← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 144

Sashe 35

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Muhibba tace"Gidan Anty Habiba zani kasan muna da taro a makarantarmu ranar asabar kuma aikin yin su cake Director din mu Ni ya bama ragamar yin aikin Gidan Anty Habiba zani mu fara aikin Tunda yana da yawa.

Sani yace"Taron me..?

Muhibba tace"Speech and Prize givingday da kuma Anniversary na shekaru shidda na kafuwar makarantar"
Ta fada Lokaci daya ta na Daukoma Sani Invitation din dake cikin Jakarta ta bashi tana fadin"Muna gayyatarka..

Ya karba ya karanta duka kafin ya tabe kafin yace"Baki fadamin da wuri ba.."
Muhibba tace"Kai ka sani kayi ma kanka..Domin mayan bbys zasu zo fa".

Sani yace"Da gaske..?

Ya fada yana satan kallon Inna da Hankalinta ke kan abunda take yi,Muhibba tace"Zan maka karya ne..?

Sani yace"Shikenan zan zo..Zasu ga babban yaro..

Barrister Muhammad Sani bello Mairago."
Muhibba tayi dariya tana fadin"Ina gayen..?inda ba gayu dai ko.?

Sani ya mike yana juya wa fadi yake yi"Karyan ki yarinya ke kanki kin san ni Hadadde ne sannan mai kyau ne kaf cikin Samarinki kin taba samun kamata..?

Muhibba tace"Ina fa.."
Sani yace"Af..Na ganeki hassadace to Sai dai ki mutu ni Sani duk kushen mai kushe bazai taba kusheni ba zan zo na watsa muku swags kunsan namu ba irin naku bane.."
Muhibba tace"Zan so kazo wlh.

Yace"Zan zo insha Allahu..

Daga haka suka bar mganar,Inna tayi ma sallama Sani yan mutumci na kusa ya Daukan mata jaka suka fita Bakin Titi,Ta samu adaidaita da tace ya rakata yace sai jibi zai zo su Sani manya shi ya biya mata kudin Napep din ya kalleta yana fadin"Bakomai mu masu arziki haka muke harkanmu.

Har Suka fara Tafiya tana Dariyan Sani yanzu haka 200 din ita kadai garesa Sani bazai daina cika baki da Fafa ba.

Ranar kasuwa suka shiga ita da Anty Habiba suka yi siyayya,Washegari Alhamis,bayan ta dawo makaranta suka fara aiki da Cake suka fara basu gama ba,sai Dare sallah kadai ke tadasu Ranar har shabiyun dare kafin su kwanta sun kwaba na Donot har sun fara Allah yasa su khalipa na tayasu da Zenan Donot din ai da wahalan tafi haka washegari kuma Jumma"a Muhibba taje makaranta sai dai bata jima ba D.Musa ya bata izini dawowa saboda aikin daya bata,Bata dawo ba sai ta biya sabon gari ta siyi wasu fararan robobi na zamani,da za'a saka abubuwan aciki sai ayi raping da foul paper,Sannan Uncel Hafiz ya fadama ta anyi pepe meat,Matar D.Musa tayi shima za'ayi Raping dinsu ne sai a ranar zai zo dashi.

Ranar ne Asma"u kanwar Baban Walid tazo ta taimaka musu sai dare suka gama Meatpie din Sani yazo sai wajen goma ya tafi sai da ya ci sannan yaso yayi guzuri Anty Habiba ta hana tace abun Amana ne Shiyasa ya hakura ammh yace ya zama Dole yaje Tunda yaga abun na manya ne.

Ranar Asabar da Safe tun karfe Takwas Muhibba ta tafi Makaranta Dauke da kayan da sukayi napep guda ta Dauka Cikin Office din Director aka shiga da komai inda taga katan katan na lemuka da ruwa ba iyaka,kowa sai jinjina mata yake yana fadin sun yi kokari tunda malaman sun Dauka sun cicci kuma sun yaba da dadin Snaks din matuka.

