Sashe 115
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nan dai akayi sallama bayan alkwarin baza"a yarda zuumunci ba...har bakin mota Hajiya da Anty Hadiza suka Rako mu mallam dai Saboda Kafa bai fito ba.
Tunda na lura ba da Hajiya zamu tafi ba na fara kuka ina rike da ita cikin Sigar Lallashi tace"Bar kuka..waya Fada miki ba da ni za'a tafi ba..?
Shiga mota muje kin ji Diyata"
Da Lallashi da komai Hajiya ta samu na shiga mota,Ina shiga sai tamin wayau tace bari ta shiga gida ta Dauko abu ta Dawo ni dai ji nayi mota ta fara tafiya haka na fara kuka ina waige,Ummi ne da Adda Sadiya suka Danne ni ina ta kuka gabadaya na Rikice.
Har muka isa Bazanga ta Danjan jahar Katsina ajiyar zuciya nake yi naci kuka har na gode ma Allah Tiryan Tiryan har kofar gidan mallam Surajo da ya zama ginin zamani.
Daman yasan da zuwan mu har cikin gida wani da'nsa yayi mana iso mu cikin gida wajen matansa muka Shiga mazan kuma suna Falon sa na waje insa yake ganawa da baki.
Surajo dai jika yake wajen mallam Shekaru talatin da wani abu da barinsa gida ya fita neman ilimi da kudi,Sai dai ko da ya dawo sai ya Dawo da Lakanin in dai yaga mutum in dai yana da aljanu a jikinaa sai ya bayyana wato lakanin gane su da kuma Yin mgana dasu ance aljanu sun sha Fitowa ta sufar mutane su yi mgana da Mallan surajo Tunda aka gane sa sai garin ya zama ta zirgan zirgan Mutane Duba da yanayin da muke Fama da shi na aljanu a wannan Lokacin jin wannan Labarin sai Hankalin mallam ya tashi yasa aka kirasa har Gumel yayi mai fadan ya daina kada ya zama Boka watarana yana jin mganar Mallam sai yayi mai alkwarin ya Daina Har Abada ya bashi jari ya koma ya cigaba da kasuwanci yana Noma.
A jiyan da mallam ya kirasa ya fadamai abunda ke faruwa bai yi kasa a gwiwa ba yace su zo saboda yana Fatan ko wanne ne aiki na karshe da zai yi Zai yi domin alfarman Dattijo mai Daraja domin sanda ya Dawo garin mahaifiyarsa tayi fushi Dashi Da Taimakon mallam da Hajiya komai ya Daidaita.
Sai da sukayi sallar azahar suka ci abincin Tuwon shinkafa Miyar Shuwaka tayi dadi taji Nama da Manshanu Matan mallam Surajo suna da matukar Kirki da karamci Daman an ce Katsina ta Dikko Dakin kara kunya a ka san mu ba Tsoro ba.
Sai misalin Biyu na Rana Mallam Surajo yace a shigo Dani daga cikin Dakin da su kawu suke bayan ya gama jin ta bakin su gabadaya sai dai Tun zuwan su Saifuddeem ya Tsargu da irin bin sa da kallo da mallam Surajo ke yi har sai da gabansa ya Fadi Haka kurum baya so ma yana Hada ido dashi sai ya labe bayan Mujaheed kansa na kasa kamar wani maraya.
Bai dai yi mgana ba Sai gyada kai yake yi har aka shigo Dani Dakin Ummi na rike dani Kamkam tunda muka shigo Dakin sai naji kamar natsuwa ta shige ni sakin Hannun Ummi nayi da kaina na isa gabansa na zauna har ina tankwashe Kafafuna sai dai ina ta kallonsa shi kuma kallo Daya yayi min ya kauda kansa ga gemunsa nan na sunna yakai kamu Uku.
Kai Tsaye bayan su Ummi sun gaishe shi yace su samu waje su zauna Bayan sun zazzauna ya sake kallon Saifuddeen kafin ya Kalli kawu yana Fadin"Wanchan da ke zaune a baya waye shi..?
