← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 144

Sashe 53

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafada tana kallonsa Sai ta bashi Dariya ganin yadda tayi Sai da ya Dara Cikin Dariyar ne yace"Ina zan sani ni Mujaheed..Kinsan yayan naki Bugun Junnu ne yanzu sai kiga ya aikata abunda rayuka zasu baci kuma Anemesa a rasa."
Sadiya ta mike tana Fadin"Ya Mujaheed tashi muje gidan Hamma mu Turkesa kafin ya fita."
Mujaheed ya gyada yana Fadamin "Nina nayi tunanin haka tun da ko mun kira ba samun sa zamu yi ba yana chan yana wannan barcin asaran.."
Karban Nihad Sadiya tayi shi kuma Mujaheed ya Fada Tiolet bayan yayi wanka ya shirya suka koma Falo suka karya sannan suka yi shirin Tafiya Allah Sarki Sadiya tana matukar kaunar Dan"uwanta Sai da ta Dibar mai Breakfast din su suka tafin mai Dashi ko da suka isa su Bama ne ke Zirga azirga a haraban gidan suna ganin sune suka basu izinin shiga Cikin gidan.

Falon wayan shuru kamar ba Mutane sai Tibi da yake babatu shi kadai Anan kan Center table Sadiya ta Sauke kayan Hannunta suka Fada Bedroom din Saifudeen yana cikin Farin Blanket dinsa yana barci cikin Salama yaji an Ja gashin Sajensa har sai da yaji zafi da sauri ya Bude ido Karaf sai kan na Mujaheed bai gama mamaki ba kawai yaga Haske ya Dallaremai ido hannu yasa yana kare Fuskarsa sai yaji muryan Sadiya tana Fadin"Hamma ji fa gari..Har Rana ta fito."
Sai Alokacin ya ganta ta kariso gabansa ido ya lumshe barci yayi jiya kamar Hauka Kaura suka je jiya shi da Parmanent sacetary basu dawo da wuri ba Hatta sallar isha"i da Safen nan daya tashi yayi ta tare da na Asuba,Sai ya koma jinsa yake kamar ya sha wani abu.

Kokarin komawa yake yi Mujaheed ya Fizge Blanket din yana Fadin"Mallan sai fa ka tashi."
Saifudeen ya yamutsa Fuska cikin muryan barci yana Fadin"kai fa Ajawo ne wlh."
Mujaheed yace"A jahu dai ka rika saka Min jaye mallam."
Sadiya dai tuni ta fice Saboda ta basu waje Hamma ya gyara kansa ganinsa Daga shi sai gajeren wando
Kichen ta shiga ta fara gyara masa duk da ba tarkace sai dai akwai kofuna daya bata gasunan,daman sai sun taru ne yake saka Tim ko bama su wanke mai ita ta wanke ta kai su muhallinsu ta gyara kitchen din ta goge ta fito Falon ta share shima Duk da ba Datti yana da mai mishi Shara duk Sati yau ma yana Hanyar zuwa sun Fito ne kawai sun ga Sadiya na Goge Tibin da Center table din Dake Falon da wani karamin Towel.

Saifudeen da ke sanye da Jallabiya Fara kal ya kalleta tana Goye da Nihad dake Barci sai faman aiki yake take yi Wani kayattacen mirmishi ya saki kafin yace"Addata..Allah ya yi miki albarka."
Sai alokacin ta juyo ta gansu Cikin Mirmishinta tace"Ameen Hamma ga Breakfast nan na taho maka dashi."
Zama yayi kan Daya daga Cikin kujerun Falon yana Fadin"Nagode sosai Addata..Da ma baki wahalar da kanki Auwalu na Hanya mai yimin shara da kai min wanki."
Mujaheed yayi karamin Tsaki yana Fadin"Daga baya kenan bayan ka gama Maidamin mata kamar baiwaarka."
Saifudeen yayi mai wani kallo kafin yace"Mallam ba ruwanka kada ka kara shiga Tsakanina da Addata..."
Ko kara kallonsa bai yi ba Sadiya kuma sai Dariya take yi Daman yunwa yake ji Abinci dai Rabon sa dashi Tun jiya da zasu dawo suka Tsaya a Hanya suka ci abinci Saboda ya aminta da Tsabtar wajen ne da ma"aikatansa yasa ya iya cin abinci Shima sama sama sakwara ce da Miyar agusi.

