← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 144

Sashe 82

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Siyayya Adda Sadiya tayi na kayan abinci shinkafa,Couscouss,Taliya,Macaroni,Kayan magi kala kala komai dai sai ta Siya kwai,Bama ne da sauran su su madara kayan Tea daidai misali Daganan suka shiga kasuwa ta siya mata su cabge da su green beans Peaces Carrot da su Allayahu Nama kifi,Tomatur din leda da na gona kayam Miya da sauran su har da Doya lokacin data siya Doya mai yawa Muhibba tace"Adda Doyar nan tayi yawa fa..?

Duk da bata Fada mata ba jikinta ya bata nasu ne kayan abincin nan.

Adda sai ta biya kudin Doyar suka bar wajen su musu Dako ya hada Cikin Kuran sauran siyayyansu sannan Tace"Kina wasa ne..Ai best Food din Hamma ne Doya..Ki Sarrafata ta kowacce Siga u are wlcm"
Muhibba tayi Dariya batace mata komai ba
sai da suka gama duka Siyayyan sannan suka koma wajem motarsu Booth sai da ya cika har baya Rufuwa sai da suka Dauki hanya ne Sadiya ke ce mata"Na kara miki wasu kaya fa..Naga kamar baki zo da kaya da yawa ba.

Muhibba ta tura baki kafin tace"Hamman ki ne yajamin shi yace kala Biyu ya isheni ashe mugunta ce"
Sadiya nata Dariya Muhibba na lura da Hanya ganinsu kofar wani dan madaidaicin gida mai bakin get yasa tace"Nan kuma wata anguwa ce Adda..?

Sadiya tace"Anguwan Sarki kenan nan gidan Mijin ki ne gidan Hamma na kaduna"
Jinjina kai tayi tana bin gidan da kallon har Adda ta Danna Hon sai kuma ta jawo wayarta tana Fadin"Na manta gidan Hamma ba maigadi"
Sai dai abun mamaki sai ga wani inyamuri ya fito Daga gidan ta gaban Window din Gefen Adda Sadiya yazo sai ta Bude cikin mamaki suka gaisa cikin Harshen Turanci ya tambayeta Daga ina..?

Tace bakin Ogansa ne Sunanta Sadiya kanwar megidan ce kusan inyamurai da rashin yarda sai da ya koma gefe ya Kira Saifudden ya rattafamai bayani shi kuma yace ya bar su su shiga,sannan fa ya Bude musu suka Sulala ciki Adda sai masifa take yi tana Fadin"Hamma yayi ta Dauka Inyamuran masu gadi...Kaji mutum sai kace waau barayi.."
Muhibba sai Dariya take yi shi din dai Da Adda ke masifan ya kwashe musu Siyayyan nasu zuwa Cikin gida shima kamar na zaria ne Falo da kitchen da Bedroom guda uku Falo guda Sai ta bayan Kitchen inda Tanki yake da Famfo,Sai dai gabadaya kura yayi yawa agidan,Duka Dakunan suna Bude ne Dakin sa ne yake da gado da Wardrpe dayan Dakin Sai Cafet da katifa a kasa Dayan kuma Cafet ne kadai shimfide a dakin.

Afalo suka samu suka yi sallar La"asar Adda Sadiya ta taimaka mata suka Zage suka gyara gidan gabadaya suka Share suka yi mopping suka fesa Airfreesher,da suka samu agidan ko da suka gama duk sun gaji saboda aikin fa da yawa,Suna gamawa suka koma gyaran kitchen shi kam sai da suka wanke shi duk yayi datti suka goge ko"ina akwai gas cooker mai shidda sai dai ba kayan amfanin girkin mata Adda Sadiya tace zata kawo mata nata kafin a siya wasu,Sai da suka gama jera duka kayan da suka siyo a mahallinsu sannan Adda Sadiya ta koma gida ita kadai tazo ma da Muhibba da Sabbin Tukwane da Robobi da kofuna da File filet da Cokula da duka abun amfani da Coolers masu kyau ta Dauko mata blander tunda tana dashi guda uku sai ta Dauko mata Daya kaya fa ta Dibo masu yawa har Muhibba na Fadin"Ita fa..?

Adda tace"Ai tana da su da yawa ne shiyasa ta fara amfani dashi kafin ta karo nata.

Da haka suka Zage da aikin Sakwara Adda Sadiya tace zata taya su yi kafin ta koma gida tare suka yi aikin da ba Domin Adda ba da bazata iya ba a karamin Turmin karfen da Adda tazo mata dashi ta Daka Sakwaran miyar kuma miyar allayahu suka yi mai Nama,sai suka Hada Lemun kankana sai mangariba suka gama aikin nan Adda Sadiya ko Salla bata tsaya yi ba tace sai taje gida Muhibba tayi tayi ta Diba Sakwaran taki Gudu gudu Sauri sukayi sallama ta hau motar ta wuce bata so ya Mujaheed ya Dawo bata a gida.

Muhibba kuma sai ta shiga wanka bata Takura masa ba Dakin dake da katifa a kasa ta kai kayanta nan ta shiga tayi wanka ta sauya kaya zuwa doguwar riga Less na Adda Sadiya ne Cif Daidai jikinta kamar don ita akayi kayan Ta Daidai ci gabas ta Tada Sallah Dayake akwai wuta Tun da suka zo haske ya gauraye ko"ina.

