← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 144

Sashe 114

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ni ko Sai bayan La"asar na Farka har kuma Dare Hajiya ke kula dani su Ummi suka sauko falon kasa suna ta Hira da Hajiya sai ga kyakyawan Mahaddatan jikokin ya'n biyun Hajiya sun yi sallama sun shigo Dukkansu Jallabiya mai ruwan kasa ne ajikinsu har da Rawani da Harami kowanne da Qur"ani a Hannunsa Aban yara ne yake Dauke da wasu Littafai wlh yara ne Yan kimanin shekaru sha Shidda ammh Kwarjininsu da Haibar Addini sai da ya Daki su Ummi akaron farko da suka fara ganinsu.
*Janafty*
*SFD0041*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
A gaban Hajiya suka Durkusa dukkansu,sai da suka fara gaida su Ummi suka amsa musu cikin Fara"a da Sha'awa jin yadda Harshen su ya karye Hausan ma bata gama kama bakinsu gabadaya ba.

Daganan suka maida kallon su kan Hajiya Magajin mallam ne yace"Hajiya Kaifa Antum..?

Hajiya tace"Alhamdulillah..ya makaranta da Himma?

Suka amsa atare da sai Hamdala Cike da Sha"awa da kaunar jikokin nata tace"Ina kuka baro Babanin naku Jafaru da Nasiru..?

Wannan karon ma Magajin mallam ne yayi mgana shi Aban yara kamar Mahaifinsa yake bai kai magajin mallam mgana da Hayaniya ba.

Ce mata yayi suna Falon Baba mallam Tare da baki cikin gamsuwa Hajiya tace"Masha Allah.."
Sai alokacin Aban yara yayi mgana Lokaci daya yana fadin"Uncle Nazir bai zo ba ne Matas..?

Hajiya tace"Ya kirani a waya yace sai wani Sati zasu shigo Hidiya bata ji Dadi ba"
Fatan samun sauki suka mata Harda su Ummi a masu amsawa da Ameen kallon yaran kawai suke cikin Burgewa Anty Habiba naji aranta Dama Khalil da Walid ne Ni kuma ina Bayan Hajiya na Lafe sai dai ina ta leken yaran ina komawa suma suna kallona cike da mamaki.

Ganin Haka ne yasa Hajiya tayi m
usu bayani da kai suka amsa mata Aban yara ne yace"Allah ya bata da Lafiya"
Suka amsa da Ameen Ameen gabadayan su hatta Muryansu iri Daya ne komai nasu iri Daya mamaki da al'ajabi ya ishi Adda Sadiya har sai da tace"Hajiya naga komai nasu iri daya ta ina kuke iya bambam ce su..?

Hajiya tayi Dariya tana kallon su sukuma suna jin Haka suka sunne kansu suna Mirmishi.

Hajiya Babba ta gyara zama tana Fadin"Shakiyan yara ne..Iyayen su kadai ke iya bambamce su in kika ce Aban yara sai mgajin mallam ya amsa in kika ce Magajim mallam sai Aban yara ya amsa su yi ta rikita Mutane shiyasa ba na Damuwa da bambamce su Duka daya na Dauke su a wajena"
Ummi tace"Ba shakka ni kaina Tun dazu nake kallon su ammh na kasa bambamce su."
Sai alokacin Anty Habiba tace"Za"a iya bambamce su ta Hallayarsu..ko ni na Fahimci Daya yafi daya sakin jiki..Da Mgana"
Hajiya tace"Allah ya yi miki albarka nima ta haka nake gano ja"iran..Ko Maamah ma tace ta haka ta lakance su..Aban yara bai da Hayaniya da yawan mgana irin babansa ne shi kuma Magajin mallam kina kallonsa zaki san komai na uwarsa ya Debo kadan"
Tura baki Magajin mallam yayi kafin yace"Nima fa da Abbu nake yanayi Hajiya"
Dariya suka saka gabadayan su Hajiya tace"Kun bayyana kan ku yanzu mun gano ku"
Jin haka yasa suka mike atare suna Fadin"Wlh baki gano mu ba"
Sai suka kara kallon juna kafin Aban yara yayi gyaran murya yace"Matas ni ne nayi mgana dazu kuma ni Sunana Sa'id Umar Yunus bazanga.

