← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 144

Sashe 135

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni kuma ina riketa da ita ina Fadin"Sannu Hajiya"
Mirmishi tayi tana fadin"Kayya..Basai nayi a hankali ba ina da ku ai nasan bazaku bari na kai kasa ba sai dai in kaiwata kasan ta ubangiji ne'
Tafada muna karisawa da ita Saman Daya daga kujerun falon su Inna tana ta binta da Sannu cikin Fara'arta tace"Bafa wani abu bane Benen nan da nayi zirga zirga ne yau..Sai da nace ma yaran nan su rabani da benen nan suka jin mganata"
Hajiya Nasara tace"Hajiya ai na zamani ne shiyasa"
Hajiya tayi tsaki kafin tace"Shiyasa nace kada wanda ya maido ni nan Kasana yafimin tunda in na Mutu a kasan za"a Birneni"
Su ummi nata Dariya Hajiya Nasara tace"Mutuwa ba yanzu ba Hajiya..Kedai Allah yasa mu dace kawai"
Muka amsa da Ameen gabadaya Inna tace"Ai da kin yi zaman ki sai mu mu sauko mu sameki"
Hajiya tace"A"a bakomai ba gashi na Hayo ba..Sannun ku da gajiya Muhibba Diyata barka da arziki."
Kaina na kasa ban yi mgana ba ta kalli su inna lokacin suna gaisawa da Hajiya nasara tace"Abokiyar zama na ne Hajiya nasara..Sanda kuka fara zuwa bata nan taje babban gidansu suna Sha'ani alokacin"
Ummi da Inna suka hada baki wajen fadin"Allah sarki"
Hajiya ta juya tana kallon Hajiya nasara kafin tace"Ga bakin da nayi ta bakin Labarin su ga Muhibba din nan kinga ta samu lafiya abunta ammh karki so ki ganta Lokacin da suka fara kawota ba yadda take"
Hajiya Nasara ta kalleni cikin Tausaya kafin tace"Allah Sarki sannu..Kin auna arziki allah ya karemu tare da megidan nata suke tafe..?

Hajiya tace"Eh mana yana cikin Samarin nan da muka gaisa da su cikin Bakin nam na Falon Mallam"
Hajiya Nasara ta jinjina kai tana ta kallona kafin tace"Allah ya tsaremu..Kin auna arziki mu Umaima sai da sukayi ajalinta Allah dai ya jikanta"
Gabadaya aka amsa da Ameen nan suka fara Hira da su Inna kamar susan juna,Ni ina gefe ina bin su da kallo su Anty Habiba ma sukan shiga Hirar sama sama duk dai kan yadda aljanu ke yin kane kane ajikin Mutane suna yadda suke so ne suke tattaunawar.

Fitsari naji ya Dauremin mara na mike na Cire Hijabin jikina Dama Doguwar rigar Wani less ke jikina ya Lafe sai cikina yadan taso ta kasa har na Shige ciki Hajiya na kallo na sai da na shige ne ta kalli su Inna tana Fadin"Ikon Allah Muhibba har da rabo aka samu..?

Ummi na Dariyar jin dadi tace"kin kusa samun jika Hajiya".

Hajiya ta washe baki tana Hamdala da saka albarka cikin jin dadi tace"Ta warke sosai abunta tayi kiba"
Ummi tace"Ta warke kam Daman wata shidda Likitan ya basu yanzu kuma kamar saura wata daya Lokacin daya diba musu ya cika Tabbas ana Tunanin komai yazo karshe"
Hajiya tace"Kai bawa na ganin Jarabawa..Allah ya tsaremu Allah ya bata lafiya ya kuma sauke ta Lafiya"
Gabadaya aka amsa da Ameen ni dai ina ciki ina jin Hirar su,da na fito daga Tiolet din gado na haye na kwanta ban fito ba ina jin Hayaniya kamar Mutane na shigowa falon suna Fita ina jin duk wanda Ya shigo sai Hajiya ta fadi sunansa ta kuma ce duka ya"yanta ne ni kaina ina ta mamakin garke Hajiya ta Haifa ita kowa D'anta ne hajiya kenan mai maida Dan wani nata.

Barci ne ya fara dauka na Sama sama karar wayata ne ya tashe ni ina Dubawa naga Saif ne cikin muryan barci na daga kiran ina Dauka yace"Kin sha mganinki kuwa..?

