Sashe 90
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari karfe 8am na Safe ya Dauki Hanyar kaduna bayan ta bashi Cake da
cookies dinsa ya tafi dashi,Tun bayan tafiyarsa sai tayi wani Tunani Tunda yace yana makara sai ya kasance da ta tashi Sallar asuba Zata Dauki waya ta kirasa wani Lokaci sai tayi ta kira yake ji har ya iya tashi ya Dauka tana jin ya Dauka zata ce"Assalamu Alaikum Is time for Subhi Prayer"
Bata kuma kashewa sai ta tabbatar da ya tashi bayan nan sai ta kara kira taji ko yana karatu wani Lokacin har sai taji yana Karatun sannan take kyalesa,Da abun ya zame mata jiki Duka Khansum Salawatil da zarar Lokaci yayi sai ta kirasa daya Dauka sai tace"Assalamu alaikum Is Time For mangrib prayer"
Wani Lokacin ko baya kusa daya zo ya gani yasan Dalilinta,Kuma tabbas hakan ya matukar kara Taimaka ma Ibadarsa,Ko makaranta take da Lokaci yayi zata kirasa domin ta Tunasar dashi in kuma ta tashi cikin Dare zatayi salla shima tana tashinsa ranar Farko data fara tashin sa cikin barci taji muryansa Ita kuma Sai tayi amfani da Muryanta ta mace cikin Hikima tace"Ubangijin Rahama Ubangijin Bayi talakai yana gangarowa Sama ta Daya cikin Sulasain nin Dare yana Fadin"Ina bawa na mai neman Taimako na yazo ya rokeni ni kuma na amsa masa "Zaka iya tashi a farkon Dare ko Tsakiyar Dare ko Karshen Dare in har kayi alwala kayi nafila kaDaga hannu ka roki Allah to zai amsa maka Duka bukatunka..Ko ka samu da gaggawa ko yayi maka jinkirinsa zuwa gaba ko kuma yayi maka kyakyawan Tanadi Ranar gobe kiyama"
Tana jin Sautin ajiyar zuciyarsa Lokaci Daya cikin wata irin Murya yace",barakallahu Fiki ya Sayyada Muhibbba..Allah yasa a mizani"
Dariya kawai tayi mai ta katse wayar ta Daga Ranar sai ya zame musu jiki ko yana Zaria ne suna kokarin tashi Suyi sallar Dare sannan Saifudden yanzu gabadaya yaji kasalar nan dake Rikesa ya sake shi karfin gwiwa kan ibadarsa da Rayuwarsa kamar an karamai ne,Duk wannan yawan barcin nasa ya nemesa ya rasa Shi kan shi yana jinsa kamar ba shi ba kamar wani Mutum na Dabam aka Sake Ko Ummi duk da bai gayamata dayaje gaisheta ya kwana Daya taga Chanji matuka sosai aranta tayi ta saka ma Muhibba albarka su Majeeda an zama yan Abuja lesson Teacher dinta har ya fara zuwa weekend kuma yana koyar da su Laala Hatta malamin Da zai rika koya musu Na Islamiya Saifudden ya Daukan musu yana zuwa sai biyar da sati yana Fashin kwana Daya,Muhibba tana mgana dasu sosai ta waya har su Iya Tunda ta karbi Lambar Talatuwa mahaifiyar Majeeda in ta kirata takan kaima Iya su gaisa da juna Adda Sadiya ma suna mgana sun zo wani Weeked tare suka yi musu ita da Mujaheed,Sun je har gidan Inna da su sun gaisa sai Dare suka dawo Ranar Litini suka wuce kaduna da Safe tare da Saifuddeen,Muhibba sai taji kewa kamar ta Bisu aiko yana kara Dawowa Weekend ta Bishi kaduna Sai tayi sati biyu ta Dawo saboda student din su zasu fara jarabawa.
