Sashe 22
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yaro ka rainani ko..?bazaka sakeni ba sai na Daka maka duka agadon baya..?
Yana jinta ammh bai Saki Hannunta ba,D'ayan hannunta ta saka tana Dukansa ta gadon bayansa ammh ko Gizau bai yi ba ballatana ya Juyo sai daya ya shiga da ita office dinsu inda suke zama Allah ya taimakesa yau bakowa Tunda Lahadi ne asibitin ba Mutane sosai suna shigowa ya saketa ya maida koda ya rufe Ummi kuma Hararan kawai yake sha Fadi take"Wlh zan saaba maka zaka budemin kofa na fita ko sai na tsinke ka da mari.?
Saifudeen ya murmusa kafin ya Duka agaban Ummi ya Dauki Dayan hannunta ya Dora asaman Fuskarsa yana Fadin"Gani agabanki Ummi kiyi ta marina har sai kin huce..!
Sai ta kasa motsi ta tsaya tana Kallonshi Cike da so da kaunar uwa ga abunda ta Haifa shi kuma yana ta lamgwabeta irin yadda yasan Lagonta.
Achan waje kuma Maman Nana nata Dariya ita da Sauran Nas dinta Kafayat ta kalla itace team na Dalibai ne masu sanin makaman aiki wato I.T,Fayels din hannunta ta mikamata kafin tace su biyo bayanta yau yan Haihuwa garesu har guda uku shiyasa ma ta Kira Ummi sakamakon itace Ke matsayin Metro babba asibitin na gwannati dake Abuja.
Ganin Ummi ta kasa marinsa yasa ya Dauki Hannunta yana marin kansa da Sauri ta Fizge hannunta tana Fadin"Baka da hankali ne..?
Kamar zai yi kuka yace"Ummi to kin k'i ki saurareni ballatana ki furta wata mgana ballata ki min fada.
Ummi ta kwace jikinta ta koma ta zauna batace komai ba Saifudden ya Rarrafa ya bita ya Dora kansa saman kafarta yana Fadin"Ummi ki yi min afuwa kamar yadda kika saba..In kikayi fushi dani ina zan saka kaina..?a inda nake in albarkanki bata tare dani wlh watarana zan lala.!
Bata bari ya karisa ba ta Dafa kansa Lokaci Daya tana fadin"Kul kar na kara jin wannan kalmar a bakinka..aduk inda kake addu"ata tana tare dakai yaro har karshen rayuwarka."
Tafada tana shafa gashin kanshi Saboda su kadai ne a wajen da ace akwai idanuwan wasu Ummi bazata iya ba,Saboda kunyar D'an fari da kuma Kunya irin ta Fulanin Zamfara.
Jin yadda ya samu Sausauci a kalaman Ummi yasa ya gyara kwanciya ajikinta yana fadin"Ummi ba"a son raina na saki yarinyar ba..In na zauna da ita zan kwareta..Zan Dauki Hakkimta ni kuma da na Dauki Hakinta Allah ya kamani gwara na Sauwake mata kamar yadda na Sauwake ma Amira afarko.
Ummi tayi Shuru batayi mgana ba Sai chan tace"Meyasa tun farko ka amsa musu kasan bazaka rike auran ba..?
Cikin Lallashinta yace"Bazasu taba Saurarata ba Ummi kuma sanin kanki ne in nayi gaddama ke zasu dora ma Laifi Shiyasa nabi Umarninsu na Farko ni kuma sai na aiwatawar da abunda yake Daidai a waj
ena..Ummi da abunda za"a zo ana Daukan lada sai kuma Bige da kwasan zunubi da Sabama Allah ai gwara a hakura dashi yafi.
Ummi tayi wani mirmishi takaici kafin tace"Ammh ai kasan ko ahakan ban Tsira ba Yaro..Iya da bafaffanika ni suka Zarga kamar yadda suka saba Goggon Atika sai da suka samu Sabani Da Mamarka zuwaira mgana bata Mutu ba sai da yaya sunusi ya dawo Lere a Washegarin da ka tafi ka barmu Cikin zullumi.
Kawai sai yaji tana Shesshekan kuka da Sauri ya Dago Cikin wani yanayi ya saka Hannayensa yana share mata Hawaye lokaci daya yana Fadin"Allah yasa bani na sakaki kuka ba Ummi.
