Sashe 139
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuma mganar ma zuwa jego ko Haihuwa gida kada ma ranki ya baci Saboda haka bafa Addini ba ne ko Farillah ba,Al'ada ce tun ta Mutanen da..Kuma yanzu zamani yazo duk an Daina matsa ma kai akan wannan al'adan ta zuwa wankan gida Saboda Tarin matsalolin da hakan suka Haifar..Ni in da zaki ji Shawarata ki zo nan Zaria in nan din kike so ki haihu kuna da Gidan ku,ku kakkabe sa a gyara muku ki
Haihunki ki yi jegon ki anan abun ki in kin yi arba"in sai ki koma Kadunan ki wanda kuma zai zauna ya Kula dake baza'a a rasa ba Ni lokacin Haihuwan Khalipa na Dawo gida Sati Biyu nayi iyayan Abban walid suka ce na dawo gidana kuma na Dawo Sai dai Babani tazo ta zauna dani har nayi arba"in ta kula dani Sannan ta koma Gida yanzu kuma bata da Lafiya kuma Inna bata da kamarta ki yi mata uzurin ta zauna ta samun Ladan Jinyarta Auta don Allah ki cire Damuwa aranki ki samu ki Haifi abunda ke Cikin ki Lafiya".
Kai na gyada kafin nace"In sha Allahu Anty Habiba in muka koma gida zan Tuntubi Saif naji in ya amince sai nazo nan din na Haihu ni ina so na Haihu kusa da gida ne Anty Habiba"
Anty Habiba tace"Ba matsala..Kuna da gidan ku hakan ma sai yafi miki akan ki Dawo gida domin ko kin Dawo Inna bazata yi miki jego ba Dole dai wata za'a neme miki"
Gabadaya na aminta da mganar Anty Habiba shi yasa sai na cire bacin raina sannan naji Kullatan da nayi da Inna ya saukar min,na saki jikina muna ta Hira da Anty Habiba da Babani ta farka muka koma Dakin Inna muka Dubata ta gane ni ta kalleni ta kalli katon cikina cikin muryan Ciwo tace"Fatima Yan uku Autar taki zata haifa..?
Gabadayan mu sai da mukayi Dariya,Inna taki mgana Sai Anty Habiba ne tace"Daya ne Babani..Kuma ke zaki karbi Haihuwar ki yi mata Jego gwara ma ki mike tun da wuri"
Tana Dariya na ciwo tace"Kayya zan so haka sai dai Ina Habiba daga gani wannan Ciwon Ajali yake nema"
Daganan sai jikin mu ya yi sanyi da kalaman Babani bamu kara mgana ba sai Inna ne ke mata mganar ta daina Fadin haka Mutuwa da Rayuwa duk ta Allah ne..
Ina gida har bayan La'asar sannan Saifudden ya Dawo yayi ma su Inna sallama bayan ya ijiye mata kudi mun tafi ko Ya Habibu ban gani ba Sani kuwa chan bakin Layi muka gansa a majalisarsy yana ta zuba uban zence shi da abokansa yan anguwa bai ma gammu ba sai da Saif yace Bama ya Tsaya aka Danna mai Hon sannan ya Juyo yana ganin Motar mu ya gane mu ne ya washe baki ya mike yana ce ma sauran abokan"Mai girma kwamishina na kira na bari na dawo"
Suka bisa da kallo wasu har suna Leke kowa ai yasan Kwamishina ke auran kanwarsa.
Ta barayin Saif ya zo bayan an sauke gilashin barayin Sani ya daga babban yatsansa alamun jinjina yana fadin"Allah ya kara lafiya ranka ya Da"ade ka dade kayi karko kune ilimin..Gwammnti ne da Kafafunta"
Saif yayi dariya kafin yace"Kana Lafiya Barrister..?
