← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 144

Sashe 124

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Barci nayi kamar bazantashi ba da asuba Dakyar ya iya Tashi na,Yana fita masallaci na koma sai da ya dawo sannan ya matsamin da taimakon sa nayi wanka na dauro alwala nayi sallah azkar ma duk nacin sa kyaleni yayi na koma barci kamar wata yar maye yasan mgangunar ne masu saka barci Saboda kwakwalwata ta samu Cikakken Hutu ranar dai har ya fita aiki ina barci Wasila ya bar ma Sallahu ta kula da ni,Ammh bai bar gidan ba sai da ya tadani yayi min Doren Tea da kwai ya kuma kara bani mgani na sha ni gabadaya duniyar ne tamin Tsit kawai ba abunda nake so na ke Bukata irin naji na kwanta ina barci Natsuwa ta kamani a waje daya.

Cikin Satin dayan da nayi da Fara shan mgungunar nan na asibiti ni da kaina na fara jin chanji ajikina da zuciyata gabadaya ba ni fa da aiki Daga ci sai kwanciya gabadaya Daga Dare zuwa Safe Saif ke wahala dani Daga Rana zuwa yammah da kuma baiwar Allah Wasila,ga cin abincina ya karu kamar gara,arana ina cin abinci fin sau hudu ko cikin Dare ne ko min barcin da nake ji yunwa sai ya Tadani Saif yaje ya Hadomin Tea cikin Jug ya kawomin na gama dashi na koma barci,Yanzu ko Hakkin sa ban cika Sauke masa ba sai dai bai damu ba Fatan sa na samu Lafiya wani Lokaci sai abu ya kamkama sai jikina ya saki sai barci.

Na fara budewa kasa na da Jikina gabadaya da alamun mgungunar bayan saka barci da cin abinci har Kiba suna sakawa,Sannan na samu natsuwa acikin kaina har ga Allah na rage Tsoro da Firgita na amince wlh barci natsuwa ne da kwanciyar Hankali.

Bani da wata Damuwa sai da in na gama ci na sha mgani na koma na kwanta in ta barci,Salla kuma in Saif na gida shi zai tadani in nayi na koma in baya gida kuma Wasila Tana Anty ki tashi lokacin sallah yayi wani Lokacin sai ta Kira Saif a karamar wayarta ta karamin a kunne in ya dameni da kiran sunana haka zan tashi ina Layi in je in yi alwala in yi Sallah wanka kuma wlh shi yake min kafin ya tafi in kuma ya Dawo shi zai Taimakamin nayi da Daddare.

Ni da kaina acikin jikina da zuciya ta na san na samu natsuwa kowa yaji yadda nake barci sai yace a kyaleni ana Fatan nasara domin ai baya ai mganin barcin ma ba sosai yake min aiki ba.
*******
*Lere*
Har satin nan ya kare Majeeda bata koma Abuja ba,Ummi kuma bata kira ba Saboda daman tasan bazai yuyu ace majeeda tayi kwana biyu ba Tunda tadan kwana biyu bata je Leren ba sannan ganin basu Dade da komawa makaranta ba sai bata Damu ba su Laala sun gaji da Tambayan yaushe majeeda zata Dawo taki ce musu komai sai suma basu kara mganarta ba ammh da gaske suna kewarta sun shaku Sun saba komai Tare suke gudanarwa.

Achan lere kuwa Inna Talatu tayi ma Majeeda mganar komawa makaranta tace sai satin nan sama ya shiga har Baffa HASHIMU sai da yayi mganar komawarta Tsakani ga Allah shi yanzu ya Daina adawa da Zaliha Daidai gwargwardo ta rike majeeda kuma ta inganta Rayuwarta bata zuwa hannun Rabbana sai da Kaya da kala kala da abun burgewa su kansu bata bar su haka ba Saifu ma bai bar su haka ba ko wannan zuwan ma Majeeda sai ta kawo masa Shadda Yadi Ashirin shi da Hayatu Sannan Har da su Inna Talatu da matan Hayatu suma da Turamam su har da Goggo Atika da Iya Majeeda kuwa sai dai ma ta yi ta kyauta da na ta komai na cikar yan mata ta na dashi sutura kuma na ta da nasu Laala da suka kwana Biyu duk tazo dasu ta rabama dangi.