******
*Bayan wata uku*
Zuwa Lokacin kowa ya saki jiki ya kuma Dauka ma"auratan sun gama Daidaita Rayuwarsu gabadaya,Haka din ne ko basu daidaita shi gabadaya bs, Cikin kaso 100% sun sami kashi 75% na natsuwar zuciya da Ruhi da kwanciyar Hankali dukkansu sun yi kiba Saifudden ya samu kwanciyar Hankali yayi kiba ya kara Haske Muhibba ma kayanta duk sun fara matseta tayi kiba ta kara fari Saboda Sauyin abinci da ruwa da kuma mayukan jiiki sannan uwa uba da kuma kwanciyar Hankali,sannan suna da Fahintar juna Kowa yasan kowa Sannan muhibba Tsaye take kan mijinta domin cika alkawarin Ummi Shiyasa wani Lokacin"Sayyada Muhibba yake kiranta"
Abu daya ne yayi musu Sauran su zama abu daya shi kuma wannan ta bangaran Saifudden ne ya tabbata yana jin sha"awar muhibba ammh kuma ya kasa Tabuka wani abu akan haka da yayi Tunanin haka sai Tasirin haka ya fita kansa ko Hannunta baya kamawa sai bisa kuskure Daki dabam Dabam suke Rayuwarsu sai hakan yafi yima Muhibba Dadi ta gwammace ko zasu Dauwama ahaka bazata taba Damuwa ba ita ba sanin Dadin abun tayi ba shiyasa bata Dauke sa wani abu ba,Hankaluka sun kwanta kowa yana musu Tunanin Rayuwar fariciki Gaya ma da suka je haka aka rika ina za"a saka su,Sun kwana Daya gidan Kawu Sunusi ita kuma ta kwana Daya gidan su Wajen Goggo Naja ammh Ta leka gidajen su goggo Barira,Kuma sun je Bakori sai dai basu Dade ba suka gaishe su tare da alheri suka juyo Babani haka ta kira Inna tana Fadin"Daga dukkan alamu Aljanin nan ya bar Autarki..sun zo ita da megidan ta cikin aminci in sha Allahu Zasu zauna lafiya matsala bazamu ganta ba"Sai hankalin Inna ya kwanta Daman bata zauna ba bata Fatan kuma ace bayan auran Auta wani matsala ya sake bullowa Innar ma bata zauna ba, Tana yawan zuwa wajen Mallan Haruna tana baran addu"a Daga banganransa ammh ganin komai Lafiya ga kalaman Babani sai ta saki jiki ta saka aranta komai ya wuce Matsalaar Muhibba ya zama Tarihi.
Abunda basu sani ba shine wata guguwar Kaddara ne ke tafe ga muhibba karar guguwar iskar kaddarar da zatayi sanadiyar Bankado Mikakkiyar Boyayyen al"amarin dake Rayuwar"Muhi" da "SAIFF" dinta.
Wannan Hutun Su Laala a zaria suka yi mata Hutun su kwanan su goma suka je kaduna daga chan suka koma Abuja Muhibba taji Dadin zama dasu matuka sai dai sun fi Sakewa in Hamma nasu baya gari sun sha yawo a zaria sun je gidan Inna da gidan Anty Habiba Sani yazo Weekeed gida suka Hade haka suka tafi da sunan Sani a bakinsu sun ji Dadin haduwa dashi Sani ne fa ai duk in da yaje ko ya Zauna sai an tafi dashi a rai Saboda Hallayarsa na Faram Faram da barkwanci shiyasa yake da Mutane kowa nashi ne,Tun bayan Dawowar su sun koma Abuja sau Daya kwana Daya sukayi da zasu dawo suka sauka alere suka gaishe su Talatuwa kamar ta goya su su Laala sun zo sun kwana Biyu har da Majeeda da ta zama yan mata yar gayu da ita,kamar ba Majeeda yar lere ga ilimi ya fara Ratsata komai ta daina yinsa cikin Hauka sai cikin natsuwa Talatuwa tayi murna Goggo Atika sai jin Haushi take taso cikin ya"yanta ne wata ta Samu haka.
