Sashe 105
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna itace ta kira Ummi ta Fada mata abunda ke faruwa hankali tashe dazu da taga yanayin Auta din,Sai dai kamar an yu ruwa an Dauke Tunda taga Mijinta sai komai ya Lafa,Na daina Zabura da ihu da kuka da Taimakon ya Habibu aka samu nayi wanka shi kuma ya rika bani abinci abaki inaci Inna sai sharan kwallah take a boye na Tsausayin mu wunin ranar tare dani Saif yayi shi Sallah ma acikin Daki muke yin ta Tare ko nan da chan bana barinsa yaje da Mallam Haruna ya Dawo Saif yayi kici kicin yace"Mallan tun da anyi wannan ba'a dace ba gobe in Allah ya kaimu zan wuce da Muhi kaduna zan kaita asibiti a Dubata"
Mallam Haruna bai yi gaddama ba Inna ce tace"Cutar Auta ba na Asibiti ba ne Saifudeen"
Cikin Ladabi yace"To inna bakya ganin abun sai gaba gaba yake yi..?
Watarana in muka nemeta muka rasa fa..?.
Daganan Inna ko Ya Habibu basu kara mgana ba Anty Habiba ko sai dubara take min na Tashi Daga jikin Saif naki nan Duniya ban ga mai rabani Dashi ba Maallam Haruna yace"Kinga Habiba kyaleta mana"
Dole ta kyaleni ana cikin hakane sai ga Wasila da lami ina ganinta na tashi naje na Rumgumeta sai ta fashe da kuka kanta nake shafawa ina Fadin"Bata yi miki komai ba ko Wasila..?
Wasila ta dagamin kai kafin tace"Eh Anty ammh naji tsoro da na ganki kina ta gudu ina ta kiran ki baki ji ba"
Nima sai na fara kukan Saif ya taso ya Rikeni na Fada jikinsa ina Fadin"Ka tafi dani wlh nagaji..Zata kasheni"
Dakyar ya Lallasheni Lami ta zauna tana ta yi ma su Inna Jaje tana maida yadda wasila ta Fada mata Anty Zeenatu na gefe tace"Nifa ina Tunanun gidan ne ba"a so ta zauna."
Mallam Haruna na jinsu bai ce komai ba kawai kallon mu yake yi sai da yaji Ya Habibu yace"Nima ina Tunanin haka bazata koma gidan ba sai dai su koma kaduna chan su zauna tare ita da mijinta"
Saifudden yace"Nima haka nake Tunani tunda Zaman nan din ya gagara'
Haka dai aka Tsaida mgana Mallam Haruna dai bai ce komai ba sai da Saifudeen yace zai je gida ya kwanta nace bansan wannan ba sai na bisa duk inda zashi Ya Habibu ya fara kokarin hanani naki jin mganarsa karhensa sai na saka mai kuka.
Mallam Haruna na mirmishi yace"Ku kyaleta ta bisa"
Da mamaki suka kallesa kai ya gyada musu kafin yace"Ku kyalesu nace"
Jin haka yasa Ya Habibu ya kyaleni na saka Hijabina da takalmin ina rike da shi kamar zai gudu yayi ma su Inna Sallama da alkwarin gobe kafin mu wuce Kaduna zai biyo dani saboda yana so ko da Inna ne sai muje chan kadunan...
Har muka fita daga gidan ba wanda ya iya motsi sai da sukaji tashin Motarmu sannan Anty Habiba tace"Wannan gidan zata koma mallan..?
Wai meke faruwa ne..?
Mallam Haruna yace"Aljanu sune da karfin da mu bamu dashi..Bamu san menene farkon wannan al"amarin ba ammh abun da na Hango yana da girma kuma ba Faruwar yanzu ba ne na Shekaru masu yawa ne..Indai abunda nake Zargi gaskiya ne Muhibba zata Dawo in bata Dawo ba mu zamu je mu Dawo da ita"
Da mamaki suke kallonsu jijjiga kansa yayi alamun Tabbatarwa kafin yace"Tabbas wannan karon bazata sha ba..zata bayyana kanta ta yadda zamu gano bakin Zaren kada mu manta da gayama Allah mu nema mata kariya da ikonsa zai kareta"
Haka ya tafi ya barsu da wadanan kalaman da suka kashe musu jiki sai dai kamar yadda ya fada kwana suka yi sallah da neman taimakon Allah daya Tsare Muhibba sannan ya warware abunda ke Boye ya fito Sarari.,Shima Mallam Haruna kwana yayi yana sallah da Rokon Allah ya warware al"amura domin kansa ya gama Daurewa.
Allah ya anmshi addu"arsu domin Boyayyen al"amarin zai fara bayyana kansa,ko ma nace ya gama bayyana.
*Janafty*
*SFD0038*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Sanda muka bar gidan su Inna muna bayan Motarsa bakar prado din nan tasa,ina kamkame dashi kamar yadda shima yake kamkame dani tamkar Gafara junanmu ya tare damu ne.