Tuni ma"aikata sun zo sun gyara Hall din daman akwai kujeru aciki,Mc ne da Dj ne suka zo suka jera komai da inda za"a hau kan step da wajen mgana sai daga chan gefe kujerun malamai da ta iyayan yara sai kuma Daga barayin Dama kujeran mai girma shugaban taro wato shugaban makaranta kenan tsarin dai ya Tsaru sai wanda ya gani Daliban da zasu yi Debete da sauransu duk da wuri suka zo kowanne Uniform ya wanku ya sha guga abun gwanin ban sha"awa makaranta tayi kal ba wani Hayaniya.

Su Anty Khadija duk sun zo suma da wuri saboda shirye shirye,ko kafin karfe goma komai ya kamallah har Baki sun fara zuwa iyayan yara da kuma Sauran Dalibai yan makaranta kowanne sanye da Uniform.

Daman Tsarin makaranta ne kowa Uniform dinsa zai saka kuma Taron sai karfe sha daya za"a fara..goma da wani abu su Anty Habiba suka zo ita da Abban walid da Asma"u da Walid da siyama,Lokacin mun koma gidan Anty Jidda da ita domin mj Shirya sai mu dawo ko da muka dawo Motoci sun cika Haraban makaranta sannan Hall ya cika ba matsaka Tsinke kaf iyalan D.Musa da ya"yansa sun Hallata shima yaransa biyu suna makarantar shashen Jss.

Muhibba Atamfa ta saka Doguwar riga mai ja ajikinta sai ta saka mayafinta dan Dubai ja akai ta Daura,mayafin sannan kafarta Cikin Takalmi ja mai Saukakkan Tudu chan kusa da Abban walid ta hango Sani na Daga mata hannu alamun jinjina ta washe baki dadi ya kamata itama ta Dagamai hannu Fararan hakoranta duk suna waje ne suma su Anty Habiba Daga musu Hannu tayi domin ta Hango su, Su Uncle Hafiz ke ijiye ma kowa abun da zai taba agabansa bangaran Iyayan yara kenan Robar snaks sai robar nama da ruwa da lemu su Muhibba kuma suna chansuna shirya wadanda zasu fara Quiz tunda shine na Farko ammh har aka fara gudanar da Quiz
din Babban bako bai iso ba D.Musa duk ya Damu sai faman duba agogo yake yi yana kuma faman kara waya a kunne.

An gama Quiz SS section suka cinye yan Jsss,sai aka fara Games,kamar na gudun kwai dayake saman step din akwai Fili,gudun buhu da sauransu an gama shi kenan an fara Debete Wani Matashi kyakyawa da Matarsa Fara mai kyau da yarsu suka shigo Halla da Hanzari D.Musa da Uncle James suka tarosu abun mamaki har zuwa Higher table na babban bako suka Zauna sai faman mirmishi suke yi Daga gani abun ya bala"in kayatar dasu.

Adda Sadiya dake ta kallon Debete din yara farinciki ya kamata ta tabo mujaheed tana Fadin"Sweety Naso hamma na wajen nab..Domin yaga aikin sa gaskiya Students din makarantarsa They Very perfect and Brilliant."
Mujaheed shima na bama idonsa abinci yace"Ai SAIFUDEEN ACADAMY ba daganan ba Sosai malaman su suke da Jajircewa kinsan yayan naki wajen Boko ba wasa ki duba aiko malaman They are perfect kuma kallesu d'aya bayan d'aya sun san abunda suke yi Saifudeen ai bazai yi aiki da wanda bai da kwarewa ba kuma Musa gaakiya mai Amana ne jajirttace ne da Taimakonsa makarantar ta samu wannan Cigaban"
Adda Sadiya tace"Haba Hamma mana why are u..?

