Sashe 61
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shuru nayi ban yi mgana ba ganin haka yasa Asma"u ta fito da waya ta Daddana ta kara a kunni har ta gama Ringing bai Dauka ba sai ta sauke wayar sai dai kafin tayi mgana Kira ya Shigo wayarta ta Dauka suka gaisa Cikin Girmamawa tace"mun yi mgana da Amarya ta nuna bata son komai.Ammh zamu yi walima."
Mujaheed Dagachan bangaran yace"Walima kad'ai..?
Asma"u tace"Eh Amaryan taku kasan Ustaziya ce."
Yar dariya yayi kafin yace"Shima Angon naku ai ya fitama Uztazan ci kuma ma duk bai san irin wad'anan abubuwan ba..Daman ko kun Tsara sai dai mu baku kudi mu ce Allah ya sanya alheri sai mun zo Daukan Amarya in mun Dawo Daga Gaya Daurin aure.."
Asma'u tace"Masha Allah..Allah ya nuna mana" ya amsa mata Ameen Ameen kafin yace"Ki Turomin acct nomber dinki yanzu."
Da haka suka Katse wayar nan take ba A dau Lokaci ba sai ga alert din kudi 200k ya turo Asma'u ta nuna ma Aisha tana Fadin"Kalli ki ga Aisha Dubu dari Biyu."
Aisha ta gyada kai tana fadin"Ba shakka kin san ai manyan mutane ne..Muhibba ga kudi fa ya zamu yi dasu..?
Muhibba ta mike tana Fadin"Ina ruwana..?Sanda kuka shirya ai ban sani ba.."
dariya sukayi basu bi ta kanta ba Asma"u ta Kira Anty Habiba ta Fadamata tace gata nan zuwa gidan.
Sanda tazo Muhibba na Daki bata san me suka Tsara ba,Sai yammah dai suka tafi Inna ta bisu da godiya
Washegari jumma'a da zani makaranta Inna ta kalleni tana Fadin"Auta kin kaima yan makarantar naku abun Bikin kuwa..?
Baki na Tura kafin nace"ni ban fadama kowa ba."
Inna ta saki salati kafin tace"Har Hafizu yaron kirki..?
Muhibba tace"Inna kawai sai nayi ta cewa zan yi aure..?kuma in suka san wa zan aura Allah kadai yasan wani kallo zasu yi min."
Inna taga dai fada ba zai min ba yasa ta fara Lallashinta cikin Hikima tace"Haba Auta ina ruwanki da wani kallo zasu yi miki ke dai ba Raya sunar Ma'aiki zaki yi ba..?Kuma aure ai na Allah ne matar mutum kabarinsa wani bai isa ya auri Matar wani ba..Ki basu Shaida ne Auta ki Fita Hakkin zaman tare in sukaji Labari a wani waje zasu ji ba Dadi."
Da wannan kalaman Inna ta saka na kwashi Katuna bikin da alewa mai yawa wanda Ya Habibu ya kawo mata na Rabo na tafi makaranta dashi Sai dai katin na wajen Ya Habibu na Dauka na wanda su Aisha suka kawomin Anty Habiba ta Diba ta kuma Dibar ma Ya Habibu har da Sani da ya bar mata sallahu na gidan Gwamnati ya ke so
Sai da naje makarantar naji banda karsashi Raba katin aure na da kaina ana tashi Break na je ajin Anty Jidda na Zube mata tana Faman tambayanta na Bikin waye sai dai ta kasa mgana data karanta taga sunana Baro baro Cikin mamaki da murna tace"Wai da gaske Anty..?
Ban bata amsa ba na mata shuru,Shuru na ya tabbatar mata da amsar ta ta fara murna tana Fadin"Kai Anty shi ne ko Labari..Gaskiya am so happy for u..!"
Kai na kasa nace"Ba'a saka da yawa bane shiyasa..plz ki raba ma sauran malaman ina jin kunya bazan iya ba."
Anty Jidda tace"Yanzu kuwa..?
Ta mike nima ma mike har zata fita daga ajin Taja ta tsaya tana kallona cikin mamaki nace me ya faru..?
Sai tace min"kin kai ma D.Musa kuwa..?
Na girgiza mata kai da Sauri ta Zari Card Daya ta mikamin tana Fadin"Bai kamata ni na kai masa ba..Ki kai masa da kanki."
Ba yadda zan yi haka na amsa na wuce ita kuma ta wuce section din mu fuskarta na bayyana Murnan datake ciki.
Salau salau kamar kazar da kwai ya Fashe ma aciki haka na shiga Office din D.Musa da Sakatariya na fara mgana sai da ta kirasa ta gayamai sannan na shiga yana zaune kan kujeransa yana faman Rubuce Rubuce sallamata kawai ya amsa batare daya Dago ba.