Sai lokacin na Tuna tun jiya ban sha ba,Sai na mutsike ido na tashi zaune ina fadin"Na manta ammh zan sha yanzu"
Cikin karya murya yace"ki tayani kula r min da kanki Muhi dita"
Cikin wani yanayi nace"In sha Allahu"
Kafin mu yanke kiran sai da yace naci wani abu kafin nasha mganin sannan muka rabu,na tashi na Duba Jakata na Ciro mganin,Guda daya ne ma saboda yanzu na daina shan su da yawa wanchan watan ma guda biyu ya rubuta mana wannan komawar ne ya bani daya sai na bangaran cikina mganin karin jini ne da na cin abinci.

Falom na fito har Lokacin Hajiya da abokiyar zamanta suna nan ganin yadda nake yamutsan fuska ne yasa Ummi ta kalleni tana fadin"Muhibba Lafiya..?

Gefenta na zauna na zube mgangunar Ina fadin"Mgani zan sha Ummi"
Inna ta tabe baki tana fadin"Shine kike ma Mutane kunkuni..?

Hajiya tayi mirmishi kafin tace"Ina da irin su marasa son shan mgani ammh ai baki ci komai ba ko..?

Kai na gyada kafin nace"Cikina a cike yake Hajiya"
Hajiya tace"A'a mgani zaki sha Haka Dokar take ko Tea ne bari a kawo miki ki Hada"
Jin haka yasa Hajiya Nasara ta mike tana fadin"Bari na saka akawo mata Hajiya"
Kafin ta mike ma sai ga wani yaro ya Shigo da gudu Hajiya ta kirasa da"Kai yusufa zo nan".

Gabanta ya tsaya yana muzurai Hajiya tace"Kai da waye kuma kake ta wani zare ido..?

Yana sosa gira yace"Hajiya to ba Iman bace ta biyo ni ba"
Yaron dan shekara takwas zuwa tara Hajiya tace"Shi ne kana Namiji kana mata gudu ita da take mace.?

Hajiya Nasara na Dariya tace"Hajiya take zane su Banu da suka girme mata ma ballatana su yusufa kannen bayanta ai kaf yaran nan Yan biyu ne kawai take shakka sai Mallam din Jafaru shima ba sosai take shakkar su ba Tafi ma raina Ya'yan Hidayan Nazir"
Hajiya ta jinjina kai kafin tace"Allah ya shirya mana ita"
Hajiya nasara na Dariya tace"Hajiya Mgaji mafiyi..Wlh Imam tsab AMINA ce babu abunda ta bari na Amina".

Hajiya na Dariya tace"Kuma gashi Sunan Zainabu abu taci mai tawagen suna"
Hajiya Nasara tace"To ai Amina ce uwarta Hajiya"
Gabadaya akayi dariya har da su Inna yaron na Tsaye sai leke yake alamun a tsorace yake Hajiya ta make mai keya tana fadin"Kai sakarai sauna ina iyayan ka suke..?

Kamar yayi kuka yace"Suna Downstar fa Hajiya"
Baki ta saki kafin tace"To ya"yan Turawa"
Hajiya Nasara na dariya Adda ne ta kwace sa tana fadin"Suna kasa yace Hajiya"
Hajiya ta tabe baki tana fadin"To kaji wani salo wai donstar.."
Dariya akayi har nima sai da na Dara yaron kawai nake kallo Fari tas da shi Daga ganinsa ya hada iri da Fulani.

Hajiya tace yayi maza yaje ya kira mata Amina ko Hanne cikin su dai kin fita yayi yana ta Rabe rabe Hajiya ta Daka mai Tsawa sannan ya fita da Gudu Ummi nata Dariya Inna tace"Kinsan fulani akwai tsoro"
Hajiya Nasara tace"Ki shi Hajiya ke yi fa domin yace ba yayi da ita sai ni"
Hajiya ta tabe baki kafin tace"Sai me..?

Ni da ke da Zazagan magidanta jarumai ba irin sa ba yana fama da Fari kamar Ubansa"
Har ni sai na Dara Hajiya Nasara tace"Ai da kin ga Yusufa kinga Aminu..Da Nenne ko Hannen tamu ta Idanuwa ya Debota"
Hajiya tace"In kin lura har karamar su Amina itama Nenne ce sak"
Kafin su kara cewa wani abu sai ga Wata Farar mace ta shigo Doguwa mai yalwar Fara'a tana shigowa Hajiya tace"Uwar sa ya kira kenan..?.