Sani ya sosa kai yana fadin"Sai Hamdala Ranka ya Dade zamu ce"
Saif yace"Madallah"
Lokaci daya ya juyo yana kallo na ni kuma sai na Tamke Fuska na kalli gefena ya kalleni ya juyo yana kallon Sani,Kafin yayi mgana Sani yace"Ita wanchan me akayi mata take juyar da fuskar tana cika kamar alkubus din dayaji yis"
Ina ji Saif na Dariya shi da Sani a fusace na juyo ina fadin"Ba alkubus ba Saura Famke"
Sani ya tabe baki kafin yace"Ai duk Daya Ba maraban su"
Hararansa nayi ina kauda kai Saif ya kallesa yana fadin"Me ka yi mata?
Sani yace"Daga na gayamata gaskiya..Tsakani da Allah hancinta bai yi maka kama da Bulunbuton yara ba...?
Saif ya Juyo ya kalleni sai kawai naji ya kwashe da Dariya yana Fadin"Kuma wlh gaskiyan ka"
Na juyo ina kallon su har da Tafawa Saboda abun yayi musu Dadi raina ya baci takaici ya Rufeni sai kawai na saka musu kuka Suka kalli juna Sani yayi baya yana Fadin"A"a kuje kawai Ranka ya Dade yarinyar nan yar sharri ce ni me nace miki da zaki sakamin kuka..?
Saif na Dariya yace"Kyaleta daman kiris take jira..Zamu yi waya Barrister"
Da toh ya amsa mai yana Daga mana Hannu muka wuce bayan an zuge glass din da aka Daga,Sai da muka wuce sannan Sani ya juyo yana Sauya tafiya shi a dole yasan kwamishina Taafiyarsa ma ta Musamman ce.
Saif ya so ya tsokane ni naki bashi Fuska Dole ya kyaleni har muka kai gida Ranar Kwanciya ma kai da Kafa mukayi ya yi ta bani Hakuri naki Hakura raina bace nace"Har kai ne zaka hada kai da Sani kuna min Dariya..?
Ya marairaice yana Fadin"Ni fa kawai yace hancinki kamar Bulunbutin yara ne,ni sai kuma na kallah naga gaskiya ya fada shikenan abunda nace fa"
Yafada yana Danne Dariyansa Takaici yasa na Bude baki ina kallonsa aiko ya Daku domin duk abunda yazo Hannuna na Dinga Raruma ina Dukansa dashi daya kasa kwatan kansa ya mike ya fara zagayen Dakin ina Binsa karshe mugunta ya Hadamin Domin yasan bazan iya Gudu ba sai ya shammaceni yaja Hancina yana fadin"Bulunbot.."
Sai na Bisa sai ya gudu ni kuma bazan iya Gudu ba, Cikina yayi nauyi karshenta dai kasan Cafet na zauna ina Haki domin Allah na gani Saif yafi karfina ammh na Kudiri niyar rama duk Wulakancin da yayi min in na Haihu.
Sai da muka kwana Biyu da Dawowa Zaria sannan nayi mai zencen komawata gidanmu na zaria na Haihu yayi shuru bai yi mgana ba yana kallona yana Breakfast ne zai tafi Office,Har ya fice bai ce min komai ba sai jikina yayi sanyi na zata bazai amince ba ne sai da ya Dawo gida da daddare yaci abinci yayi wanka sannan yayi min mganar Tambayata ya fara yi na fasa komawa Wajen Innar ne..?
Kai tsaye nace"Saif Abubuwan sun ma Inna yawa ga Babani gani..Bazata iya ba shiyasa na yi shawara da Anty Habiba gwara na koma chan na haihu sai a samu wacce zata kula dani"
Kai Tsaye yace"Meyasa bazaki Haihu anan ba Muhi..?
Kai tsaye nima nace mai"Saboda na fi son kusa da gida ne Saif"
Shuru yayi kafin yace"Is ok..Sai dai ni zaki bari ni kadai..Zan yi missing dinki exopecially dis ur Nose"
Ya fada Lokaci daya yana Jan min Hanci make hannunsa nayi Lokaci daya na saka Hannu na Tsingulesa a Damtssn Hannunsa.
Zafi yaji ya yarfe Hannun yana Fadin"Ni mintsin ki nayi..?