Kwata kwata ya saki wannan gabar Tsakaninsa da Zaliha sai fatan alheri da kansa ya kirata ya gayamata Majerda tace sai wani sati zata dawo Ummi tace a kyaleta Bakomai jin ta bakin Ummi sai ya kyale majeedan.

Iya kuma ba ta Damu ba ita karatun Bokon nan ba Damunta yayi ba ita azaton ta ma su majeedan sun samu Hutu ne kamar yadda take zuwa a baya.

Ba wanda ya Lura da yanayin da Majeeda ta dawo sai mahaifiyarta Inna Talatu ta ga majeeda ta koma Shuru shuru sai yawan zama adaki ta Saba abaya in tazo har girki ita ke yi saboda har Baffa Hashimu da yaji majeeda tazo zai ci ga mai girkin yan gayu nan tazo Talatu sakar mata girki ai Zaliha sai dai Allah ya Biyata bayan inganta Rayuwar majeeda da ilimi har ta bangaran girkin zamani bata barta abaya ba,Haka in ta girka suna ci suna Santi suna saka ma Ummi albarka ammh ban da wannan zuwan ita kuma sai bata Takura mata ba Tunda ta tambayeta ko bata da Lafiya ne sai tace mata lafiyanta kalau daganan sai ta shareta ammh ta Lura da wani abu wannan zuwan Majeeda bata zama ashashen su gari na wayewa zata Tare shashen Iya alhalin abaya in dai tazo garin har ta koma tana shashen iyayan nata ita da Bangaram Iya sai dai in taje gaisheta ko in an aiketa.

Duk tana lura da ita sai dai batayi mata mgana ba sai da ta ga asabar tayi gobe Lahadi taga majeeda bata yi shirin komawa Abuja ba,ko wanki batayi ba ballatana ta Hada kayanta,Da Safen kafin Baffa Hashimu ya fita sai da yace"Majeeda ba yau zata koma Habujan bane..?

Ko sai gobe ne Lahadi"?

Inna Talatu tace"ban sani ba ina jin Sai dai gobe domin ban ga ta shirya kayanta ba"
Baffa Hashimu yace"To im ko hakane ta shirya da wuri sai su tafi da Gaddafi shima gobe zai koma Sulaje in da yake kasuwancin sa'
Da Toh Inna talatu ta amsa mai Tunda bai ga Majeedar ba tana bangaran iya.

Sai da yaje gaisheta ne ya ganta kwance a kasan cafet din iya ta Lullube da zani cikin mamaki yace"Ita wannan lafiyan ta kuwa Iya..?

Iya na Tauna goronta da sauran Hakoranta da suka Rage tace"Yo ina zan sani kai ma ka tambaya Hashimu Tunda yarinyar nan ta Dawo bata da aiki sai zuwa nan ta min wannan kwanciyar kuma nayi tambayan duniyan nan ko wani abu ke Damunta tamin banza bata ga Dama ba"
Baffa Hashimu ya jinjina kai kafin yace"Ke Majeeda tashi zaune"
Ba musu ta mike tana fadin"Ina kwana Baffa"
Amsawa yayi da lafiya lau yana Fadin"Yaushe kika shirya komawa Habujan..?

Sai majeeda ta kasa mgana Iya ta balla mata Harara tana Fadin"Ya na miki mgana kina kunnen uwar shegu dashi..?

Majeeda kanta na kasa tace"Ni..Ni bazan koma ba"
Ba iya kadai ta Razana ba Hadda Baffa Hashimu da Inna Talatu da tazo Shashen kenan taji mganar sai ta kasa shiga ta Tsaya jikinta na rawa tana Sauraran abunda ke faruwa.

