← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 144

Sashe 76

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Goggo Atka ta tabe baki kafin tace"Sai kin Dawo in dai Zaliha ce gaki ga ta..!ita dai muhibba ganin bawani Sakin Fuska yasa bata wani Dade ba suka mata sallama ko ta rakasu ballatana ta kaita Dakunan mutan gidan suka fice,suna tafe zasu koma Majeeda sai bama Muhibba Labarin goggo Atika take yi daganan ta san matar masifaffiyace
Suna zuwa kofar gida suka iske Motar Saifudden sannan ba mutanen kila har ya sallame su sai dai su bama da suke Tsaye kame suna ganinta suka ramkwafa suna gaisheta da Harshen Turanci ta amsa musu cikin Sakewa
Iya na jin Sallarmaasu tace"Ga su nan ma sun dawo"
Sai da suka shigo Falon Sannan Iya ta kalle su tana Fadin"Ku kuma Daga shiga cikin gida sai a neme ku a rasa..Tun dazu megidan ki yazo zaku wuce na aika cikin gida akace kun fita."
Majeeda ce ta tsaya bayanin inda suka je ita kuma Muhibba Saifudden ta kalla Dake tsuke cikin Suit Fari da baki ta gaishe shi ya amsa kai Tsaye yana fadin"Ki shirya yan zamu wuce."
Da toh ta amsa mai kafin ta shiga ciki,domin ta shirya kayanta aranta tana jin Takaicin shi da bai Fadamata har Wajen Ummi zasu ba.

Majeeda ma jin haka yasa ta kwashi Gudu zuwa shashen su tana fita Iya tace"Kaga Muhirba tayi Hankali ni na manta da zuwa gaida Atikar.

Yana jinta bai ce komai ba gajiya yayi da jiransu ya mike bayan ya ijiye mata,kudi yana Fadin"Iya zamu tafi sai wani Lokacin..Kudin nan naki ne na bama su baffa nasu."
Iya sai ta fara matsan kwallah tana ta saka albarka shi dai ya fice ya barta yana Fadin"su same ni a mota...bana son jira!

Tana ciki tana jinsa ta bata rai a ranta tace"Uzurarre!

Daman ta gama Hada kayanta ta fito ta Duka tana ma Iya sallama ta Dafa kanta tana ta saka albarka Daman ta tashi da Safe kafin tayi wanka ta gyarama iya Dakinta ta share duk da Iya na ta bari ta bari bata bari ba din
Kusan duka gidan suka rako su bakin Mota Majeeda da kullin kayanta Bakinta har kunne saboda murna,Shi dai yana cikin mota Saboda sanin Halinsa yasa Muhibba tace Majeeda ta fara shiga motar tana shigowa ya Dago yana ganinta da Sauri yace"Ke koma..ita ta fara shigowa."
Ya fada da Sauri ai gwara ita ta zauna kusa daahi ina zai iya zama kusa da kazamar yarinyar nan.

Majeeda ta koma da baya tana Fadin"yace ki fara shiga..!

Haje na gefe tace"Ke ya kamata ki Fara shiga Amarya."
Kamar bazata shiga ba hakanan dai ta shiga ta zauna sai dai bata Gogu dashi ba sannan majeeda ta shigo Bama ya Rufe kofar ya koma gidan gaba ya kame Tim ya tada motar suka fara Tafiya suna Daga musu hannu Talatuwa har da kwallarta na kewa, Majeeda suna ta,kuka har suka Fita Daga Layin majeeda na daga musu hannu sai hawaye da kuka Muhibba ta jawota jikinta tana Lallashinta yana gefe yana kallonsu ta gefen ido yana mamakin yadda ta iya saka Majeeda ajikinta baki ya tabe kawai ya kauda kansa Tun yana Dari dari har sai da ya Saki jikinsa ganin bai ji wani yanayi ba,Yana jin majeeda ta zage suna ta Hira da Muhibba sun Dame sa yasa yayi gyaran murya kafin ma yace wani abu Majeeda ta kama bakinta itama Muhibban sai tayi shuru abunta da suka fara Nisa barci Majeeda tayi ita kuma Muhibba daman bata barcin mota Har suka isa Abuja tana kalle kallen Hanya bata taba zuwa Abuja sai yau ko da suka isa haraban gidam Ummi uku saura na Rana suna jin dirin motarsu har da Ummi a masu tarban su Saifudden ya fito Daga mota yana fadin"Ummi baki taba zuwa tarbata ba ssi yau..!"
Ummi ta wucesa tana Fadin"Ai yau din ba naka bane na Di'yata ne"
Baki ya saki Da yaga Ummi ta wucesa taje ta Rumgume Muhibba su kuma su Laala Majeeda suka rike suna murna.

Ummi fadi take"Maraba da zuwa Diyata..!

Muhibba cikin jin Nauyi ta amsa Ummi tana gaisheta Ummi ta amaa cikin Fara"a kafin su Laala ma su gai she da Muhibba ta amsa tana tambayansu makaranta sukace Lafiya lau.

Majeeda ma ta gaida Ummi ta amsa tana Fadin"Majeeda Yan mata.