Sai dai ina karisowa ya Dago kansa yana Mirmirshi kafin yace"Have a sir MADAM.!"
Sai gaba na ya fadi na zauna kamar ban da jini cikin nazarina yace"Madam akwai damuwa ne..?
Dakyar na gaishesa ya amsa yana kallona Hannuna na rawa na Dora mai katin saman Teburinsa ina Fadin"Sir..!
Ba musu ya sa ka hannu ya Dauka ya karanta Lokaci daya ya Dago da mirmishi saman Fuskarsa kafin yace"Kin fita ko ba sabulu.daman nace bari nagani ko zaki kawomin gayyatan..?
Yafada yana kallona ni kuma jikina sai rawa yake yi bai damu ba ya cigaba da fadin"Sir Mujaheed ya Turomin.Congratulation Muhibba..Insha Allahu har chan Gaya zani Daurin aure."
Ya fada yana kallonta da Mirmishi sai Muhibba ta kasa kallon D.Musa ballatana ta amsa mai haka ta fice Daga Office din D.Musa ya bita da kallo cikin mamaki Aransa yana Fadin Sabanin kenan yanzu ko akasasin sa..?
Shi dai an ce mai Sabani ne to ga katin aure kuma shima duk a matsayin Sabanin ne..?
Bai damu ba,Tunda shi bai cika shiga Hurumin da ba nasa ba sai dai Borh of Them ya taya su Murna Muhibba Is a Nice person ba domin kyanta ba Sai Domin Nagartatan haka shima yallabai Is a good Person yana da kyawawan Hallayar da bakowa ke dasu ba ya tayasu murna matuka.
Koda Muhibba ta karisa Seection din su Har aji Hafiz ya biyo ta yana mata Tsiyan Amarya Amarya kunya yasa ta kasa mgana ya mata Fatan Alheri ya koma ajinsa ashe har Student sai da Anty Jidda ta bama Alewa wad'anda suka samu har da Student din ta da aka tashi taje Signing Attendence Headtecher da Sauran malamai na ta mata Congratulation.
Ban da Anty Usaina da Anty Khadija Bakin ciki kamar su mutu gani suke kamar wasa ne ba gaskiya bane Har Hafiz suka tara suna Tambaya yace su bari Ranar Bikin suje su gani aiko sun yi alkawarin sai sun je su gani wanu irin Biki za'yi tare da ganin mijin da muhibba zata aura Gulma dai wasu ai jininsu yake.
Data koma gida sai taji kamar an Sauke mata wani nauyi mai girma yan Islamiyan su ma Nusaiba da jamila da suka zo ta basu suka je suka Raba,bayan nan ita Muhibba bata yi gayya ba,Bata da wasu kawaye su Aishar ma ba domin sun saka kansu ba,bazata matsa ma kowa ba.
Washegari Lahadi Anty Habiba ta Diro Ranar ana ta ma gidan gabadaya Fenti shirgin Dakin Inna an saka su Cikin Madafinta na Tsakar gida duka Dakunan kuma Anty Habiba ta siyo Sabuwar Leda an saka sai waje yayi kyau su siyama na gidan su da su bello suna da wasa da Murna har da Walid Khalifa dai bai zo ba yana gidan kakaninsa yafi zama achan fiye da gidan Inna Saboda chan akwai sa"aninsa.
Adaran Ranar Anty Habiba ta fita bayan naji tana ta waya da wata kawarta da sukayi secondary School tare,mai suna Salamatu zuwa chan sai gata ta Dawo da Baggo guda cike da kaya ta shiga Dakina ta baje a gabana nq idar da sallar isha"i na kenan ta fara Gwadamin kayan,wadanda ke Dauke da Tarkadan mai kayan da suna kamar haka KAYAN BUZUWA,set ne guda babu abunda babu aciki har da Hadin kaza da Zabbo gumba kala kala sannan gefe daya akwai had'in na Infection wanda Anty Habiba ke Fadamin da su zan fara tana Fadin kayaane masu inganci da Nagarta ita tun da tayi aure dasu take amfani dashi kayanta akwai tsada ammh kuma suna da inganci sannan mataki mataki ne kowani set da kudinsa.
Cikin mamaki yawan kayan nace"Anty duk wannan nawa..?
Anty ta kalleni kafin taace"Wannan set din na 50k tayi promo ta barmim 30k hadin Amare ne sannan na Infection ma tayi min sauki Tunda ta Hannun babbar Mai mata talla na siya.."
Na kara kallon kayan kafin nace"A ina kika santa to ke Anty..?
Anty Habiba tace"Kawata ce tare mukayi secondary school da ita..ta hannunta na siyan kayan"
Muhibba ta jinjina kai kafin tace"Tab wazai sha duk wad'anan..?