Ummi bata san Lokacin data Hararesa ba Lokaci daya tace"Ka sani koke koke ma yaro..Ammh ni Uwa ce har da uba a wajen ya"yana musamman ma kai shiyasa tun alokacin na yafe maka kada Fushin Allah ya Sauka akanka ni kuma albarka da Yardanta nake rokon Allah ya Saukar akanka ba Fushi ba.
Saifudden ya kasa mgana illah Hannayen Ummi daya kama ya Damke yana kallonta cikin so da kaunar irin ta d"a dake yake yima Uwarsa,Cikin karyewan sauti tace"Ummi ki yafemin..
Kai ta jinjina kafin tace"Na yafe maka yaro..Na yafe maka duniya da Lahira..Sai dai ka sani banji Dadin Sakin da kayima majeeda ba duba da karancin shekarunta.
Saifudden yace"Hakane ki yi hakuri Ummi bazan kara ba
Kansa ta shafa tana Fadin"Allah yayi maka albarka.
Ya amsa mata Ameen sukayi shuru na wani Lokaci kafin tace"Ka je Lere ne..?
Da kai ya amsata mata cikin mamaki tace"Yaushe..?
Kai tsaye yace"Yau..Daga chan nake ma.,Ummi ta jinjina kai bata tambayesa ya suka kare ai tasan Halin abunda ta haifa kila ma mgana ta kare kenan shine ma ya fara bata Labarin yadda suka karesai dai bai Fada mata suna kokarin kaisa gidan mgani ba yadai fada mata Goggo Atika tace kila aljanace ta auresa yadda yake mgana cikin Nishadi Ummi tasan ya maida mganar mara amfani Cikin Kallonsa tace"ai tayi gaskiya nima na fara Tunanin haka..Domin a shekarunka bazaka guji aure hakanan ba.."
Sai Saifuddeen ya bata rai yana Fadin"Ummi Allah ki daina Daukan mganar yaran nan fa..Nasan su suka saka miki Wannan Tunanin.
Ummi tace"Eh sune ina ruwanka..?
Sai yayi gum bai kara mgana ba Ummi ta Turesa daga jikinta tana Fadi "Ni Dagani Gotai gotai dakai..Ko Laala ai bazatamin wannan kwakumar ba.
Ya matsa yana Dariya yace"Ummi ko kewata ma baki yi ba.
Ummi tace"Ina zam yi kewarka ni da ke da yammata na akusa.
Saifudden ya sosa kunne kafin yace"Ummi Bording school zan kai su Laala akallah dai zasu kara sanin Rayuwa.
Ummi ta mike tana fadin"Ban yarda ba kuma ban amince ba.
Tafada tana kara Hade rai Saifudeeen ya mike yana Fadin"Haba mana Ummi me suke yi agida ban da sakarci gwara akai su ni akaai wata ma nan garin Sulaja Ummi ai ba nisa zasu yi ba."
Ummi ta juyo tana Fadin"Ko acikin garin Abujan ne ban amince ba nace ko ana Dole ne..?
Saifudden yace"Allah ya baki Hakuri Ummi.
Bata ce komai ba ta Duka tana Duba wasu Takardu saman Teburin dake gabansu shi kuma yana Tsaye yayi shuru sai chan yaji tace"Ya aikin naka..?ka kira Dan"uwanka kuwa..?
Saifuddeen yace"Bai kirani ba Ummi Adda ce kadai ta kirani mukayi mgana."
Ummi ta juyo ta aikamai da Dakuwa tana Fadin"Kira nawa yayi maka ka kashe wayar..?Sau nawa yana zuwa Office dinka baka nan..?
Sai ya sadda kai yana sosa keya Ummi tayi yar dariya kafin tace"Allah ya Shiryeka yaro..Ka kirasa nace..Sannan har Kawunku ma ka kirasa ai shima kayi mai laifi"
Saifuddeen yace"To Ummi zan kirasu sai natsu yanzu bana cikin Hayyacina.
Da Sauri Ummi ta juyo tana Fadin"Meke damunka..?
Fuska ya kwabe kafin yace"To ummi yunwa fa..Tun tea din Safe ban ci komai ba har yanzu.