Mujaheed yace"Zai zo ai Ummi ta kirasa tamai mgana da ita na Hada shi domin nasan ita kadai ce ne zata tankwarasa muna hanya kafin mu shigo ya fadamin zai shigo kafin a tashi."
Da haka sukayi shuru suka cigaba da kallon abunda ke gudana an gama Debete din ihu da tafi ya karade Hall din su Khalipa suka cinye Debete din sosai yaron ya Burge kowa Hatta Sadiya da Mujaheed kuwa,Sadiya sai da taso har kan Step ta rike Hannun Khalipa tana Tambayansa sunansa yace mata"muhammad khalipa bamalli."
Kansa ta shafa ta Dauko 5k sabbi yan dubu dubi ta basa tana Shafa kansa sai Hall ya Dauki Ihu Uncle James ne ya karbi abun mgana bayan Add Sadiya ta koma wajen zamanta ya gabatar da Mr and Mrs Muhajeed Abdulsalam Dala,aboki kuma Amini dan"uwa ga mai wannan makarantar Sannan ita matar Mrs Sadiya Salahudeen lere kanwa take shakikiya ga mai wannan makarantar sai kallo ya koma kansu kowa sai jinjina kai yake saboda Hango kyau ilimi da Nasaba da kudi da jin Dadi a wajensu aran Muhibba tana Fadin tab shi mai makaranta ya za"a gansa kenan Billions kenan.

Daga Debete sai aka Fara Drama ita kan an sha Dariya matuka Drama din ta Kayatar an yi na Turanci an yi na Hausa,yaran sun yi matukar kokari suka gama ana tafi da sowa da kuma Jinjina,Lokacin har 12 ta wuce shugaban makaranta bai iso ba kuma ana Fatan shi zai mika kyattuka ga Dalibai sannan da malam da za"a karrama ganin bai iso ba sai mujaheed ya wakilcesa aka fara kiran yan SS 3 yayi musu jinjina sannan aka kira sunaayen prefect d'aya bayan d'aya yana mika musu kyattukansu sannan aka fara kiran yan Jss3 masu kokarin ajin aka basu kyauta sai primary section suma an bama prefect kyuta sai kuma masu himma cikin Dalibai an kuma kira wad'anda sukaci Quiz an basu sannan an karrama sauran suma anbama masu debet Khalipa ya samu kyauta ta musamman ta hazikin Dalibi Muhibba da su Anty Habiba baki yaki Rufuwa har Walid ya samu kyautar best subject a mathematics.

Gabadaya su suka mika kyattuka ga yara sannan sai akazo kan malamai sai aka kira Sadiya a matsayin wacce zata mika tambarin girmamawa ga Hazikan malamai.

D.Musa aka fara kira aka karramasa a matsayinaa na Shugaban makaranta mai adalci,sai Uncle james sai primary section Aka kira Head teacher itama aka karramata Daga ita sai Umcle Hafiz aka fara kira ai ko yaci karramawa Domin yana da kokarin taimakama Dalibai ya fito ya karbi kyautarsa ba Tsammani Muhibba taji an kira Primary 4 Teacher Muhibba Bello mai Rago,Sai tafi ya tashi kunya ta kama Muhibba sani sai dago mata Hannu yake yana washe mata baki ta mike tana Hardewa ta isa ga step haka kurum taji gabanta ya fadi da suka Hada ido da Sadiya hannu ta bata suka yi musabaha sannan ta bata Aword din ta karba aka fara Daukansu Hotuna daman akwai masu Hoto har yan jarida sun zo wajen D.Musa ya gayyacesu.

Da zata tafi sai da suka kara kallon juna ita da Sadiya suka ma juna mirmshi sannan taje ta zauna su Khadija da Usaina kamar zasu yi bindiga Saboda bakinciki,Suna gani Uncle Hafiz ya daga mata babban yatsansa yana Fadin"Congratulation.

Ta amsa cikin mirmishinta daman tana kusa da Anty Jidda ne an cigaba da Kira sauran malaman an karrama su har da Anty Jidda a matsayin Best Teacher a section din su kamar yadda itama Muhibba ta karba,Bayan Anty Jidda ta dawo daga karbo nata ne Muhibba taji maranta ta Daure sai taji kamar abu na zubar mata ta karkata tayi ma Anty Jidda Rada da Fadin"Anty ina ga kamar period dina ya shammaceni zai kunyatani cikin jama"a."
Anty Jidda ta zaro ido tana fadin"Subhanallah kuma baki zo da shiri ba..?
Chapter 35 · 0% Book details