Mikewa nayi Dakyar Daga kan kujeran da muke zaune na Tura Cikina gaba na wuce ina Fadin"Im mutum yayi maka mugunta in yafi karfinka kana da Damar da zaka rama Duk ta hanyar da kaga yafi maka Sauki Daga yau ka na kara tabamin Hanci sai da kaji Mintsini"
Na fada har ina Cije mai baki Dariya yayi yana Fadin"Tare zamu koma Zarian Muhi kema kinsan I can stay here"
Na Dauka wasa yake yi ashe da gaske ya ke yi,Hatta Ummi ni da kaina na Kirata na Fadamata tace yayi daidai Sannan tace mu tafi da Zeeha Wasila Tunda tana makaranta ta zauna gidan Adda Sadiya Inna ma Anty Habiba ke Fadamata Ranar da ta biyo gida ta Dauki Anty Zeenatu suje su yi mana Share share aaboda cikin Satin nan nace mata zamu Dawo..
Inna Tayi shuru kafin tace"To wa kike ganin zai zauna da ita..?.
Anty Habiba tace"Ni naga ki kira Goggo Barira ita ke da abokan zama nasan Hakimi bazai hanata ba ki yi mata mgana kiji"
Inna ta amince da hakan ta Kira Goggo Barira suka yi mgana tace bakomai zasu tattauna da hakimi Tasan ma bazai hana ba washegari sai gashi ta Kira Inna tace ya amince da Zarar na sauka Lafiya zata shiryo tazo.,Inna da kanta ta kirani ta Fadamin sai naji Dadi na kuma kara gasgata mganar Anty Habiba Naka sai naka Dadin zama sai bare.
Cikin Sati dayan muka gama parking din duk abunda zamu bukata gudun mgana yasa na Kira Iya da kaina na Fadamata iya yanzu tayi Laushi sosai,Albarka kawai ta saka da Fatan Sauka Lafiya da Saif ya Dawo na Fadamai mun yi waya da iya tabbas naga yaji Dadin ashe kowa na son nashi komai Lalacewarsa..?
Wasila bata so tafiyar nan bata ba, na nuna mata Saboda karatunta sannan in na Haihu zata zo suna kuma ai ba zarian zan koma Gabadaya ba zan Dawo..ita da Laala sun cizi yatsa Mama zuwaira ta Koma gaya Adda na yin arba"in su Laala kuma sun rubuta Jamb bai yi kyau ba ne Saif yace sai wata shekarar su kara Rubutuwa tukunnah Shiyasa suke kaduna basu koma ba Majeeda tazo ta kwana Biyu ta koma Saboda makaranta.
Na samu rakiyar Adda Sadiya da Laala sai ni wasila da Zeeha,Motata nan Kaduna na barta a motar Saif Bama ya Tukamu,Saif kuma sai gobe zai taho Yace suna da Taro Siyasa ta matso Gwamna Abdulhadi Datti ya kara neman takara a Tenure na Biyu.
Koda muka Isa Direct GRA MuKa sauka Allah Sarki sai na Tuna Sanda na bar gidan nan a firgice sai ga shi Cikin Kuduran Allah na Dawo da kafata da Lafiya Junaidu kamar an bashi kujeran makka sai Lale maraba da Dawowata yake yi,Saboda Dalilin Dawowata Saifudeen ya Dawo dashi bakin aiki.
Gidan na nan Tsab sai ma fulayoyi da suka girma mun iske su Anty Habiba da Anty Zeenatu har da Baba Lami sun gyara gidan yana tashin Kamshi,Har girki sun yi mana Dayake sun taho da Cefanen su.
Sai da muka ci abinci muka natsa sannan suka shiryamin kayana a Bedroom dina mai Falo inda zan zauna koda na Haihuwa Dakin Saif kuma yana nan a zaman nashi Sai kallon ko"ina nake kamar bakuwa na Dauka zan ji tsoro sai dai ban ji komai ba na Riga na Dauka ma kaina cewa Abunda ya Faru dani ba Gaskiya ba ne wani abu ne kamar mafarki shi kuma mafarki ba zahiri ba ne...