Ummi tace"Su Laala basu dafa wani abu bane ko baka biya gida bane.?
Saifuddeen kamar zai yi kuka yace"Su Laala kuma Ummi..?
Sai tayi dariya kafin tace"Oh n Tuna bari na aika asiyo maka waina nan bakin asibiti.
Ai sai Saifudden ya fara kokarin Amai tuna mai wainar wata arniyace Daka daka saboda datti itace Ummi zata ce yaci abun hannunta ganin yadda yake yi ne yasa Ummi Kwasan Dariya Daidai Lokacin da Maman Nana ta shigo ita da Uniform dinta ajikinta Green.
Ganin yadda Ummi ke Dariya ne yasa ta Juya tama fadin"Na bata Lokacin Uwa da D'anta.
Ummi ta kirata tana fadin"Dawo daman wajen ki zani."
Maman Nana ta dawo tana kallon Saifuddeen daya Harde Hannu akirji kamar zai yi kuka yana wani yamutsa Fuska Cikin Sakewa tace"Yaron Ummi lafiya..?
Ummi na Dariya tace"Daga zan mai abun arziki yace yana jin yunwa nace zan siya mai waina wajen Anna shine y fara kokarin Amai.
Maman Nana ta rike Baki Tana Fadin"Haba Hajiya kema ai da Laifinki me yaro zai yi da wannan wainar aiko ni bazan iya cinta ba ballatana shi."
Saifudden na jinsu bai ce komai Ransa Fes ganin yadda Ummi ke farinciki mgana sukayi da Maman Nana tace zata koma gida tayi ma Yaro abinci sai dai gobe ta kula da komai sannan ta Kira Metro Uwani tace tana kan Hanya.
Daganan Ummi Karamar Jakarta ta Dauka Saifudden ya karba ya Rayata a kafadarsa suka fito daga office din Suna gaba yana binsu abaya Nurses sai Kallonsa suke rataye da Jaka ko ajikinsa Suna ta gulmarsa gashi mai kyau dashi,Gaba yayi ganin Ummi ta Tsaya mgana sai daga baya ta biyosa shi ya Bude mata gidan gaba ta zauna sannan ya zagaya ya zauna bangaran Direba Ummi ta kallesa Rataye da jaka tayi dariya tana fadin"Shiyasa naga ma"aikatanmu na kallonka suna Dariya ka wani Rataya jaka kamat mace.
Saifuddeen na kokarin Tada Mota yace"Ba ruwana dasu..Ai ba jakar wata bace jakar uwata ce..!
Itama Dariyan tayi cikin Farinciki suna zuwa bakin get Jatau yana ta washe baki fadi yake"Hajiya za"a koma gida kenan..?
Ummitace"Eh sai gobe Jatau.
Fatan alheri yayi musu sannan ya Bude musu get suka fice ya rakasu da kallo Aransa yana jin sha"awarau ganinsu Cikin Farimciki afili ya Furta"Kai wasu dai suna da Sa"ar Rayuwa kaga komai achanchan kamar su suka tsara ma kansu Rayuwa.
Daga aaibitin kasuwa Ummi tace ya kaita suka shiga yana Binta kafa Kafa Dauke da Jaka sukayi Cefane shi ya Biya kudin sannan ya kwashi ledoji yakai Mota suka koma gida su Laala sun san in Hamma ya Dawo yaga Datti sai sun raina kansu baya Duka Tsallen kwado ne da Up and Down zaku sha sai kun gwammaaci duka.
Sun yi girki Couscous suka Dafa da Miyar Kifi.sannan sun share dakunan Tas sun saka Burner,Sannan sunyi wanka sun sauya kaya,sun saka Atamfa iri daya wacce Mama zuwaira ta dinka musu ne.
Ummi na dawowa sallah kadai tayi saboda suna kasuwa la"asar ta kamasu,su kuma su Laala suka shirya suka tafi Islamiya gidan wani Barrister Mu"az abokin babansu Laala ne Lokacin yana Raye tare sukayi aiki a Supreme court ya"yansa kananan sa"anin su Laala suna da uztaz din dake koya musu karatun addni nan suke zuwa suna Haduwa dasu suyi karatun.