Sashe 81
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sadiya na zama gefen ta tace"Haba mana me ye haka..?kada ki manta kune Ministry of Educaton fa gabadaya yau ko daina zuwa kikayi bamai cewa don me kuma duk wata Dole arika baki alawunki ko Board of bata isa tayi mgana ba"
Ta karishe Fada tana Dariya itama Muhibba dariyan tayi batace komai ba Ruwa kadai ta sha Adda tace ta Hado musu breakfast..?
Muhibba tace"Am ok wlh Ummi Sai ta cika min cikina muka baro su.
Sadiya tace"Nima yanzu na gama Sallamar ya mujaheed ya tafi office nayi ma Nihad wanka tayi barci ina gyara Dakinsa ne kafin nayi wanka.
Muhibba tace"je kici gaba da aikin ki ai ina nan."
Adda ta mike tana Fadin"Ok bari na Dawo to"nan ta barta afalo bayan ta Dauki kayanta ta shigar mata dashi nata Dakin bayan fitan Adda Sadiya ta Dauko wayarta ajaka da Niyar kiran Ummi sai taci karo da Sakon da ya sakata Dariya bata shirya ba.
"Ki bude min Daki na malama."
Haka kawai ya Rubuta kenan Dazu da Safe kenan ya Turo mata kafin yayi Knooking bata ma yi Saving din Lambarsa ba sai alokaci ta rasa me zata saka mai kawai sai taa yanke shawaran sakmai sunansa na yanka ta Saka SAIFF kawai sai hannunta ya zarce tayi Saving dinsa a haka kamar zata sauya sai kuma ta barshi haka dinsa,Ummi ta kira suka gaisa ta Fada mata sun sauka Lafiya tana ma gidan Adda Sadiya Ummi tace"Masha Allah ki gaisheta Allah ya huta gajiya.
Daganan suka yi sallama Inna ta kira suka gaisa Tace mata sun dawo suna Kaduna ita tana gidan Sadiya Inna tace ta gaiaheta Daganan ta kira Anty Habiba suka Dade suna mgana tace mata Tana asibiti ne tazo awo Cikinta ya fara Girma Muhibba sai cewa take yi "Zamu sha suna."
Anty Habiba ta kwabe ta da Fadin"Waya sani ko ina haihuwar kema zaki Sauke naki..?
Tana jin haka bakinta sai ya mutu ta kasa mgana har sukayi sallama Sani ta kira wayarsa a kashe jiya sun yi mgana da Ya Habibu datace bata samun Sani a waya yace mata karatu ne yayi zafi kamar suna jarabawa ne shiyasa.
Gajiya tayi da wayar ta Maidata jaka ta kishingida har ta fara barci taji mganar Adda a saman kanta sannan ta Farka tayi wanka ta saka Riga da wando plazo gefenta ta zauna da Faratin kayam karyawanta tana Fadin"My sister ko zaki shiga ciki ki kwanta ne kafin anjuma..?
Muhibba tace"Ima jin barci da gaske fa.sadiya ta nuna mata Dakin ta tana Fadin"Ki shiga ki huta kafin anjuma.
Ba musu ta mike ta shige bedroom din Adda sai da ta kusa zama yar Kauye ganin Tsaruwarsa kan gadon ta hau ta kwanta sai barci Saboda Gajiyan tafiya,Sai wajen sha biyu saura ta farka shima wayar Anty Jidda ce ta tasheta ko da ta tashi wayar ta Tsinke sai ta kiranta Daga baya bata Dauka ba.
Tana zaune saman gadon sai ga Adda ta shigo ganinta zaune yasa ta kariso tana Fadin"Har kin tashi..?ai baki Dade ma kina barcin ba..?
Muhibba tayi mika kafin tace"Naji ai na warware gajiyar"
Sadiya ta zauna gefenta tana Fadin"Ai in kayi tafiya duk sai kaji bayan ka ya kage kaji gajiyan duniya ta saukar maka.
Muhibba tace"Balle ni da bana son Doguwar tafiya."
Nan hira ta tsinke tsakaninsu kukan Nihad ne ya fitar dasu Falo ta tashi Adda ta bata Nono Muhibba ta Dauketa ta goya sai ta koma barci mai mata aikace aikace tazo tana Kitchen tana wanke wanke su kuma suna Falo saman kujeru suna Hira.