Tana nan zaune har aka kira sallar isha"i abun ya Burgeta akwai masallatai a kusa dasu kamar acikin gidan ake yin sallar har jam"i ta bisu.

Bayan ta Idar ta kashe Daurinta ta Feshe jikinta da Turare ta koma Falo ta Zauna ta kunna Data sakonni na shigowa Karfe Takwas da Rabi Daidai taji karan Bude get da shigowar Mota gabanta ya fadi Ras ko bata Duba ba tasan shi ne ya Dawo.
*Janafty*
*SFD0030*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Ganin ta kasa samun natsuwa ne yasa ta fara karanta Hasbunallahu acikin ranta kafafunta har shaking suke yi Saboda Fargaba minti Biyar tsakani aka bude kofar afalon ya sawo kansa cikin da irin salon tafiyarsa Bama na biye dashi a baya Dauke da wayoyinsa da Tap dinsa Sai dai me?

Kamshin daya ziyarci hancinsa shi ya sa ka mai wani ni"ima da karsasashi bai san Lokacin da ya tsaya cak ba har yana Lumshe idanuwansa kafin ya Bude su Falon ya fara bi da kallo har zuwa Lokacin da ya Sauke idanuwansa a kanta tana zaune ne ganin ya ganta yasa ta mike Tsaye da Sauri kanta na kasa jikinta na rawa kadan.

Ganin ta kawai da yayi sai yaji wani Sanyi har sai da ya saukar da ajiyar rai sai kuma yaga Falon yayi mai kyau fiye da ko yaushe Gaskiya ne da ake Fadin Mace itace gida in bata gida ya zama kango.

Ko bai Fada ba ya riga ya sani Muhibba tana da Muhimmanci a Rayuwarsa yau kaf bai yi wasa da Sallah ba Kasalar data kan rikesa yau bai ji ta ba Cikin jam"i yayi sallah Sai kuma yaji yafi samun natsuwa kan yayi ta shi kadai matukar kunya zai ji Ranar da Muhibba ta san komai a kansa tasan bayan Rauni akan Ibada har ta Addinin ma bai san shi yadda ya kamata ba.

Sanin da yayi Bama na bayansa yasa yaki Motsawa sai kawai ya mika masa Hannu yasan mganar sai ya Doramai wayoyinsa saman Hannunsa kafin ya Saramai ya juya ya fice Daga Falon shi kuma ya fara taku zuwa Cikin Falon.

Ya tuna yanzu nan yana Hanya Mujaheed ya kirasa yana mai masifan yasan bazai zauna da matarsa ba meyasa ya kawo ta Kaduna..?Sai ya bar na shi matar har takai Dare a gidanshi Kuma yasan ya Hanata Driving din Dare bai biye masa bane saboda baya cikin Mood din alokacin Ammh shi kanshi yasan duk cikin Kannensa Adda ta Daban ce she care For him kamar yadda take kula da kanta.

Da Farko yayi kamar bai ganta ba ganin bata yi wani motsi ba sai kawaii ya kama Hanyar Dakinsa Ciki ciki yaji muryanta"Sannu da zuwa.."
Kamar bazai tsaya ba sai dai ya Tsaya Lokaci daya ya juyo ya kalli bayanta kafin yace"Thank you"
Da haka ya shige Dakinsa sai da ta tabbatar da ya shige Sannan ta Sauke Numfashi ta koma ta zauna ta Cigaba da Duba wayarta da Anty Jidda suke Charting tana tambayanta ko tana Lafiya yau bata shigo makaranta ba..?

Sai ta sanar da ita bata gari ne tayi tafiya bata matsa sai taji in da taje ba, tayi mata Fatan Dawowa Lafiya Uncle Hafi sun yi mgana shi kirari ya fara mata da Matar kwamishina girman ki ne.

Tana Dariya ta tambayeshi Student dinta yace bata da Damuwa akwai Teacher dake kula dasu.

Charting ya Dauke mata Hankali har bata san ta Dauki Lokaci mai Tsawo ba Sai da taji kamshin Turaransa a Kusa da ita sannan ta Dago kanta suka Hada ido ya sauya kaya alamun yayi wanka ya saka Farar Jallabiya Kau da kanta tayi aranta tana Fadin shi dai Daga Fari sai baki haba dai.

Akwai karamin Frige a Falo nan ya isa ya Bude ya Dauko Ruwa sannan ya Dawo ya Samu kujera mai zaman banza ya zauna ya Dora kafa Daya kan Daya sannan ya Bude ruwan ya Fara sha Kadan kadan..

Ita kuma sai ta kasa Danna wayar ta koma Ta Lafe samam kujera jikinta na rawa bai kalleta ba taji yace"Ya gidan"?

Sai da ta waiwayo ta kallesa taga Hankalinta baya kanta sannan ta maida kasa a Hankali tace"Komai..Komai lafiya"
Jinjina kai yayi kafin ya mike yana Fadin"Addata ta kai Dare ne kafin ta tafi..?
Chapter 82 · 0% Book details