Sashe 42
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Junaidu ya zube yana gaishesu domin duk da bai taba ganin wani yazo gidan ba ammh ganin Ummi sai ya shaida kila yayar yallabai ne domin shi bai ga tayi kama da Mahaifiyarsa ba, Saboda yanayin jikinta Ummi ta amsa mai cikin Fara"a da sakewa tana kara kallon yanayin gidan aranta ta kara tsinkewa da lamarin yaro.
Mujaheed ya tambayesu ko Saifudden na ciki kafin Tim ya amsa Junaidu ya amsa mai da cewa yallabai na ciki Tun jiya da suka shigo bai kara Fitowa ba.
Yana daya daga cikin Hallayar Saifuddeen na sakaci da Ibada bai Damu da Ibada ba,Khamsil salatun ba kowani Lokaci yake yinta cikin jam"i ba,Sannan ba kan Lokaci ya kan yi su ba,Ban da su ko Nafila bai da kokarin yi,ballatana azumi da sallar cikin Dare Shi banda Ramadan da suka Zame mai Dole baya iya wani azumi duk da kuma yakan wuni da yunwa bai ci abinci ba,Yana da rauni matuka wajen Ibadarsa bar shi da karatu da bama aiki muhimacci sai barci su kadai ne aikinsa.
Haka su Ummi suka rankaya cikin gidan Falon ba kowa sai talabijin dayake tayi shi kadai ga wayoyinsa nan zube kan kujera tun jiya bai kara bi taa kansu ba,yana cikin Dakinsa yana Fama da kansa har waye garin yau abunda ya faru ya kasa bace mai sannan Fuskar Muhibba da yanayin daya shiga lokacin data rikesa ya kasa bacewa acikin ransa.bedroom
uku ne aciki Falon sai da suka shiga duka Biyun ba kowa aciki kafin su danganta dana karshen suka samu Saifudden kwance cikin Farin Blanket dinsa,barcinsa yake yi hankalinsa kwance kamar ba abunda ya faru mujaheed ya kalli Ummi itama ta kallesa Cikin jin haushi tace"Tashe sa.."
Duka ya d'aka masa da karfi Sai da Saifudden ya mike a firgice,sai dai wad'anda ya gani ne yasa ya kasa Motsi Cikin mamaki yace"Ummi..Man..!
Ummi ta ballamai Harara kafin tace"Sauko mallam bana ma son wata mgana."
Ba musu ya yaye blanket din ya zuro Tattausun kafafunsa kasa ya mike jikinsa ba riga sanye yake da Karamin bakin wando Three quater Da Sauri Ummi ta kauda kai domin Tsarin Hallitarsa ya bayyana Cikin bada Umarni tace"Ka shiga kayi wanka ka shirya kanka minti talatin na baka.
Saifudden ya kalli Ummi da mamaki kafin yace"Ummi..!
Hannu ta dagamai tana Fadin"Kada ka batamin Lokaci ina jiran ku afalo.
Daga haka ta fice ko waiwaye,Tana fita Saifudden ya kalli Mujaheed dake gefe ya Harde hannu saman kirji yana kallonsa cikin mamaki yace"What all dis Man.?in ma zaka zo why zaka Dauko Ummi..?
Mujaheed bai ce mai komai ba agogon Fatan dake hannunsa yakai duba kafin yace"Ka fara cin Lokacinka..Kada ka batamana Lokaci.
Ya fada yana Hade rai sai ya ma ya fito da wayarsa yana Dannawa Dole yasa Saifudden ya kwashi jikinsa ya shige Tiolet Mujaheed ya rakasa da kallo aransa yana fadin"Dan rainin Wayau kawai."
Minti goma Saifudden ya kwashe a Tiolet sannan ya fito,Yana digan ruwa a saman kansa da karamin Towel yana goge Babban kuma yana Daure a kugunsa Mujaheed na Dakin har Lokacin sai dai a lokacin yana zaune ne sabanin da ya barsa yana Tsaye ne.
Har Saifudden ya gama goge jiknsa ya shafa mai ya shirya Cikin Shigar kanana kaya,Mujaheed ya kallesa kafin yace"Ka sauya wannan shigar ka saka Kaftan."
Saifudden ya Dago a Fusace yana Fadin"Bazan sauya ba din.."
Mujaheed ya tabe baki bai kara mgana ba sai da suka fita falo Ummi na Zaune tana ganinsa da wannan shigar ta nuna mai hannu tana fadn"Juya ka sauya kaya..Manya kaya zaka saka mallam.."
Mujaheed ko baka Fadamai bane.?
Mujaheed yace"Na fadamai yace bazai Sauya ba din ba"
Ummi ta kallesa tana ballamai Harara Lokaci daya tana fadin"Au bazaka sauya ba..?
Saifudden Haushi ya kamasa sai kawai ya juya ya koma Ciki mintina goma sai gashi ya fito cikin shigar wata Danyar shadda Fara tana maiko Daga gani ta bama Hamsin baya Saboda yadda take sheke sai dai kansa ba Hula Ummi tace"Koma ka sako Hula ka rufe wannan uban gashin naka bazani gidan
mutane dakai ba kanka kamar shekar ungulu"
Me mujaheed zai yi in ba Dariya ba wani kallo Saifudden yayi mai yasa ya Dannen Dariyarsa ya Fice Haraban gidan yana Dariyansa Ganin ya Tsaya ne yasa Ummi tace"Au bazaka je ka sakan bane sai na make ka."