Da sauri na Daga ido ina kallonta sai da suka fada naga idanuwan su kuwa iri Daya ne cikin Dariya har Hakoran makkanta suka bayyana tace"Hajiya megidan naki kika bangara yazo yana min kukan kin Dage sa"
Hajiya tace"Kaji sharri..Diyarku ce ta bugesa ni sawun barawo na taka"
Hanne tace"Hajiya kada fa ki Dawo kina mana yar murya"
Hajiya tace"Allah ya kyauta min"
Akayi Dariya gabadaya tayi ma su Ummi Sannu da gida ni kuma Taga ina kallonta sai tamin mirmishi kafin ta kalli Hajiya tana fadin"Hajiya gani yace inzo kina kirana"
Hajiya tace"Tea zaki hado ma Muhibba zata sha mgani"
Hanne ta kalleni kafin tace"Ok itace mara lafiyan ko Hajiya..?

Hajiya tace"Eh ammh ta warke..Kun shigo dazu tana ciki."
Hanne ta kalleni kafin tace"Sannu bari na kawo miki"
Ta juya zata fice Hajiya ta kirata ta Juyo tana fadin"Ina mamah ne ban ganta ba..?

Hanne tace"Muna kasa tare da ita bari nayi mata mgana da tare zamu shigo su Anty Sakina ne suka shigo yanzu"
Hajiya tace"Su kuma basa tashi Fitowa sai dare ko tsoron Titi basa yi"
Hajiya Nasara na Dariya tace"Hajiya ke kike Tunanin haka su ina ruwan su balle Daga Sakinar har Saratun sun iya Mota fa"
Hajiya ta tabe baki bata kara mgana ba Hajiya nasara na cigaba da gayamata su basa tsoron dare balle ai kusa suka Dawo yanzu ba Nisa.

Ba jimawa sai ga Hanne ta shigo da kayan Tea da Flaks da Kofi ta sauke a gabana nayi mata sannu ta amsa cikin Mirmishi.

Tana shirin zama kusa da ni Hamida wacce muka fara ganin Tun farkon zuwanmh ta shigo da waya a hannunta tana Fadin"Hanne Mijinki na kira"
Da Hanzari ta mike ta karba tana Fadin"Bawan Allah duk yau yaji ban nemesa ba"
Ta kara wayar akunne tana Fadin"Aminullahi na"
Hamida ta sakar mata Duka abaya ta bangare tana fadin"Hajiya kin ganta ko..?.

Hajiya tace"Ba Hajiya ba Amunullahi na kaganta ko zaki ce..?

Gabadayan mu muka saka Dariya itama Dariyan ta saka ta shige Cikin Dakin da na fito tana Cigaba da wayarta bayan shigarta ne Hamida tace"Hajiya su Anty Sakina sun zo..Kema Anty Nasara sun je Shashen ki baki nan su kariso nan ne..?

Hajiya tace"Eh mana sa gaida ma baki gasu nan".

Ta juya kenan suka ci karo da wata mace da ta sawo kanta Dakin,Ina kokarin Hada tea naji muryanta tana Fadin"Hamida kin kasheni..".

Hamida na Dariya ta harareta kafin tace"Muka kashe juna dai nima ai goshina na Mutane ne naji zafi"
Dariya suka saka atare kafin Hamida tace"Ina Sauran yan"uwan naki AMINA?
wacce aka kira da Amina na kallah tana mgana cikin Haraara"Ina da yan"uwa da Dangi da ya wuce ku ne..?

Hamida bana son iskanci fa"
Hamida ta rike baki kafin tace"Su Anty Sakina fa ba yan"uwanki ba ne kishiya ai yar'uwa ne Aminene"
Yadda tayi ne yasa sai da su Hajiya suka Dara kwalar Hamida taci tana Fadin"Zan miki rashin mutumci Hamida..ke ki bari in Sadik ya kara aure sai ki samu yar'uwa"
Hajiya ta gyada kai tana Mirmishi tace"Mamah kyaleta kin ji ko..?

Baki san yanzu kun girma ba ne..?
Chapter 135 · 0% Book details