Sadiya ta rasa yadda zata shigo da mganar dake bakinta sai Dubara ta zo mata ta kalli Muhibba tana Fadin"Yauwa My Sister gwara da Allah ya kawo min ke kin min Laifi Kafata har zaria naso na taka naji Dalilin ki na aikata abunda kika aikatamin"
Sai Muhibba ta Rude Cikin In ina take fadin"me kuma nayi ni Muhin Inna..?
Sadiya ta gimtse Dariyar ta tana Fadin"Laifi kika yi min babba ma kuwa..?
Muhibba kamar zatayi kuka tace"Ni wlh ban san Laifin da nayi ba."
Sadiya tace"Amanar da ma baki ne naga baki kula da ita ba."
Muhibba tace"Amana..?
Wata Amana kuma?
Sadiya ta gyara zama tana Fadin"Au har kin manta..?
Amanar da na Damka miki Ranar Daurin auranki..."
Muhibba tayi shuru tana Tunani har ga Allah ta manta cikin wani yanayi tace"Ki tunamin Adda na manta."
Sadiya ta kalleta Cikin ido kai Tsaye tace"Amanar Hamma na da na baki my Sister..Nace ki kula dashi..Ki kula da Abincinsa da Komai nasa sai kuma nagansa duk ya Rame ba yadda nayi Tsammanin ganinsa ba.
Tafada cikin yar Zolaya Muhibba ta Bude baki kafin tace"To ya kike tsammanin ganinsa..?
Adda tace"ah na gansa yayi katon ciki mana yana Tafiya Dakyar.!"
Me Muhibba zatayi in ba Dariya ba Adda Sadiya na tayata tana Fadin"Eh mana ammh maimakon katon ciki sai naga duk ya rame..Kuma nasan My Sister ta iya Girke girke masu Dadin da in Hamma ya same su da yanzu ya zama Tulele."
Muhibba na Danne Dariyanta kafin tace"ai in ya zama Tulale bazai ganu ba.."
Sadiya tace"Ai nafi son ganinsa haka bana son yana rama."
Muhibba tace"Shi ya fada miki bana kula dashi..?
Hararanta Sadiya tayi kafin tace"Ko bai Fadamin ba ai ina ganinsa da dan wuya ammh kalle ki kinyi Bul bul Dake Daga alamu dai ya fiki iya Kiwo.
Muhibba tace"Ai ba Laifina bane."
Adda tace"To kaji ki laifin waye kuma..?
Muhibba ta sauke numfashi kafin tace"Nashi ne mana baya cin abincina ko na girka.
Adda aranta tace an zo wajen kafin tace"Bangane ba..?
Kin taba bashi ne yace bazai ci ba..?
Muhibba ta girgirza kai kafin tace"Gaskiya ban taba basa ba..Naga dai baya bukata ne kuma bai Taba nema ba."
Adda ta gyara zama tana fadin"Basai ya mema ba ko yace yana Bukata ba Muhibba..Hakki ne akan ki a matsayin ki na matarsa ki Dafa ki basa yaci ke ko da zaki shekara kina Dafawa bai ci bane hakkin yana wuyan ki ne, Ballatana nasan waye Hamma na yana da kyamkyami ammh na Tabbata ke zai iya cin abin hannunki in kika dafa kika basa bazai ki ci ba."