Kasa ya sauka ya Hada Tea da Kuma Soyayyan Doya daman ai Yana sonta ya cigaba ci yana korawa da Tea suna Hira sama sama da Sadiya data gama ta zauna Tana hutawa.

Mujaheed na jinsu bai saka musu Baki Hiran yan"uwan su ne na Lere yana ta Danna wayar sai chan yace"Kawu ya Kira ka man..,?

Saifudeen sai da ya Hadiye Doyar Bakinsa sannan yace"Satin nan kaf bamu mgana ba.."
Kai Tsaye Mujaheed yace"Ashe baka ma san nan da wata Biyu zaka zama Angon MUHIBBA BA."
Tea ne a bakinsa ammh yana jin abunda Mujaheed yace sai da ya Dawo mai ya fara tari ba kakkautawa sai da Sadiya ta Ruga Kitchen ta Dauko mai Ruwa ta bashi yasha tana Buga Bayansa Duk ta Rude Fadi take"Sannu Hamma.."
Mujaheed na gefe ya saka Dariya yana Fadin"Ji yadda kake wani zaran ido kamar ba kai ka kira kawu kace masa kana son ta ba."
Saifudeen ya Dago yana kallonsa Idanuwansa Jajir cikin wani yanayi yace"Ni ba cewa nayi ina sonta ba..Cewa nayi zan iya zama da ita akan yaran nan da iya take Hada ni dasu."
Mujaheed ya kalli Sadiya itama ta kallesa kafin su kalli Saifudeen din Daya Dafe kansa dayaji yana Saramai kamar zai fashe Cikin Dariyan shakiyanci Mujaheed yace"To ai gata nan zaka zauna da ita..Babanninka na Lere sun isa Gaya sun nemi auran Muhibba kuma an basu sun Biya Sadaki da komai da komai nan da wata Biyu u are Mr Muhibba."
Ya karishe Fada yana Dariya Saifudeen yaji kamar Kibiyar ta Kiftamai ta Cikin ido Gif,sai ya koma ya Jingina da kujera bai kara mgana ba Mujaheed ne ya cigaba da mai bayanin abunda Mama ta Fadamai da wayarsu da kawu ya karishe da Fadin"To kaji yadda aakayi to wlh nazo daman in fada maka ne auran nan ba kamar sauran bane in aka aura maka Yarinyar mutane ka Saketa Wannan karon wlh ko Ummi bazata Daga maka kafa ba,kawu kuma kasan sauran."
Saifudeen yaji wani Dum a kansa Shi ya fadi abun da bakinsa ammh wannan Labarin yasa yaji wani Zafi acikin jikinsa cikin wani irin yanayi yace"Ummi ta sani..?

Sadiya tace"A"a ammh kawu yace zai je ya sameta suyi mgana."
Daganan bai kara mgans ba yana ji Sadiya da Mujaheed tana mai Fadan ya kamata yanzu ya sauya domin Lokaci yayi da shi zai samu Good Family Sadiya sai Faman yabon kyawawan Hallayar Muhibba take yi duk yana jinta bai kara cewa komai ba ranar dai gidan Saifudeen sukayi wuninsu ita tayi musu girki Dayake Store dinsa cike yake da kayan abinci.

Sai Dare suka tafi Suna tafiya Saifudeen yayi wanka ko zai daina jin Zafin daya ke ji acikin jikinsa Tun Sanda Mujaheed ya sanar dashi an saka Ranar auransa.

Sai bayan ya fito wankan ya kunna wayarsa kamar ana jiransa sai ga Kiran Baffa Hayatu,yasan dai Iya ce ke Nemansa tayi mgana dashi Bai Dauka ba sai da ta katse ya Kira su da Baffan suka Fara gaisawa kafin Ya bama Iya abakinta ya karajin karin bayani Iya nata yabon karamincin Iyayen Muhibba kamar yadda su Baffa suka Fadamata bai da zabi illah Godiya da yayi mata ita dasu Baffa yace zai shigo karshen watan nan yana son mgana da ita tace shikenan suka Rabu Tana ta sakamai albarka da Fatan Allah ya jikan Mahaifinsa.