Da farko ban d'au saunar hanyar da muka bi ba saboda a zuwa wannan Lokacin ni kaina na fara sanin kwakwalwata ta fara samun matsala ba komai na ke jinsa yadda Mutane ke jinsa ba sannan ba komai nake ganin shi yadda mutane suke gani ba.
Ban dawo hayyacina ba sai da na ganmu a Haraban gidan mu na Gra Junaidu ya bude mana bayan mota sai Faman kirari yake yi ma Saifudden Lokacin da ya rikoni muka fito ji nayi kamar zan mutu saboda Tashin Hankali makalkalesa na kara yi cikin rawan jiki da na zuciya na ke fadin"A"a bazan iya zama anan ba..Don Allah ka fitar dani wlh tace zata kasheni"
Nan da nan na sakamai wani irin marayan kuka ni kadai da al'amarin ke Faruwa dani nasan irin kwatankwacin Halin da nike ciki ganin Idanuwan su bama ya Dawo kan mu yasa ya maidani Mota shi ma ya shiga ya Rufo Rumgumeni yayi yana shafa kaina zuwa bayana cikin Sigar Lallashi,Kara rike sa nayi ina Fadin"Wlh tace sai ta kasheni..Ka da ka shigar dani zata kasheni..'
Gabadaya na Rude shima na Rudar dashi yana sakin Huci mai zafi yace"Ba wanda ya isa ya Cutar da ke Muhi matukar ina tare da ke" ya karishe fada cikin Muryansa mai cike da Zati Dagowa nayi ina kallonsa Fuska na tayi Jage jage da majina nace"To in dai kana so na Rayu ka fitar dani daga nan wajen wlh bazan iya zama ba"Sai na kara fashe mai da kuka ina Dafa Saitin zuciyata ina cigaba da Fadin"Kusan wani Hali nake kwana ina tashi acikin wannan gidan..?bazaku taba Fahimtata ba Saboda al'amarin da ni kadai yake Faruwa wlh ji nake kamar na Mutu bana jin komai Daidai bana ganin komai Daidai ji na da ganina sun Dauke gani nake yi kamar ba acikin wannan Duniyar nake ba..Ka Dauke ni ka tafi dani mu yi nesa da wannan Duniyar don Allah" Na karishe fada ina Tusa hannuna cikin Damtsen Hannunsa irin karfin rikon da na yi mai ne yasa ya Fahimci da gaske nake yi sai shima ya jijjigani da Karfi Cikin wani irin Yanayi yace"Ina kika so muje..?Kasar waje kike so mu fita Muhi..?Ko
ina ne zan kai ki matukar zaki samu salama da kwanciyar Hankali"
Cikin Zubar hawaye nace"Ni Mutuwa nake son nayi Saiff"
Da karfi ya sakeni cikin zare min ido yace"Kul bazaki taba mutuwa ba yanzu Muhi sai mun zama abu daya Duniya Daya..Mun haiyayyafa mun aurar da ya'yanmu mun tara zuru"ar da zasu zama gatanmu watarana kamar yadda muka zama gatan namu iyayen"Jikinsa na Fada cikin kuka da bansan Lokacin da ya zama jikina ba yana kara rikeni acikin jikinsa yake fadin"Ko mutuwa tazo daukan ki Muhi Sai ta fara Daukan ta kafin ta Dauke ki"
Ina jinsa yana ta mganganu yana Lallashina ni dai ban ji na samu Salama ba sai da naji yana yi ma su Bama mgana ajiyar zuciya na sauke sanda muka bar gidan acikin Sabon gari muka koma ya kama mana Hotel,da naga Hotel ne ban yi wani mgana ba Domin ni daman babbar Tashin Hankali na wannan gidan da nake jin kamar zan mutu in na koma Cikinsa,muna shiga bai barni haka ba shi yayi min wanka ya Nadoni cikin towel ya kwantar dani Bani da kaya shiyasa sai da barci ya kwasheni ya Fice farkawa kawai nayi naga baya Dakin na fara kiran sunansa a Rude ina kuka,Gabadaya a tsorace nake ina kamkame da jikina a chan kuryan gado,Sai gashi ya shigo ina ganinsa na Rugo zuwa gare sa na Fada jikinsa Ledoji ne guda uku a Hannunsa ya sake su ya Tareni ajikinsa jin yadda na Sake sauke ajiyar zuciya irin na yara cikin Rauni nace"Ina ta jin Tsoro ka tafi ka barni"Cikin tsananin Tausayi na yace"Ba tafiya nayi ba kaya naje samo miki da abunda zamu ci"
Kafa kafa na rika binsa Doguwar riga ya siyamin guda biyu sai pant da kayan barci sai brush da mayafi shima ya siyo jallabiya guda biyu da Boxers shi ya sakamin kayan barci ya kuma bani kazan da madaran da ya siyo da Hannunsa bawan Allah nan bai samu sukuni ba sai da nayi barci ya samu yayi wanka ya sauya kaya yazo yayi shafa"i da wuturi ya Tssaya a Hanya yayi sallar Isha"i kazan yaci kadan ya kora da Madara,yasan ban yi Sallar Isha"i ba ammh ganin na samu barci sannan barci nada Tsada a wajena yasa ya kyaleni.