Yau talata tana makaranta Shekaran jiya Saif ya koma kaduna yaso ta bisa sai Saboda Students dinta Tunda Daga aji uku suka dawo ajinta suna Bukatar Karatu sosai da aka tashi gidan Anty Habiba ta wuce ta gaisheta cikinta ya tsufa tayi nauyi sai bayan La"asar ta koma gida tana komawa taga abun mamaki Sabuwar Mota Dal a Harabar gidan 307 red Colour Abun sai ya bata mamaki tun kafin ta tambayi junaidu ya fada mata wani Mutum ya kawo sakon yallabai sannan ya bada key din motar yace abata haka ta karba jikinta a sanyaye tayi ta kiran Saif bai Daga ba sai daga baya ta kirasa ta fadamai Sakon da aka kawo sai yace ta bari Ranar Friday zai dawo.
Muhibba kamar zatayi Hauka Saboda Murna da Saif ya Dawo yace mata Motar ta tace zai rika koya mata mota Ranar asabar da Lahadi in yana gari Har ta iya sai ta rika Tuka kanta zuwa makaranta karo na farko da Muhibba ta Daka Tsalle ta Rumgumesa tana Fadin"Thank you so much..Allah ya saka da alheri"
Duk da yaji kamar wuta ta jasa haka ya Daure ya riketa yana fadin"U deserve it Sayyada"
Muhibba tsananin Farinciki bai barta tayi barci ba Ranar washegari Inna ta fara kira ta shaida mawa ita kuma tana ta saka albarka har ya Habibu sai da ta kira Sani ne na Uku data Fadamai Ihu ya saka yana Fadin"Ihu ihuuu..Mun yi mota tab..Zamu shiga gari"
Muhibba tace"Kayi biyayya na rika baka aronta D'ani"Da Sauri yace"An gama Ranki ya Dade"
Anty Habiba ma ta kirata ta fadamata ta mata murna tace sai an kawo musu Sabuwar amarya su saka albarka Muhibba har Ummi sai da ta kira da Adda Sadiya sai dariya take mata jin yadda take murna.
Washegari suka fara zuwa Filin idi koyan mota kasa rike Sitiyari Muhibba tayi hannunta sai rawa yake yi saboda bata saba ba ammh haka ya dinga bi da ita Sati uku Tsakani Muhibba hannunta ya fara Fadawa,Sai dai bata fara hawa babban Titi ba sai dai cikin anguwa take kaduna tayi mai sati daya achan ta kara koya sosai tunda chan Driving school din ya sakata na kwana Biyar ta kara kwarewa shi Saboda aikinsa ba Lokaci.
Cikin Sati Biyar cikin na shidda sai gashi Muhibba ta je makaranta da Motarta Su Uncle Hafiz suna ta saka albarka Anty Usaina da Khadija sai yake suke yi ba baka sai kunne Muhibba har gida ta kai ma Inna Mota suka fito suka gani suka saka albarka sannan ta matsa ma Inna ta Tukata zuwa gidan Anty Habiba itama tayi murna matuka Ta saka albarka tace itama in ta Haihuwaa mota take so Abban walid yace mata Kada ta Damu zata samu mota Sani bai dawo ba ammh wayar sa ya cika da Hotunan motar Muhi har a Dp yana Saka Motar kamar tsohuwaar tashi ya kosa ya Dawo ya samu Dama ya hau motar nan ya shiga gari.
Duk da Hannunta ya Fada bata Tukin Dare kuma bata shige shige iyakarta makaranta ko gidan Inna La"asar nayi take komawa gida kada tayi Dare.
Ana cikin Haka wata ranar Laraba aka tashi da Rasuwar kakar su Hajiya Tafisu ta Gaya,ita tana ma makaranta Anty Habiba ta kirata tana Fada mata Tace batajin Dadi sai gobe zata tafi da Saif ya Kirata ya yi mata gaisuwa Shima Ummi ta kirasa ta fadamai ya bata izimin in da masu tafiya zasu tafi ta bisu su tafi tace Anty Habiba ce Inna da Ya Habibu an ce sun tafi tun Safe.
Haka kuwa akayi sai washegari alhamis suka tafi ita da Anty Habiba da Anty Zeenatu sukaje suka kwana Daya suka Dawo chan suka baro Inna sai an yi bakwai zata Dawo.