Dole ya juya yaje ya sauko Hular kalan aikin jikin kayansa sannan Ummi ta tasa shi suka fito takalmin kafarsa baki ne budadde sai agogon Hannunsa ma na Fata ne baki mai kyau,Excort dinsa sun taso ya dakatar dasu da Hannu suka koma suka kame Gaba ya shiga Ummi ta koma Baya suka Fice Daga gidan Junaidu na Faman Binsu da Allah ya kiyaye.
Ba wanda yayi mgana har suka fita Daga GRA din,sai da suka Dauki Hanyar Dogarawa sannan Saifudden ya juya yana kallon Mujaheed Lokaci Daya yana Fadin"ina zamu je..?
Mujaheed na Driving bai ko kallesa ba yace"Nima bansani ba Tambayi Ummi."
Ya juya yana kallon Ummi Data Hade rai yace a hankali"Ummi ina zamu je.?
Ummi ta ballamai harara kafin tace"Gidan masu saida mutane."
Yana jin haka ya kama bakinsa ya Tsuke bai kara mgana ba har suka iso kofar gidansu Muhibba da Sani da isma'il suka fara cin karo suna Tsaye a kofar gidan suna mgana agaban idon su Su Ummi suka firfoto daga cikin Mota Sani da Saifudden suka kalli juna kuma kowa ya shaida juna Saifudden ya kauda kai sai yanzu ya fara shan jinin jikinsa,kar dai ace gidan su yarinyar ce ta jiya Ummi ta kawosa daya shiga uku,me zai mata..?
Bai son ganinta,ganinta na sakashi Faduwar gaba da shiga wani yanayi.
Sani da Isma"il ne sukayi musu barka da zuwa Ummi tuni ta shige cioi Isma"il ne ya bama Saifudden Hannu suka gaisa Sani kuwa Tamke fuska yayi haka shima Saifudeen dayake jinsa kamar yana Takure ne.
Ba'a jima ba sai ga Ya Habibu ya leko da kansa domin Ummi na shiga suka Hadu da Ya Habibu shine ta sanar dashi ya fito ya shigo dasu Saifudeen kwarjin Ya Habibu ne ya Dakesa yasa ya basa Hannu suka gaisa shima Ya Habibun kallon Saifuddeen din yake yi Cikin Nazarinsa kafin ya kalli Mujaheed yana Fadin"Saifudeeen kenan ko..?
Mujaheed yace"Eh shine gwamnati ne da kanta ta ilimi.."
Dariya Ya Habibu yayi shi ko Saifudeen sai yayi kamar bai ji ba Sani Tuni ya shige cikin gida sanda ya Habibu yayi musu jagora zuwa Cikin gida yana Dakinsa domin har ga Allah yana jin Haushin Saifudeen in ya Tuna sanda ya ture muhibba.
Muhibba tunda Ummi ta shigo tace ga Saifuddeen zai shigo Jikin Muhibba ya fara rawa,Duk da suna Dakinta ne ammh Ba inda jikinta baya bari Lokacin da taji sallamansu sai da Cikinta ya karta Tuni Sadiya da Anty Habiba sun fice sun barta Anty Zeenatu kuma tana bangaranta tana girki saboda baki.
Bata san me ke gudana Dakin Inna ba taji dai tana ta Hira da Dariya Cikin Annushuwa Domin suna shiga Dakin Saifudden ya duka daga kofar Dakin kansa na kasa yana gaida su Inna Ummi ta kallesa tana Fadin"Dago kanka yaro.."
Ba musu ya dago yana kallon Ummi inna ta nuna mai tana fadin"Ga mahaifiyar Muhibba
nan da sabani ya hadaku jiya, gidansu
ne nan mahaifinsu ya rasu wannan yayanta ne ta nuna Habibu sannan ta nuna Habiba ta kara da Fadin ga yayarta nan sunanta Habiba kuma nan daka gani gidane..Sai da muka zo bada hakurin abunda ka aikata muka san haka..da Kawunka da mahaifin ita muhibba aminan juna ne in kana jin BelloMai Rago a bakin kawu to nan ne gidansa kuma duka nan iyalansa ne."
Saifudden ya jinjina kai aransa yace ya shiga Hannu kafin ya rankwafa yana kara gaida Inna,Ta amsa cikin sakewa Lokaci daya tana Fadin"Sannu
kai ne Saifudden.?
Ya amsa mata cikin Sanyinsa inna ta kara fadin"Kai ne kuma kwamishina ko..?
Kansa na kasa ya amsa mata su Ummi nata Dariya Inna tace"Kuma kai ne ALJANIN da ka razamin auta ko..?
Gabadaya sai aka kwashe da Dariya Saifudden da kansa ya Daure da mganar Inna ya Dago yana kallonta Sadiya ta yi dariya kafin tace"Inna kin Tsorata Hamma fa.."
Inna tace"To nima ai a tsoracen nake..Kai Habibu ku dubamin kafarsa badai kofato ko.?.
Sai aka kara kwashewa da Dariya Mujaheed na Dariya yace"Inna adubasa wlh kada yazo yana da kofato."
Sai D'akin ya Dauki Dariya Umma babba tace"Bana son Sharri..D'a na kafarsa ta mutane ce gata ce fara sol da ita hangota Innr
Habibu"
Tafada tana nuna kafar Saifudeen dake duke yana jinsu ya kasa Fahimtar mganar su ballatana yasan ina suka dosa yana ji Inna na Fadin"Eh to na amince yanzu wannan Saifudden ne ba Aljani saifudden din Auta ba."
Nan ma dariya aka saka gabadaya Ummi ta kalli Sadiya tana Fadin"Ina D'iyata.?