Kawu ya juya yana kallon Mujaheed da Saifudden kafin yayi mgana mallam Surajo yace"mai Farar jallabiya nake mgana"
Kafin kawu yayi mgana Mujaheed yayi saurin cewa"mijin ta ne shi"
Mallam Surajo ya jinjina kai bai ce komai ba sai dai ya kara dagowa yana kallon Saifudden har sai da kowa ya Tsargu Kawu ne yace"Ga mara Lafiyan nan a gabanka mallam'"
Bai Dauke kansa Daga Kallon Saifudden ba yace"Na ganta tun sadda ta shigo wani abu nake gani..A inda ba"a zata ba ni kuma a nan nake ganinsa"
Sai falon ya dau shuru a ka koma ana kallon kallo cike da mamaki Saifudden kuwa ya kasa Dago kansa gabansa ke fadi fat fat ya kasa sakin jikinsa,
Tun kallo D'ayan nan da
mallam Surajo yayi ma Muhibba bai kara ba sai dai ya kara D'aga ido ya kalli Saifudden kallo na sosai da sai da ya kara jin wani irin tsarguwa da acikin jikinsa yake jin idon malamin a kansa cikin muryansa mai Taushi da kaushi Mallam Surajo yace"Bawan Allah ya sunan ka?
Saifuddeen ya dago kansa a Firgice yace"Saifuddeen"
Gabansa na Faduwa Fat!Fat!Mallam Surajo ya murmusa kafin yace"Cikakken sunanka nake so naji"
Saifuddeen ya Runtse ido kafin yace"Dr.Saifuddeen Conel.Salahudden Lere"
Jinjina kai yayi bai kara mgana ba Ummi da Kawu suka kalli juna Kawu ya kasa Hakuri ya gyara zama zai yi mgana kenan ya Daga mai Hannu Lokaci daya yana fadin"Ba sai kayi tambaya ba zan amsa muku tarin tambayoyin ku"
Sai da ya kara natsuwa sannan ya Dago kansa yana Fadin"Ba aljanu ajikin wannan yarinyar taku..Sai dai Naga wani al"amari ajikin wannan bawan Allah nan da kuka ce mijinta ne."
Gabadaya sai kallo ya koma kan Saifuddeen cikin mamaki Ummi tace"Wani al"amari ne Mallam..?
Mirmishi yayi kafin yace"Zata bayyana kanta yanzu nan kun zo inda Aljani bai isa ya boye kansa ba komin karfinsa komin ikonsa.."
Zata bayyana."
Zata fallasa komai..."
Abubuwa zasu warware kansu."
Duk ita take aikata komai ba"a sani ba muguwa ce sannan bakar Kafura ce ita ta kusa haukata wannan yarinyar ba Domin ita din mai yawan Ibada bace da Tuni ta HAUKATA TA"
Kawu cikin karfin Hali yace"To Hauka na nawa kuma mallam..?
Me ya rage a Hankalin Muhibba..?
Gabadaya kowa ya shiga mamakin Lamarin Ga kalaman Mallam Surajo masu Daure kai da gangar jiki.
Mallam Surajo yayi Dariya ba Ko Carbi a Hannunsa ballatana ace da shi yake Lakanin zaune yake saman Darduma Hankalinsa kwance.
Kafin yace"Ba ta Haukace ba..Da Sauran Hankalinta ba haka Hauka take ba..In da ta Haukatata da yanzu bata Tare daku tabi Duniya..Haka taso tayi mata so tayi ta KASHE TA ma"
Ido kowa ya zaro ba"a san adadin Mutane Nawa ne suka Hada bakin Wajen fadim"ita wa...?
Kai ya girgiza kafin yace"Zata bayyana kanta yanzu tayi kuma bayanin komai da bakinta Dolenta"
Sai jikin su Ummi ya fara rawa Saifuddeen sai yaji kansa ya Sara jikinsa na rawa zafi na Huromai Cikin jikinsa Iska kawai yake nema Da Sauri ya mike baya iya ganin gabansa zai fice Da wata irin Murya da ba wanda yasan Mallam Surajo nada ita yace"INA ZAKI KUMA..?
DAM!
