← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 144

Sashe 119

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai bayan mangariba muka shigo Zaria su Inna sun cika da Farincikin ganin na Shigo gida da Kafata gida ya Cika da makota har da Lami da Wasila haka ta kamkame ni tana fadin"Anty ta warke"Mirmishi kaawai nayi sai bin mutane da ido kawai mazan waje suka tsaya sai da suka yi sallar mangariba da Isha"i sannan suka shigo Gidan Sani na ganina Lafiyata kalau bana fizge fizge ya daka Tsalle ya Nufeni yana kiran sunana Nima ina ganinsa na Nufesa muka Rumgume juna Ina Dariya Kaina yake Shafawa Lokaci daya yana Fadin"Allah abun godiya Auta ta samu Lafiya"
Sai da aka ci abinci aka natsa sannan Labaran abunda suka gudana tun tafiyarmu har zuwwvyau kowa ya cika da Al'ajabin jin wannan al'amarin Saifudden sai da ya kara jin Labarin sannan ya kara Tabbatar ma kansa ba mafarki yake yi ba da gaske komai ya Faru daman ai yasan haka zata faru ya Zargi kansa sai dai yayi Hamdala acikin ransa na yadda komai yazo karshe..

Inna sai faman kallon sa take yi tana Fadin"Sannu kaji..Allah ya kara tsarewa"sai maida zencen ake yi Inna nata godiya ga Ahalin Mallam da Hajiya Babba Kawu yace"Ai zamu shirya mu je godiya na musamman"
Anty Habiba tayi karaf tace"Baba A bari sai sallah Lokacin kowa yana gida suma gidan mallam din tace Da Sallar kaf yaran su da jikokin su suna nan a garin zasu sallah"
Ummi tace"Kwarai kuwa sai muje alokacin muma mu rama wannam karamcin shima mallam Surajon baza"a barshi haka ba"
Baba Surajo yace"in sha Allahu ai mu me ke da godiya..Jin dadin mu kuma an dace da abunda aka je nema sai dai Fatan Allah ya Tsaremu"
Aka amsa da Ameeen Inna sai jinjina Labarin Saifudden take yi kafin ta Share kwallah Tana fadin"Har aljanu ma Sun shaida kirkin ka Allah ya jikan ka mallam"
Aka amsa da Ameen ni dai da wuri nayi barci ban san iya Lokacin da suka Dauka suna Hira ba an daina Tsaida mganar gobe su Anty habiba zasu rakani gida na Kaduna Inna ma ta bada goyon bayan Haka ammh Saifudden yace ataho da wasila Saboda ta rika taimaka min Tunda har yanzu sai a hankali kowa yayi na"am da haka.

Mazan gidan Saiff na GRA suka je suka kwana kafin Safe mutanen Gaya da na Lere sun ji Labarin mun Dawo Lafiya kuma an Dace Hatta Babani dake chan tana Fama da kafa sai da ta Kirani aka bani muka gaisa tana tamin barka da arziki.

Da safanan yan gidan su Anty zeenatu duk sun shigo,Lami kuma daman data shigo da Safe Inna ta Fada mata tafiyarmu da wasila sai ta koma gida Saboda Wasilan ta shiryo.

Sai wajen sha Daya na Safe mazan suka Dawo nan gidan Inna ita kuma Anty Habiba da Adda Sadiya da taji Sauki Direba ya kaisu sukaje suka kwaso min kayana Duka kadan suka Rage suka Dawo Lokacin har Anty zeenatu tamin Tsifa ta taimakamin ta wanke min kai kanwarta Hajara ta fara min kitso mai kyau da Tsari Ita kuma Autar su Sa'adatu tana saka min Lalle Dayake ta iya na Salatif.

Kawu da Mama zuwaira kafim Azahar suka mika hanya Baba Surajo ma haka,Ummi kuma sai sun rakani Kaduna sai ta wuce Abuja Tunda Lafiya ta samu an isa barka sai dai ba sosai ba Saboda gani nan dai sai bin mutane da ido sai an yi Dariya nayi Ban cika gane komai ba Tabbas acikin kaina akwai Damuwa sai dai an bar mganar da cewa bayan kwana Biyu Asibiti zasu maidani a Dorani kan mgani kila wannan karon adace
Zuwa yammah duka shirye shiryen ya kammallah na fito ras dani sai dai Rashin Sukuni nayi wanka na saka wani Less mai ruwan pick da Milk,kamar ba ni ba yaushe rabon da na zauna haka Inna sai sharan kwallah take yi tana kara Godema Allah,sabbin Littafan addu'o'i Ya Habibu ya siyomin da 40,Rabbana da Qur'ani Izifi Sitti babba da karami da Carbi na Hannu da na zamani ya Damka ma Saifudden,Wajen Biyar na yammah muka Dauki Hanya ni da Wasila da Rakiyar Ummi da Adda Sadiya sai Anty Habiba da Mujaheed sai Sani da Saifudden yace ya taho gobe sai su dawo tare da Anty Habiba.

Duk kawaicin Inna har kofar gida suka Rakamu ita da su Anty zeenatu da taso zuwa ya Habibu yace ta bari Daga baya sai taje tamin kwana Biyu.

