← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 144

Sashe 79

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka ta mike ta Tada Sallah Galala yayi yana kallonta sai kuma jikinsa yayi sanyi duk da Nasiha ce ammh kuma kamar mganace ta gayamai wato an ce a Daki yaro dan shekara goma shi kuma da ya girma me take nufi..?

Kunya da Takaici suka saka Kasalan ta Sake sa ya mike Dakyar ya Fada Tiolet yayi Alwala har ya fito bata Idar da Sallah ba Jallabiyansa Fara ya Dauka ya koma Bayin ya sauya kaya zuwa Jallabiyan sannan ya fito ya saka Saukakken Takalminsa ya fice Ita kuma Tana salla sai bayan fitar sa sannan ta Idar a ranta ta guduri Niyya gyara Mai Ibadar sa Rauninsa kuma zai Sake sa da yarda Allah.

Har karfe bakwai tana zaune tana addu"o'on ta bayan ta gama azkar Daganan bata koma barci ba shi kuma bai Dawo ba sai ta kwashe abunda ya kwanta ta gyara don kamar ba'a kwanta ba sannan ta fita,Dakin Ummi ta shiga bata ciki ashe tana Kitchen ita da Laala tana shiga ta Duka ta gaisheta ta amsa tana Fadin"Diyata mun tashi lafiya..?

Muhibba ta amsa mata da Lafiya Laala ma ta gaisheta ta amsa cikin Sakewa ita ta karbi aikin Laala na feran Dankali Laala ta koma Daki abunta ta bar Ummi da Muhibba suna aiki suna Hira da Muhibba tace Ummi ta koma Daki zata yi aikin ita kadai Ummi tayi Dariya kafin tace"Ina jin Dadin gani na muna aiki tare da Muhibba kada ki damu..!

A haka suka karisa aikin nasu Ummi ta koma Daki tayi wanka itama Muhibba din wanka tace taje tayi,Duk da tana Fargaban zuwa Dakin haka ta Daure ta koma ashe ya Dawo yana cikin Bargo akan gado ya dungule ita dai bata bi ta kansa ba ta Dauki kayan da zata saka ta shige Tiolet tayi wanka ta kuma wanke kayan jikinta ta shanya a Tiolet din ta fito da wanda ta Dauka ajikinta Mai ta shafa Sama sama ko kayan Shafarsa bata taba mai ba tazo da nata gudun mgana har ta gama abunda take yi ta fice bai motsa ba Duk Tunaninta barci yake nan kuwa idanuwansa Biyu juyi kawai yake yi ya kasa barci mganar data Fadamai ta ishesa a cikin Ransa.

Basu jira sa ba suka karya bayan sun gama Ummi tace zata shiga asibiti ammh bazata Dade ba zata dawo su fita da Muhibba taga gari su Laala nata murna Tunda Ummi tace har kasuwa zasu Shiga zata yi ma Majeeda Siyayyah
Su ta bar ma gidan Suna Falo suna kallon suna Hira Majeeda na gaban Tv kamar zata shige ciki sai mgana take yi duk abunda tagani sai tayi mgana su kuma suna mata Dariya nan ta Fara barci sai da Zeeha ta tasheta tace ta shiga Ciki dakin su ta shige ta hau Gado sai barci har Rana tayi bata Sani ba sai da aka kira wayarta ta Farka Daman da abunta a makale da ita Inma ce suka gaisa tace ta bata Ummi su gaisa tace tatafi wajen aiki sai dai in ta Dawo basu jima suna mgama ba sukayi sallama sai alokacin ta Fito Falo sun gyara ko"ina suna zaune suna Hira majeeda ta gaji da kallon tayi barci
sannu suka yi mata Mamakin Dadewar da tayi tana barci ne ya isheta har sha Biyu saura su ta tambaya sukace Ummi bata Dawo ba sai kawai ta Fada kichen bata re da Tunanin komai ba ta Dora Jallop din Shinkafa da Nama tunda akwai kayan Cefane su Laala sai dai sukaji kamshi suka shigo suna Fadin"Laa Anty Har kin gama girki..?

Dariya tayi kafin tace"Zan dai gama muje mu yi sallah kafin mu idar ya karisa.."
Laala ta Hura hanci kafin tace"Hamma na kwasan gara..!

Suka saka Dariya har da Tafawa ita da Zeeha dariya tayi musu tare suka fito ita ta wuce masaukinsu su kuma suna tashin Majeeda Daga barcin abun na bata mamaki baya gajiya da barci yana nan kwance cikin bargo bai Tashi ba Har ta Shiga tayi alwala ta fito da Ruwan hannunta ta yarfamai a Saman fuskarsa da garin barci ya jaye Abun Rumfan nasa.

Bai tashi ba sai da ta kara yarfamai sannan ya Bude idanuwansa sun yi Jajir kafin yayi mgana tace"A ranar gobe kiyama Farkon Hisabi a wajen Allah Itace Sallah..In tayi kyau to duka ayyuka sun yi kyau..in ta baci kuma Duka Sauran ayyukan sun baci..!