Muhibba tayi shuru jikinta yayi sanyi Sadiya data Fahimci haka sai ta Dafa kafadarta tana Fadin"Saurareni Dakyau Muhibba..Ba Domin Hamma na Dan"uwana ba Sai domin gaskiya sunanta gaskiya..Daga kuma kin ta sai Bata ne..Ki sani Ubangiji bazai taba miki Uzurin domin bai taba Tambayarki ba..Ke dai ki gyara zaman auran ki da Lahirarki,Sannan kuma kamar kanwata na Dauke ki Ina so ki yi zaman aure irin na kowaccr mace yar Gatam mijinta,Sannan ina so ki kula da Hamma ma bai samu kulawar kowa ba,ba cikin mu ya tashi Rayuwarsa kusan gabadaya cikin kadaici yayi sa don Allah Muhibba ki cire komai aranki ki rike auran ku hannun Biyu Hamma na bai da matsala ba kuma zaki samu matsala dashi ba da yardan Allah"
Ta fada cikin wani yanayi Muhibba taji gobobinta sun yi sanyi cikin wani yanayi tace"in sha Allahu Adda nayi miki alkwarin zan gyara in muka koma gida"
Adda Sadiya tace"a"a basai kun koma gida ba..Daga yau daga yanzu nake so naji kince zaki gyara"
Muhibba tace"To zan gyara Daga yau in sha Allahu"
Adda Sadiya ta washe baki kafin ta Rumgumeta tana Fadin"Thank you my Sister Allah ya zaunar daku lafiya"
Ta amsa mata da Ameen kafin su Saki juna Muhibba ta kalli Adda cikin marairaicewa kafin tace"Ammh nan zai barni na kwana gunki ko..!"?
Sadiya tace"A ina..?aiko ya barki bazan bari ba gidan ki zaki koma bari ma ki gani."
Wayarta dake gefenta ta Dauka ta kirasa har sau biyu bai Dauka ba sai ta kalli Muhibba kafin tace"Kin yi alkwarin zaki gyara Daga yau..Nan da Sati Daya nake so naga duk kun kasa tashi Saboda kiba da kwanciyar Hankali."
Muhibba sai ta hau Dariya gaskiya tana Kaunar Adda tana da Dadin zama Hira suka zauna suna ta yi hirar ma Sadiya ke ta bata Shawarwari tana bata wasu Daga Cikin Labaran da Ummi ta Riga ta Fada mata Na auran sa da Majeeda da Amira
Sai bayan sallar azahar bayan sun yi salla suka shiga Kitchen Adda Sadiya nata da Miyar nama farar shinkafa kadai suka Dafa sai suka Hada,kunin aya suka sha,Saai bayan sun gama ne Saifudden ya Kira Sadiya da Zumudi ta Dauka tana Fadin"Hamma.."
Cikin Muryansa yace"Addata ina meeting ne dazu din"
Cikin jin Dadi tace"Bakomai..Daman tambayanka zan yi gidan ka na kaduna kana da kayan abinci ne.?
Cikin mamaki yace"Me ya faru..?
Adda Sadiya tace"To hamma ba chan kace Muhibba zata zauna ba kafin Weekend..?
Cikin basarwa yace"In ta amince ba.."
Da sauri tace"ta amince wlh Hamma."
Baki ya rike kafin yace"Addata.."
Da Sauri ta Katse shi da fadin"Haba Hamma na.."
Sai ta bashi Dariya sai da ya murmusa kafib yace"Kinsan ba girki na iya ba..Babu komai cikin gidan man ban da kayan Tea"
Adda Sadiya tace"Shikenan Hamma ina neman iziinka zamu fita Kasuwa da My Sister."
Har ga Allah bai gane wacce take nufi ba shiyasa yace"Wace ce haka?
Tana Dariya tace"Matar ka mana MUHIBBA ba.."
Ajiyar rai yayi kafin yace"Adawo lafiya"
Ta amsa da Ameen ya katse wayar cikin jin Dadi ta kira Mujaheed bai Dauka ba sai ta bar mai Sako Muhibba na Dakinta Lokacin bata san mganar da sukayi ba zuwa kawai tayi tace ta shirya zasu fita daga chan zata rakata gidanta.
Ba musu ta shirya ita ta Goya mata Nihad
Adda Sadiya zata tukasu a Motarta ta Honda,Muhibba na gidan gaba bayan ta saka kayanta a Gidan baya suka kama Hanya suna cikin Tafiya sai ga Alert ya shigo wayar Sadiya tun kafin ta Duba Taga Firstbank kuma tasan wanda ke da Amana da wannam Bakin Hamma ne
Sai da suka isa katon Shagon provisiom dake kan Titin anguwan Rimi ta bude sakon Dubu 100 cash ya Turo mata Mirmishi tayi shiyasa ta sha Fadama ya Mujaheed Muhibba ta Musamman ce a wajen Hamman ta.