Mun isa kafin mangariba gidan na nan a gyare sai dai Datti da kura Adda da Anty Habiba suka Zage suka gyara gidan,abinci kuma Sani da Saifudden suka fita suka yo mana Oder din shi,Dakin Saifudden suka shiryamin kaya na dayan Dakin kuma Suka Sauki Wasila.

Ni dai ina cin abinci sai barci Dakyar na iya ma sallar Isha"i mganganun da alluran asibiti ne ke aiki ajikina yanzu,ba kuma wanda ya matsamin Domin barcin zai kara taimakamin wajen samun natsuwar kwakwalwata.

Tare muka kwana da su tunda akwai Dakuna Sani a Dakin falo ya kwana shi da Saifudden ni kuma da su Anty Habiba Da Ummi Adda da ya Mujaheed gidan su suka koma suka kwana Washegari tun Safe Ummi ta dauki Hanyar Abuja Bama ya tafi kaita Hankalinta duk yayi gida Allah yasa ma bata da matsala su Laala na Gidan Barrister.

Su Anty Habiba sai chan Dare suka tafi Lokacin har Cefane sai Saifuddeen yayo gabadaya ta gyaramin kitchen din takai komai a muhallinsa har girko sai da tayi da taimakon wasila Ta Dafa Dambun Shinkafa da Zogale da yake daga gida muka zo da Shinkafar an surfa da Zogale bushasshiya.

Sai da suka yi Haraman Tafiya na ji na fara kewa ina kuka Anty Habiba ta Rumgume ni ta na Lallashi tare da cemin duk abunda nake so na kirata ta manta ni bani da waya,waya ta bama wanda ya kara bi ta kanta.

Nasha kuka da suka tafi Bama ya kai su Bayan ya Dawo daga kai Ummi Ina kuka har da Majina Saifudden ya Rumgume ni yana sauke Numfashi na kara shigewa jikinsa ina Fadin"Saif ina jin Tsoro"
Da Sauri yace"a"a muhi..ina tare da ke..Babu abunda zai kara Tsorata,ki"
Yana rike dani har cikin Falo Wasila tunda ta ga haka ta shige ciki shi ya Dinga Lallashina Sai dai na bisa da gyada,kai a hankali yake kallona aransa yana Fatan dole zai nema min Sauran Lafiyar da tamin tawaye da karfinsa da Aljihunsa ammh kafin nan sai mun zama abu Daya bazai jira ya kara rasa Damarsa ba.

Sallar mangariba ce kadai ta fidda shi,shima da Dubara sai da yasa Wasila tazo ta kamani yace ta sani nayi alwala nayi sallah kafin ya Dawo haka akayi Wasila ta rika sani a hanya tana fadin yi kaza Anty yi kaza kamar wata yarinya tare muka sallah Sai dai Addu"a da addini bai bace min Daga Tunani ba Rairai na dinga Rere azkar din maraici acikin kaina kamar ana min Wahayi minti daya biyu sai na Tambayi wasila ina Saif..?sai tace min yaje ya Dawo Anty bai shigo gidan ba sai Bayan sallar isha"i ya shigo da Ledoji Biyu ya bama wasila Daya ta zo yimai sannu da zuwa ni kuma makale masa nayi ina kukan ina ya tafi ya barni yana Rike dani yace"Ba inda nake gani nan tare dake Muhi"
Kasa barin sa nayi shi ya Dagani Dani da Ledan muka shiga ciki ya maida koda ya Rufe daman ya rufe kofar Falon ya kuma ce ma wasila in ta gama kallon a falo ta kashe komai tayi addu"a taje ta kwanta.

A kasan Cafet muka zauna akan cinyarsa ya Dorani ya Bude ledan Zabbi ne gasassu aciki sai Madaran Yoghourt mai kauri,Yana bani abaki nima sai na yago na basa ahaka muka Cinyar da juna muka sha Madara karba karba tas muka Cinye gwara shi bai ci Dambu ba ammh ni naci ammh Sai dai na kara cikina ya cika sosai.

Tiolet ma ban barsa ba Tare muka shiga ya Tubeni tas yayi min wanka shima yayi nasa wanka sannan ya Nadoni a Towel ya Daukeni Dakyar Saboda na kara nauyi Saboda koshi ya fito dani Kan gado ya Direni ya shafamin mai ban da kallonsa da kiran sunansa ba na komai Bai sanya min kaya ba Shima bai sanya komai ba yayi kasa da wutar Dakin ya kwantar dani akan gado shima ya kwanta gefena kamkame sa nayi jikina na mutuwa Saboda yadda Fatar mu ta gauraye waje Daya a chan kasa kasa nake kiran sunansa"Saif
"SAIF"
a hankali yamin Rada a kunne yana fadin"Ga ni nan Muhi..Ba inda zan je..Ina nan tare dake abadan Da"iman"
Daganan sai karatun sa ya sauya yayi alkwarin sai mun zama abu daya a wannan daran tare da yakinin Gina sabuwar Rayuwa tare da ni.

Tabbas zasu sake sabuwar Rayuwa.
Chapter 119 · 0% Book details