← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 144

Sashe 68

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita dai Muhibba fitowa tayi ta neman ma kanta abunda zataci,Butar Tea din ta sabuwa ta Dauka ta Dafa Ruwan Zafi Ta hada tea tasha,Ranar ta fara shara Tunda duk kwanakin da tayi a gidan Gidan bai yi kura ba bayanta sai da ya kage Domin duka Dakunan ta gyara ta goge har Falon Farko,Dakin sa ne bata ko kallesa ba, ta goge ko'ina sannan ta Kunna Burner kamshi ya Turara gidan Tana cikin Goge goge ne a kitchen taji Shigowar Kafa Daf Daf na maza kafin tayi wani yunkuri ta fito Su bama sun fara Sauke kayan cafane a lodoji da katan katan din Ruwa da lemuka har sai da suka gama basu mata mgana ba suka Fice Sai da suka fitan tazo ta Duba kayan duk abunda ta Rubuta sai da aka Siyo sai ranta yayi mata Dadi ta Zage ta fara kwasa tana kaiwa Kitchen tana saka komai a Muhallinsa..

Harta kwai an siyo Da Naman Rago da kaji har da kifi duk ta saka shi Cikin Fridge Ranta Fes zata fara girkinta,kayan Tea ma an jiggosu su kamar su kadai ne abinci agidan tabe baki tayi domin ita har ga Allah bata Dauki Tea a matsayin abinci ba,Aranar dai Muhibba ta Fara Girkinta Jalop din Cous.cous ta Dafa mai mai Kifi ta Hada lemun kankana Saboda har dashi ta saka kuma an Siyo Gida ya kaure da kamshi Sanin baci yake yi ba bata Matsa ma kanta ba,Nata kadai ta saka sai nasu Junaidu ta Fita Haraba ta kai musu Suka amsa suna mata Godiya Madam sama da kasa na tashi a bakinsu.

Cikin wannan weekend din Muhibba girkinta take yi mai Rai da Lafiya Safe da yammah Megidan dai baya kwasan wannan garan daga ita sai su Bama da su kansu sun fara shaida Oga yayi aure,Shiko In ya fito da Safe ya sha Tea sai kuma wani Daran ko kallon abincinta ba yayi saboda kyamkyami garesa bakowa ke girki ya ke iya ci ba...shirin komawa Kaduna yake yi Gobe Litina yana Da shiga Office agoben,Bai wani ji ya Takura ba Tunda ba cika ganin Muhibba yayi ba kowa harkan gabansa kawai yake yi acikin gidan adaran sukayi mgana da Ummi kan komawarsa kaduna Ummi tace itama Muhibban zata koma makaranta goben kamar yadda da sukayi mgana da Safe ta Fadamata ta Cinye Hutun Sati biyun da D.Musa ya bata.

Sun yi mgana da Ummi kan In ya Dawo wani sati ya Dauki Muhibba suje Lere ya kai ma su Iya yace insha Allahu sannan mganar makarantar ta ummi tayi mganar Direban da zai rika kaita yace bai yi shawaran hakan ba sai in ya Dawo yanzu dai ba now ta fara Hawa adaidaita.

Muhibba ko abakin Ummi taji zai koma office gobe,Ita bata da matsalan komai sai na rashin kwanciyar Hankali suna waya da su Inna hankalinta kwance Sani ya koma makaranta ita matsalanta D'aya mugun mafarkin datake fama dashi Abunda bata sani ba ba mafarki bane Komai dayake Faruwa Zahiri ne..Sannan wannan shine alama da Somi somin akwai manyan Jiga jigan Tashin Hankali da Rashin kwanciyar hankali da zasu kara bayyana a Rayuwarta bata sani ba.

Yanzu aka fara wasan.
*Janafty*
*SFD0025*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Tun da tasan gobe Litini tana da zuwa makaranta in ta bari wannan Firgitattacen barcin ya kwasheta bata sani ba to akwai matsala ta tabbata kafin tatashi an yi nisa da karatu in ma ba"a tashi Break ba.

Ta kuma yi lakari da barcin na kamata ne in ta zauna ko ta jingina da wani abu shiyasa Tun yinin Ranar bata yi sa a Bedroom dinta ba, a falonn ta yini Bata kuma yarda ta zauna ba tun bayan datayi sallar mangariba tana so tayi lesson plan din ta ammh kuma tana Tsoron ta zauna zence ya sha bambam sai ta Hakura sai da Safe,Kasa zama waje daya tayi data koma cikin Dakin barcinta,tana ta Zirga zirga har ta kayan da zata sanya sai da ta fiddo su hade da Takalmin da zata sanya da mayafi Saboda dai kada ta zauna bakinta kuma Dauke da Hailala Isha'i take jira a kira gabatar da ita Hade da shafa'i da Wuturi tayi alkwarin in Allah ya yarda yau sai tayi yaki da Shedan din Dake Danneta cikin Dare.

Saboda kada ta zauna adaran nan ta Tsiri wanke bayi tazo ta kara share Dakin duk da ta Tsabtace gidan Sanin zata fara Zirga zirga makaranta ba lalle ta kara zama agida ba sai Weekend.