Rufe fuska tayi tana Dariya su Laala na Tayata sai alokacin ummi ta waiga bata ga Saifudden ba cikin mamaki tace"Ina yaro..?

Laala na Danne Dariyan ta tace"Ummi ya shige fa tun dazu."
Ummi ta tabe baki batayi mgana taja Hannun Muhibba suka wuce cikin gida.

Afalo suka zauna ana kara gaisawa Daidai Lokacin da su Bama suka shigo da akwatin Muhibba da Roban Dambun naman da suka gani ya sauke ya fice Ummi ta kalli Laala tana Fadin"Dauki kayan majeeda kuje Dakin ku tayi wanka tayi sallah sannan ku zo mu ci abinci"
.da Toh ta amsa mata kafin taja Majeeda zuwa Dakin su bayan Ummi ta mata mgana Muhibba kuma Ummi sai ta Umarci Zeeha ta Dauki kayan Muhibba ta rakata Dakin Saifudden.

Da sauri ta mike ta Dauka zata Dauki Roban Dambun Nama Muhibba tace"Ban da wannan Naku ne..Ummi kuyi hakuri bai gayamin zamu zo har nan fa."
Ummi tace"Bakomai Diyata mun gode kuje ki samu kiyi wanka ki yi sallah
Kafa kafa Zeeha na gaba tana baya Sai da suka fara knoking,sannan ya basu izinin shiga tana gaba tana binta a baya yana Tsaye gaban madubi yana Sharce gashin kansa bai ko juyowa ba yace"Waye..?

Zeeha jikinta na rawa tace"Dama..Dama Ummi ce ta ce na Rako Anty Muhibba Dakin ka da kayanta....."
da sauri ya juyo yana kallonsu Sai muhibba taji jikinta yayi sanyi cikin mamaki yace"Ummi tace ki Rako ta Dakin nan..?

Zeeha ta Daga kanta alamun eh bai Tsaya ba ya raba su ya fice Daga Dakin Zeeha ta sauke numfashi tana Sauke akwatin hannunta tana Fadin"Anty muhibba sai kin fito
Yake kawai muhibba ta mata har ta fice ta rufo mata kofar sannan ta Sauke numfashi tana bin Dakin da kallo shi komai nasa baki ne ammh Zanin gadon fari ne da blanket din dakin sai tashin kamshi yake yi ita kam ba wanka zatayi ba sai ta Fada Tiolet din ta Dauro alwala shima Tiolet din Komai Fari ne gwanin sha'awa.

Saifudden ko yana fita falo yaga Ummi zaune tana Bude Dambun Naman da Muhibba ta kawo musu sai ta gan sa a kanta cikin mamaki tace"Kai kuma lafiyarka kazo ka Tsayamin bisa kaina..?

Saifudden ya zauna gefenta yana Fadin"Ummi naga kin Turata Dakina."
Ummu bata kallesa ba tace"Eh to da ina zan tura ta..?

Kai Tsaye yace"Ummi baga Dakin su Laala ba sai ta sauka chan."
Ummi ta tsaya cak tana Hararansa Kafim ta mike dauke da Dambun namanta tana Fadin"Ka raina ni ko yaro..?Wlh zam maka rashin mutumci matarka ce in bata Sauka Dakin ka ba, Dakina zan sauketa..!?

Kansa ma kasa ya kasa mga Tsaki taja ta shige kitchen tana Fadin"Mutumin banza kawai..!

Tana jinsa yace"Ummi daga mgana..Allah ya baki hakuri naga alaman kin daina sona."
Daga kitchen yaji tace"sai yau ka sani kenan..!

Mirmishi yayi bai kara mgana ba Sanin Halinta ammh yana Fargaban Abunda zai faru yau bai taba kwana da mace daya adaki Daya ba.

Bai koma Dakin ba har Ummi tace su fito su ci abinci nan kasan Cafet suka zauna Laala taje ta kira Muhibba ta fito Sanye da Hijabinta Majeeda ma ta sake wanka sai dai wasu mattatun Kaya ta saka duk a Hargitse Ummi ta kalleta kafin ta kalli su Laala tana Fadin"Meyasa ku ka barta ta saka wannan kayan..?baku bata cikin naku ba.?

Suka yi shuru basu ce komai ba Ummi tace"Majeeda ki bani kayan da kika zo dashi..Su Laala zasu baki nasu ki fara amfani dashi kafin an dinka miki naki"
Ta amsa cikin Farimciki Saifudden na kusa da Ummi Muhibba kuma na gefenta suka sakata a Tsakiya haka suka gama cin abimci Bayan sun gama Ummi tana ta bari bari Muhibba bata zauna ba ta taya su Laala kwashe komai zuwa kitchen bata fito ba sai da ta taya su suka wanke duka kwanukan suka gyara Kitchen da suka fito ganin Ummi suna Hira da Saifudden sai ta bi su Laala zuwa Dakin su suka Tsinke da Hira suna bata Labarin Hamma Saif tana Dariya da Labarin ranar da sukayi gulmarsa ya kamasu Muhibba ta sha Dariya matuka.
Chapter 76 · 0% Book details