Shima Magajin mallam yace"Ni kuma sunana Yunus Umar Yunus bazanga"
Sai Hajiya ta rike baki tana Fadin"Ja"iran yara"
Dariya suka fara mata su Ummi na taya su kwafa Hajiya tayi kafin tace"Ai iyayan naku na tafe karshen wata zasu raba ni da shakiyan cin ku."
Da Sauri suka Hada baki wajen Fadin"Hajiya har da su Banu..?

Hajiya tace"Har da su Tani ma duka gabadayan su ne nan zasu yi azumi sai bayan sallah zasu koma"
Murna suka kama yi Domin akwai shakuwa mai girma Tsakanin su da yan"uwan su da kauna mai inganci tsakanin su da iyayansu Haka suka Fice suna mgana da Junan su ammh Cikin Harshen larabci su ummi sun saki baki cike da Shauki da Burgewa.

Sai bayan fitan su ne Ummi tace"Kannen nasu gabadaya suna chan Madinan kenan..?

Hajiya tace"Eh ita Amina mahma kenan haihuwarta Shidda ne..Daga yan biyun nan sai takwarata Iman sai tazo tayi Mai sunan ta Amina sun yi ma wata tsohuwa yar Maiduguri Yakaka takwara wacce ta zauna wajen Aminar achan Saudiya har Allah yayi mata rasuwa,sai tazo ta yi Abdurrahaman suna kiran sa Sudes sai tazo tayi Aliyu sai karamar mai suna Hannatu ammh tace min tana rokon Allah ya kara bata wani Cikin ta Haifi Hamida"
Su Ummi suka jinjina kai suna fadin"Daga gani suna kaunar junansu"
Hajiya tace"Bama a mgana tare suka taso tun suna yara..Sun shaku da juna Fiye da yan"uwan su na ciki Daya..Daga Hamidan har Hanne ba wacce bata Haifi Amina ba,su kan su sun Haiyayyafa Hamida ya"yanta Bakwai ita tana Haihuwa akai akai Gwara Hanne tanakan jima bata Haihu ba,Ita Amina da ya ke tana da abokan zama uwargidan dai ta samu matsala bata Haihuwa Amaryan Saratu ya"yanta Hudu duka mata sai ta Dauki Banu babbar ta danka ma Sakina Saboda karramawa tunda ita bata taba Haihuwa ba."
Ummi tace"aiko ta kyauta Allah ya bada Lada ya zaunar dasu lafiya zan so matuka naga wannan kyakyawan zuru"ar naku Hajiya"
Hajiya na Dariya tace"Haba ai an zama Daya zumunci kuma ai Diyata Muhibba ta Hadamu har Abada..Duka ya"yan namu da jikokin nan zasu yi Sallah,Duk wadanda ke aure wasu garuruwan irin su Joda da ke kasar ketare duk zasu zo sallar azumi Daman in ba wani babban Sha'ani ba sai da Sallar ake haduwa gabadaya ayi Zumunci tun ballatana ma da kowa yaji Danmallam da iyalansa wannan shekaran suma suna nan"
Ummi ta jinjina kai kafin tace"Hakane to Allah ya kawo su lafiya..Allah ya kara shirya zuru"a."
Nan ma suka yi ta Hira Nidai har nayi barci ajikin Hajiya har sai da su ya Jafar suka shigo gaida su Ummi suma yaran su basa gida sai kanana mata Mazan shi da Nasiru duk makarantar kwana suka kai su.