Iya ta saka salati ta dire tana Fadin'"Bazaki koma ba da akayi miki Uban me a chan?.yarinyar zaki yi ma knki Tunda Zaliha tatafi dake chan Habuja kika koma abun sha"awa kowa ya ganki sai yace majeeda ta koma yar gayu har ana jin Haushin haka shine Saboda jin Dadi zaki ce bazaki koma ba"
Baffa Hashimu Saboda Haushi ma ya kasa mgana Majeeda daman kiris take jira kawai sai ta saka kuka har da majina,Iya ta rika Tafa Hannu tana Fadin"Yau ni naga shegantaka Hashimu..dauko min icce na gicciye yar banza yarinyar nan"
Jin haka yasa Majeeda ta mike tana Buga kafa Lokaci daya tana Fadin"Ni wlh bazan koma ba na riga na fada bazan koma ba"
Daga haka ta fice tana kuka Tana Fira taci karo da Inna Talatu wani irin Kallon banza ta wurga mata ta Bude baki zatayi mgana kawai ta Fizgi Hannunta sai shashensu har cikin Daki kuma ta maida kofa ta Garkame.

Iya kuwa Majeeda na fita sai ta koma tayi Tagumi tana sharan hawaye da Haban zaninta fadi take yi"Ni dai Wlh ba Ruwana Zaliha Mutuniyar kwarai ce ita da Danginta..Duk Cin kashin da muka sha yi mata bata taba Dago ido ta kallemu ba baiwar Allah ta wahala Damu Saifu ma ya wahala Damu komai ta samu sai ta tuna Damu Wanda kuma ya Hada ai ya Raba Hashimu ammh Zaliha a uwa ta Daukeni ku kuma yan"uwa bata yadamu ba, da wani ido yanzu zamu kalleta Shegiyar yarinyar nam zata kunyatamu."
Sai kuka wiwi Baffa Hashimu ya sauke Numfashi kafin yace"Wlh nima Iya kunyar ta nake ji..Basan da wani ido zan kalleta ba"
Iya na sharan majina da Haban zaninta tace"iya ka in taki ga Sailuba nan yar wajem Atika sai ita taje ita kuma sai ta zauna gata ga garin nan aiko aure zamu yi mata bazata zauna tana Hada jiki da iyayanta acikin gida nan ba don ubanta"
Iya tayi Sababi har ta gaji Baffa Hashimu jiki ba Laka ya fice Daga gidan ammh aransa ya Kuduri niyar ko Majeeda naso ko bata so sai ta koma Habuja tunda ita sakara ce mara wayau.

Bangaran Inna Talatu kuwa tana kulle Majeeda acikin Daki ta fito ta cigaba da Sabgarta,sai da ta gama abunda zatayi sannan ta koma Dakin ta iske Majeeda ta ci kuka har Idanuwanta sun kumbura.

Wani kallo ta watsa mata kafin tace"Sauko ki zauna mgana zamu yi"
Jikin majeeda na rawa ta sauko saboda Tunda taga yanayin Innar ta tasan sauran.

Gefen gado Inna Talatu ta zauna Lokaci Daya tana fadin"Me naji kina fadama iya da bffan ki dazu?

Sai majeeda ta kasa mgana kanta na kasa Tsawa ta Daka mata tana Fadin"ba da ke nake mgana ba..?

Jikinta na rawa tace"Nace ne..Nace bazan koma ba"
Inna Talati tace"Da zalihar tayi miki mene?ko kuma su zainabun ne suka yi miki wani da yasa kikace bazaki koma ba..?

Sai Majeeda ta fashe da kuka ta kasa mgana Inna Talatu tace"Karki batamin rai na make ki wlh ki Bude baki ki yi min mgana"
Majeeda na jan hanci tace"Bakomai"
Inna talati tace"Zaki ce bazaki koma ba ne ba Dalili?
Chapter 124 · 0% Book details