Da haka ta juya ta Dauki Hijabinta ta saka ta Tada Sallah Lumshe ido yayi ya kara Budewa a kanta kawai sai yaji Mirmishi ya Subuce mai Tuni kasalar jikinsa ta Sakesa ya Sauko Daga kan gado ya Fada Tiolet Wanka yayi ko da ya fito bata Dakin sai ya samu Sarari ya shirya a tsanake cikin Riga da wando ko da ya gama an Idar da sallah sai yayi na shi a gida kawai yunwa yake ji Shiyasa ya fita Falo nan ya iske su sun baje suna cin abinci suna ganinsa suka fara Rige rigen gaishe shi amsawa yayi yana kallon Muhibba wacce kanta ke kasa tana cin abincinta cikin Yanayinsa yace"Ina Ummi..?

Laala tace"Ta je asibiti ammh tace bazata Dade ba."
Jinjina kai yayi ya juya zai koma Ciki Zeeha tace"Hamma ga Breakfast dinka chan a kan Dining ga kuma Lunch Anty Muhibba ta yi mana."
Kamar zai ce wani abu sai kuma ya fasa yace Ok sannan ya nufi Dining din yunwa yake ji Tea ya hada ya sha sannan yaci Jallop din nan Kusan tada wandaa aka saka mai yayi Saboda Dadi a aransa yace ashe haka ta iya Girki..?

Shiyasa junaidu ko da yaushe yake mai godiya suna kwasan gara bai sani ba yana gama ci ya koma Daki ya Dau wayarsa ya Bude Data yana ganin Sakonni,wasu ya bada amsa wasu kuma ya share,Har aka kira sallar La"asar da wuri yayi alwala ya tafi masallaci yana Fita sai ga Ummi ta dawo sallah tayi sai taci abinci tana ta Sa ma Muhibba albarka Dukkansu Daman sun shirya ko da Saifudden ya Dawo a haraban gidan ya gansu Ummi zata tukasu.

Cikin mamaki yace"Ummi ina kuma zaku je..?

Ummi tace"Gidan Barrister zan kai muhibba ta gaishe su daganan ta dan ga gari har kasuwa ma zamu shiga zan yi ma Majeeda siyayyah.

Bai ce komai ba Tim ya kallah Kafin yace"Drive them and Excort Them..!"
Daga haka ya kalli Ummi yana Fadin"Zai tuka ku Ummi sai kum Dawo..!"
Daga haka ya shige Cikin gida kamar yadda ya Fada a motarsa Tim ya Tukasa Bama na gefe sun je gidan Barrister sun gai she shi da matarsa suna ta yaba Hankalin Muhibba da zassu tafi matar ta bata Turaruka Barrister kuma kudi ya bata 10,Daganan sun je har park sannan suka shiga kasuwa Ummi ta siya musu kayan kwalliya da su pad majeeda kuma aka siya mata Iners da Kayan barci sai atamfa da leshi kala goma basu Dawo gida ba sai da suka biya suka kai Dinki suna shigowa gida ana mangariba a Kofar gida suka Hadu da Saifudeen zai je masallaci da Jallabiyan sa fara kamar wani balarabe suma suna shiga gida salla suka fara yi sannan Ummi ta sa Zeeha ta fere doya ta Dafa Laala kuma tayi miyar Sources din.

Bai dawo ba sai bayan sallar Isha"i Muhibba da wuri ta kwanta Saboda ta gaji Majeeda da su Laala kuma suna Dakinsu ummi ne da Saifudden suka Dade suna mgana sai lokacin ya Fadamata gobe zai shiga Office zasu koma zai sauke Muhibba agidan Sadiya Ummi tace hakan nada kyau kafin ta kallesa tace"Ka barta taje taga iyayenta..?

Girgiza kai yayo kafin yace"Ummi ni ban Hanata ba in tana Ra"ayi zata iya zuwa."
Ummi ta gyada kai kafin tace"In kun koma ka Dauketa ka kaita..Sannan ka shiga Ka gaishe da Innar nasu Dazu muka gaisa da ita sai da ta tambayeka
Shi dai da Toh kawai ya amsa Ummi ta mike tana Fadin"Kuma ka fara shiri kuje chan gaya babban gidansu ka gaishe su.

Fuska ya yamutsa kafin yace"Ummi..!"
"Ko bazaka je ba ne kake so ka Fadamim..?

Ta fada fuskarta ba wasa da Sauri ya mike yana Fadin"Na Tuba Ummi zamu je Insha Allahu..Sai da Safe.

Ummi ta rakasa da mu kwama Lafiya.

Koda ya shiga Dakin ta Dade da barci chan gefem gado ta shige cikin Hijabinta shima barcin yake ji bayan ya saka kayan barci irin kwanciyar jiya sukayi ita a saman gado shi kuma ya kwanta saman Cafet.
*Janafty*
*SFD0029*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
DA asuba ma da ta tashi ita ta tashe shi,kin tashi yayi ya koma barci kasala bata sake sa ba,Ganin haka yasa ta janye bargon da ya shige aciki yana juyowa kafin yayi mgana ta rigasa da cewa" A cikin alamomin Munafuki akwai rashin Samun Sallar asuba da isha'i acikin jam"i."
Tana gama Fadin haka ta sakar mai bargonsa ta juya ta tada sallar.

Ya dade yana kallonta yau ma kalamanta sun gama kashe mai jiki kenan shima Munafuki ne?tunda bazai iya Cewa yaushe da yaushe ne yake samun Sallar asuba acikin jam"i ba.
Chapter 79 · 0% Book details