tana Fadin"Anty kin Tsorata ne Allah ba kowa agidan nan sai mu kadai"
Kallonta nake yi kamar wata wacce ta zare ganin bazata Fahimceni ba yasa nace mata"Ina Wayata wasila..?.

Nemin wayata ki Dauko min wayata"
Na fada cikin Tsawa da Fitar Hayyaci Fita falo tayi tana Fadin"A falo kika barta Anty"
Kamar kada wasila ta fita sai naji kamar iska ya wuce ta saman kafadana ina juyawa baya kuma ban ga komai ba sai na Dawo da kallo na ta gaban Madubi yadda na Zabura ne nayi gefe ina rawan jiki yasa naji kaina yayi mummunan sarawa wlh ita na gani ajikin madubin ta bayyana hannunta yana gabda da kaina kuma da nayi gefen bana ganinta sai dai Dakin naji ya fara juyamin na kamkame jikina Hakorana suna Haduwa waje daya Gif Gif kamar mai Zazzabin mutuwa.

Sama sama naji Wasila na Fadin"Ga wayar Anty"Nasan dai na mika Hannu na karba Jikina na rawa na Bude wayar sai dai bana gani sai Dishi Dishi Saif nake so na kira ammh kuma Dubu na mamaye ganina kamar wacce aka Dauka aka yarfar haka naji ni na zube a kasa wayar kuma tayi gefe kamar ana ganganrata haka ta shige kasan gado na mika hannu ina kamo wayar sai naji kamar an yi sama da Hannuna azaban da naji ne yasa na saki kara mai karfi Ina ji Wasila na kiran sunana ammh bani da zarafin amsa mata Domin ita nake ji kamar ba aduniyar nan da muke ciki ba ne in da nake kaina bayajin komai sai Dariya da Ihu da Koke koke..

Cikin Dariyan naji ana kiran sunana Cikin wata murya mai saka firgici"Muhibba..!

"Muhibba..!

"Muhibba..!

Kaina na rike da Hannun Bibbiyu ina jijjiga jikina a kasa Lokaci daya ina Toshe kunnena so nake yi nayi mgana ammh na kasa dakyar na iya fadin"A"aaaa..."
Da karfin sosai daganan naji Hannun Wasila a jikina tana rikeni tana Kiran sunana sai kuma naji Dif na Dawo Duniyar wasila nasan dai ta taimakamin na mike ina Dingishi ta kaini Dayan bedroom din na zube kan gado ina Haki ina haki ina Haki Jinin jikina yana gudu numfashina yana Gudu yana Sarkeni ji nayi kamar an Daureni da Kacha na kasa Motsi rawan Sanyi nake yi na kasa mgana Ina jin kukan Wasila ina jinta tana kirana ammh kuma Ji na da ganina baya Tare da ni yana chan nesa ne itama Sama sama nake jinta.

Daganan kuma bazan iya kwantanta abunda ya faru ba na dai san wannan Daran na Dandani azabobi iri iri,haka aka Dinga walagigi dani Tsakanin bangon yamma da gudu da arewa na Cikin Dakina ban san ina Wasila ba Saboda ido na yana Rufe ne sannan ina ji kamar an Daureni da Sarka.

Mari kuwa ban san adadin wanda na shaba Haka zan ji ana jana a kasa kamar wata kayan wanki ina jin mganarta ina jin Dariyarta tana Fadin"Meyasa baki tafi cikin salama ba kamar sauran..?zaki Mutuuuuu..Sai na KASHE KI..!

Wani Buga kaina da akayi da gado ne ban iya kara sanin inda kaina yake ba sai da naji Muryan wasila a tsakar kaina tana Fadin"Anty Anty..!

Sannan na iya bude kumburarrun Idanuwana na sauke anata tana sanye da hijabi ganin na Farka yasa ta Sauke ajiyar rai tana fadin"Kin bani Tsoro jiya da yau Anty..Da Safanan fa nan kasa na ganki kamar wacce aka Tunkudota daga saman gado"
Araina nace Tunkudoni mana akayi ammh na rasa yadda bakina zai bude nayi mgana ganin ina neman tashi yasa ta taimakamin tana min Sannu ina jin yadda gababadaya jikina ya Sauya ammh bai Dameni ba Burina na Fita nayi nisa da wannan gidan da nake ciki.

Wasila ta rakani Har Tiolet ta taimakamin na wanke baki nayi alwala,nazo nayi salla azaune ina yi ina kuka Domin ko"ina na kashina Ciwo suke bakina ya fashe harshe ya Datse da Hakorina,Wasila na zaune gefe tace"Anty da me kika Fasa baki..?

Domin shi Kadai ta gani Faahewar bakina kallon ta nayi cikin karfin Hali nace"Jiya baki ji komai ba bayan mun Dawo wannan Dakin..?

Kai ta girgizamin kafin tace"Ban ji ba Anty ina zaune dake nima barci ya kwasheni sai da naji iskar Safe ta window ne na tashi na leka naga gari ya waye shi ne na ganki a kasa na tasheki"
Kai na girgiza wato ni kadai ce ke jin komai kenan cikin shakewar murya nace"Wasila ki hada kayanki yanzu zamu bar gidan nan..'"
Ido ta zaro kafin tayi mgana nayi saurin Fadin"Don Allah kiyi sauri baamu da Lokaci"
Mikewa tayi tana fadin"To Anty ke fa na hada miki naki kayan..?.

Da kai na amsa mata ina Fadin"Kada ki damu dani".

Jikinta a sanyaye ta fice domin duka kayanta suna Dayan bedroom dina ne Dakyar na iya mikewa bayan Fitan Wasila,Hijabin jikina na Zare na juya kenan zan isa ga wardrope din dakin niyyata na sauya kayan jikina kafin mu Tafi kawai sai naji na bangaji Abu ina Dagowa nayi mummunar ganin da sai da na wuntsila sai gani a karshen gado ina makyarkyata Ita na sake gani wannan karon ta nuna min Fuskarta sai dai nuni mara Dadin gani Fuskarta bata mutana ba ne Hakoranta da jijiyoyinta Hancinta da Harshenta duka suna Bude ne data Bude baki Hakoranta har sun sunkuya kamar na kare,Jini na Digan mata Tunda ga saman kanta har zuwa Bakinta,idanuwana na Runtse jikina na kyarma ina so nayi ihu na kasa kamar iska ssi gata saman kaina Tana Zagaya ni Lokaci daya da Dariya gigitattaciya mara Dadin ji.

Jikina na Takure na Hade waje daya kamar Biro haka take tsalle a saman kaina Jelan gashinta yana Dukan Saman Fuskata da jikina gabadaya in ta Dakeni da gashinta sai naji kamar na Mutu na Dawo ne Kaina kamar zai fashe gida Biyu kunnuwana suna jiyomin Ihu da Dariya acikin kaina Hannuwana na saka Duka Biyu na Toshe kunnuwa cikin karaji da Ihu nace"A"aaa...Ki rabu dani..Kada ki kasheni..!

Dif naji an yi ammh na kasa Bude ido na cikin Gigitattaciyar muryan da kamar acikin kaina ake yi naji tana Fadin"Kina so na barkiii..?

To ki fita Daga Hanyar abunda yake mallaki na zaki mutu ne..Ki tafi Cikin Salama ki Tsira da Rayuwarki nan Din DUNIYA TA ceeee...DUNIYA TA CEEEE...!
Chapter 103 · 0% Book details