Gaban kowa ya amsa Hatta ni sai da na koma jikin Ummi na makaleta jikina na rawa Yaron Anty Habiba Amir sai da ya Tsandara ihu saboda Firgita Cak Saifuddeen ya Tsaya ya kasa ko wani kwakwaran Motsi Cikin wani yanayi mallam Surajo ya kalli Anty Habiba yana Fadin"Ki koma cikin gida da shu .Duk wacce ke da tsoro ta koma cikin Gida ba mu ne zamu yi mgana da ALJANAR CE zata yi mgana Dolenta"
Ai jin haka kadan ya Rage Adda Batayi fitsari ba kowa sai ya kwalalo Ido Anty Habiba da take a firgice ta mike ta Fice da Sauri Amir na Cigaba da Tsala kuka Adda Sadiya ga Tsoro gashi Tana son jin abunda ke Faruwa sai ta kasa tashi ba Matan ba har Su Mujaheed sun Firgita kawai sun Dake ne Ummi kuma bata tsorata ba,bakinta ne bai Daina ambaton Allah ba.
Mallam Surajo kallonsa kyam na kan Saifudden da wannan kakkusar Muryan tasa yace"Kina Tunanin anan ma zaki iya tsira ne..?
Karya kike yi..Tunda kika bari suka zo nan To watan tonon asirin ki ne ya kama kuma da bakin ki zaki bayyana kanki in kuma kika bari ni na bayyana ki sai na kona ki da ayoyin Allah kin yi muutuwar Wulakanci Mafi Munu acikin Jinsin ki"
Ya fada cikin Kaushin murya da Natsuwa gabadaya sai kowa yaji shuu kamar Dakin wani abu ya Gifta Dariya Mallam Surajo yayi kafin yace"Babu inda zaki iya zuwa Kin zo inda Karfin ki bai isa yayi miki wani amfani ba"
Kawai sai gani akayi Saifudden ya Dafe kansa yana Layi kamar zai Fadi Dakin ya fara girgiza kamar za"ayi Girgizan kasa Mujaheed ya Damke Hannun Ya Habibu bakinsa na rawa yace"Kawu..kasa zata Tsage..!
Adda Sadiya kuwa sai kuka har da Dashin Fitsari.
Mallam Surajo yace"Ku bar ni da ita bayyana take so tayi"
Ai jin haka yasa Mujaheed har da su kawu suna rige rigem matsewa jikin bango jikinsu ba inda baya rawa tun ballatana ma Baba Surajo,Baba Sa'idu ne bai firgita ba cikin muryansa yace"A"a ka fada mata kada ta bayyana..akwai wad'anda hakan zai Cutar dasu"
Mallam Surajo yace"Ban bata ikon haka ba damam kee...Ajikinsa zaki Tsaya a inda,kika Saba zama anan zamu yi mgana MUNAFUKA Kawai"
Kamar kiftawan abu sai jin wani irin Ihu da kukan mace mukaji kafin Saifudden ya juyo yaraf ya zube Durkushe gaban mallam Surajo Cikin muryan mace ya Hada Hannayensa yana Fadin"KA...DA...KA..MIN.
HA...KAAAA..."
ILahirin wajen ba wanda jikinsa baya rawa ni kuma sai naji muryan nan dake Tsorata ni nan da nan na Rude ina kokarin Guduwa ina nuna Hannu ina Fadin"Itace..Gata nan..Zata kasheni Ita ce..!"
Mallam Surajo ya kalleni kallo Daya kafin yace"Koma ki zauna anan wajen bata isa ta kara yinkurin cutar da wani ba"
Hatta Ummi jikinta kyarma yake yi tajani ta zaunar dani a gefenta Adda Sadiya na jikin bango ta makure sai Salati take yi acikin ranta cikinta sai uban motsi yake yi kamar zata yi barinsa.
Ido Cikin ido mallam Surajo ke kallon Saifudden da kansa ke sunkuye jallabiyan jikinsa ta jike da Zufa Cikin Kaushin murya yace"Kin san akwai irin wannan ranar kike wahalar da bayin Allah?
Kina ta Zangon kasa kina wasa da Hankalin mutane..Har kina neman Cutar da yarinyar da bata ji bata gani ba..Kinsan ai akwai irin wannan Ranar kika nemi kasheta..?
Me ta tsare miki..?
NACE ME TA TSARE MIKI?