Daman da alwalanta ana kiran sallar Isha"i ta shinfida Darduma ta tada Sallar data idar sai ta Dora da shafa'i da Wuturi,bata yarda ta zauna ba mikewa tayi a tsaye ta Karanta azkar din barci saboda kada ta zauna barci ya Dauketa Sai da ta tabbatar da ta gama ta shafe jikinta dashi Sannan ta Sauya kayan jikinta zuwa Saukakku na barci masu Taushi Riga da wando..

Wayarta ta Dauka ta kamo Suratul Maryam ta saka ta dan Daidaita Volume din yadda bazai Fita har waje ba Ta kakkabe gadonta ta hau da Bismillah ta kwanta bayan ta kashe Haskem Dakin ta sakaya kofar duk da ba da key ta Rufe ba,kwance take cikin Blanket lokaci daya muryanta na Fita kasa kasa tana bin karatun cikin muryanta mai sanyi,Muhibba ta samu natsuwar da bata taba samu ba Tunda aka kawota gidan kuma bata taba barci Cikin Salama ba Sai Ranar Barci tayi harda Saluba karo na Farko da taji kiran Sallar Hudu da Rabi na asuba,Ta tashi cikin Natsuwa da Salama da bata taba jin sa ba yau ne Rana ta farko data kwana agidan ta kwanta tatashi batayi wannan mugun mafarki ba sannan tatashi cikin Salama da Natsuwa.

Tiolet ta shiga ta Dauro alwala tazo ta tada Raka'atul Firjir,ta zauna tana ta Istigifari Kafin a tada Salla ta mike tayi sallarta bata koma barci ba Karamin Hijabinta ta Dauka da tazo da shi tun daga gida ta saka saman kayan barcinta ta nufi kitchen Ita ta kunna hasken Falon Dake hade dana Kitchen Dankali ta fara Ferewa ta soya sai ta soya kwai ta Dafa Ruwam zafi da yaji Kayan kamshin Shayi masu sanyaya makoshi.

Awa Biyu ya dauketa kafin ta gama ta kwashe nata a karamar Cooler,Sauran kuma ta zuba ma Junaidu maigadi a karamar Cooler data ke sanya musu abinci dakinta ta koma tayi wanka Ta shirya tunda har bakwai ta wuce bata so ta fara makara,Tayi shigarta Cikin Atamfarta mai kalan Kore da ja riga da sikat ne bai kamata sosai ba ammh sun mata kyau matuka cikin wanda Inna ta dinka mata ne Kitchen ta koma ta Dauko abun abin karin ta, ta zauna anan Falon farko taci ta Hada Tea sauran kuma ta barshi a Cooler in ta dawo zai mata amfani na Junaidu kuma ta bari sai zata fita gabadaya.

Ganin Lokaci bai karisa ba yasa ta zauna Tsakiyar gadonta tana Rubuta Lesson plan dinta kada taje makaranta abubuwa su hade mata,Ta dukafa kan abunda take yi bata ji motsinsa ba Ba kuma taji karar Bude kofar ba saboda ta Bude kafin ta fara Rubutun akwai nepa ita tun da tazo bata taba ganin an dauke wuta ba ko suna Daukewa ma kila cikin Dare ne bata sani ba.

Kanshim mayem Turaransa ne ya fara mata maraba a kofofin Hancinta da Sauri ta Dago daga duken nata suka Hada ido hudu dashi Gabanta yayi Rugu Rugu ya fadi Lokaci daya taji jikinta ya saki kamar ana Kassarata,sai dai kuma ta kasa Dauke kallonta daga garesa yadda yayi wani irin kyau da Tsari wanda bata taba ganin wani namiji dashi ba Lokaci Daya Haibarsa da kwarjininsa suna Dukanta suna kara saka Jikinta mazari har sai da ya gane Hannunta ya fara rawa da sai da Biron hannunta ya kwace ya fadi saman Littafin nata shi kuma bai janye kallonsa ba itama kamar an Dasata ta kasa Daina kallonsa duk da yadda kallon nasa yake kassara mata jiki..

Yana Tsaye bakin kofar Bedroom dinta bayan ya Bude kofar ya shigo Sanye yake da American Suit bakake Duka daga sama har kasa kafarsa ma Bakin Booth din Takalmi ne mai Tsada da yarari,Agogon Hannunsa baki ne na kamfanin Rago Kansa ya sha gyara yana kyalli sai Hannunsa guda daya Dauke da Tap dinsa da wayoyinsa guda biyu dayan Hannun kuma yana cikin Aljihun wandon Suit din dake jikinsa yadda ya isketa sai tayi mai kyau da wani Annuri daya kasa Dauke idanuwansa daga kanta.

Shima da Farko yaji Faduwar gaba ammh kuma shi Namiji ne bai nuna wani Razana ba sai dai ba shakka shima kallonta yana sakashi jin wani Sanyi na shigarsa kamar wanda Zazzabi yake son kamasshi.

Muhibba ganin bazata iya Jurewa ba yasa tayi saurin maida kanta kasa gabanta na wani Fat fat kamar wacce tayi gudun Tsere shima kan nasa ya kauda Lokaci daya yana bin Dakin da kallo a ransa yace shima yayi kyau kamfanin sun isa tsara gida ni ko araina nace kamfaninta..

Sai da ya gama karema dakin kallo Tsab Sannan ya Sauke Numfashi Hancinsa na shako masa kanshim Turaran wuta data,kunna a Burner cikin wanda Anty Habiba ta siya mata ne yana da kamshi Sosai.
Chapter 68 · 0% Book details