Har su Adda Sadiya sun ji Dadin Hira da Hajiya haka kurum Dattijuwan ta kwanta musu arai dukkan su a sama ta Sauke su Dakuna ne sai iya kirgan ka Ummi tace"Dole gida cike da ya"ya da Jikoki."
Dakin Hajiya na kasa na kwana ita da Baba mallam basa hawa bene sai ta kama Saboda Kafa da asuba ita ta tadani mukayi salla tare sai jana da Hira take yi sama sama nake amsa mata Rabi Duk shirme ne ta kalleni ta Dafa kaina tana Fadin"in sha Allahu zaki samu Lafiya Muhibba har ki Dawo da Lafiyarki"
Ni dai sai dariya nake yi mata matar nan tasan mutumci bata taba ganina ba ammh tamin abunda ko Inna albarka ta taimakamin nayi wanka ta bani abun karyawa tamun tofin addu"a da ruwan zamzan ta bani nasha bayan ta shafe min Fuska da kaina dashi ko da su Ummi suka Fito nima na shirya Cikin wata Doguwar Riga da Hajiya ta sake bani Ummi sai Fadi take yi"Hajiya Har da wata Dawaniya kuma..?

Hajiya tace"Haba Zaliha an zama Daya Dukkan ku ya"ya na Dauke ku ko bakwa uwar da ni ne..?

Da Sauri suka ce"Haba Hajiya ai kowani D'a zai yi alfahari dake a matsayin uwa ta gari"
Haka dai suka yi Hira har sai da Kawu ya Kira Ummi yace mu fito Sannan muka fito Hajiya na rike da Hannuna Hatta Farin Hijabin dake jikina Hajiya ta bani shi Sabo Dal ko saka shi ba'a taba yi ba.

Har Falon Baba mallam ina makale da Hajiya kamar ma ina jin Tsoron Mutane bayan su Ummi sun gaishe da Mallam suka juya suna gaida su kawu da Tun jiya basu kara Haduwa ba,Sai yau,yan biyun Hajiya suna Hadda sun dai shigo da Safe sun gaishe da Hajiya kafin su wuce.

Banga Saifudden ba yana waje yana waya kowa ya kira sunana bana kallonsa ammh mallan na kira na sai gashi na isa gabansa na Durkusa ina Fadin"Ina yini..?

Baba mallam yayi Dariya yana Fadin"ina kwana ko Diyata..?

Ko Jikata dai zan ce?

Kawu na Dariya yace"Sai dai jikar Mallam mu ne ai ya"yan naka"
Hajiya na Dariya tace"Gaskiya kam..!

Baba Sa"idu yace"Ai mu ya"ya mun cike Gurbi Baba sai dai ajokokin..!

Gabadaya Dariya ake yi kamar an Dade da sanin juna kaina ya Dafa yana karantamin Addu'o'in Tsari kafin ya Tofa ya Shafemin kaina Lokaci daya yana fadin"In sha Allahu Zaki sami Lafiya..Ina nan ina jiran Tattaba kunnina In har muna da Rabon gani."
Gabadaya aka amsa da Allah yasa nan Baba mallam yace"mun yi mgana da Surajo..Ba matsala a baya naso Hajiya tayi muku Rakiya sai Sa'idu ya nuna gwara shi yaje saboda ba kowa agidan Nasara taje gidan su Biki yana Tunanin Kada Hajiya tatafi bani da mai kula Dani"
Gabadaya akayi Dariya Baba Sa"idu yace"Ko ka ga Laifina Baba..?

Hajiya tace"akan mallan ne ai bazan yi mamaki ba"
Baba mallam yace"Rabu da Zainabu Abu kasan tana jin wani iri tunda na kwace mata gwamnatin ta"
Hajiya tace"Nima ai na samu wasu ya"yan gasu nan ku je chan ku karata"
Gabadaya falon aka saka daariyan Diramar Hajiya da Mallam.
Chapter 114 · 0% Book details