Shi daman mganar Majeeda ce zata kaisa saboda yana so ya cika mata alkwarinta In Iya ta amince Ummi bata da wata matsala.

In Saifudeen yace yayi barci to yayi karya duk yadda barci yake da Muhimmanci a wajensa ya kasa Kansa azababben ciwo ya kwana yana yi mai sannan ga Zafin Jiki kamar ana Hura mai Huta acikin Jikinsa rashin barcin yasa ya makara sai wajen Takwas ya tashi yayi salla yana da karatu da Dalibai a zaria sai dai ya Kira waya yace bazai samu zuwa ba sai wani Sati ko kankani bai samu lokacin Tunanin makomar Sabuwar Rayuwar da zai Tunkara ba.

Ko Tunanin ya shigo kansa sai kuma kamar an shafe masa A kansa sai yaji kansa yayi mai nauyin ya Fara saramai shiyasa ya sarara ma kansa da Duk abunda ya shafi Muhibba.

Sai da yamma ya samu kiran kawu yana koramai jawabin abunda ya Faru Saifudeen bai nuna komai ba sai Godiya sun rabu kan Ranar Jumna"a Kawun zai je Abuja suyi mgana da Ummi.

Daman shima Ummin ce Damuwarsa ammh Tunda kawu zai je su yi mgana yasan zata sauko shi zai amince da wannan auran Saboda Farantama mutane Dadama sannam yana jin Alamar zai iya zama da ita har zuwa wani Lokaci mai tsawo koda ba na Har Abada ba shi gabansa ne ke Fadi ko sunan ta yaji an fada ballatana kuma yaganta su hada ido da ita.
*****
*Zaria*
Ranar al'ahamis Baba Surajo ya dira a gidan su Muhibba bata nan tana makaranta dashi da duka kayan saka ranar har da buhun masara da sauransu ya taho dasu sai dai su Inna suka gansa kwatsam Ya Habibu ma na kasuwa Inna ta kira shi ta kuma Kira Mijin Habiba tace don Allah tana son ganin Habiba yana wajen aiki sai dai ya Kirata a waya ita dataji haka sai Hankalinta ya tashi ta Dauka ba Lafiya ne sai ta shirye a gurguje ta Nufi gida kusan Lokaci daya suka kariso da Ya Habibu suka iske Baba Surajo da kayan Niki niki a Falon Inna.

Bayan sun Zauna sun gaishesa ya amsa Cikin Fara"a dayake shi ya Habibu ya san da mganar da Baba Surajo ya Rattafo bayaninsa Anty Habiba ne kadai bata gane ba,Bata kara shiga Rudani ba sai da kawu ya Sauke kudi Cikin bakar Leda gaban Inna yana Fadin"ga sunan dubu dari uku da Hamsin ne..Dari Biyu da hamsin na sadaki Dubu dari na Gaisuwan iyaye sai kwalayen Minti goma da Buhun masara da gero da Shinkafa,mun saka mu su Lokaci nan da wata Biyu kamar yadda mukayi mgana dashi Habibu."
Inna ta Dauki kudin sai ta Fara Sharan kwallah Fadi take"Allah ya jikan mallam da Rahma.

Suka amsa da Ameen Habibu ta mikama kudin tana Fadin"Rike a Hannunka Habibu."
Ya karba ya rike Anty Habiba ta kallesu kafin ta dire kan Inna tana Fadin"Inna kayan auran waye wad'anan..?

Inna na Share kwallah da gefen Hijabin tace"Shiyasa nace ma Mijin ki kizo..Na kanwarku ce Muhibba D'an wajen Babanku Sunusi na Gaya yake sonta gashi har an saka Lokaci."
Cikin mamaki Anty Habiba tace"Auta ta sani kuwa..?
Chapter 53 · 0% Book details