← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 144

Sashe 86

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sani yace"Sai Hamdala"
Saifuddeen yace"To Allah ya taimaka"
Sani ya amsa da Ameen Sani Cikin Girmamawa yace"Mu shiga ciki Yallabai..Sai hakuri yarinyar nan da ta shiga ba wanda ta sanar ma tare kuke Shirme gareta kamar yar fari"
Saifudeeen ya Murmusa kafin yace"Ko ba yar fari bace ai Auta ce ko Barrister
Sani na Dariya yace"Kwarai kuwa yallabai..Bismillah"
Gaba yayi shi kuma yana Binsa a baya har Falon Inna Sani ya fara shiga shi kuma ya Duka yana kwabe Takalminsa sannan ya shiga a gefe ya zauna Inna na chan gefe tayi Saurin Fadin"A"a dawo saman Darduman kada ka zauna a kasan Leda"
Bai yi musu ba ya koma saman Darduman da Inna ta shimfida mai kansa na kasa ya shiga gai she da Inna ta amsa cikin Sakewa tana tambayansa aiki ya amsa mata da Lafiya Inna tace"To Allah ya taimaka wajen su Zaliha mutanen Gaya duk Lafiya suke..?

Kwana Biyu bamu yi mgana da Alhajin ba.."
Kan na kasa yace"Duka suna Lafiya suna gaishe ku"
Inna tace"Muna amsawa mun gode kwarai"
Sai sukayi Shuru Sani ne ya mike yana Fadin"inna bari na yi ma Ya Habibu mgana"
Inna tace"Na aiki muhibba sai dai kasan Halinta kila ta hade da Zeenatu ta manta aiken da nayi mata"
Sani ya fice yana Fadin"Kadan daga aikin Autarki inna.

Inna Dariya tayi bata ce komai ba Sani na Fita suka kusa cin karo da ya Habibu kallonsa yayi kafin yace"Miye haka..?Kana tafiya baka kallon gaban ka..?

Sani na sosa kansa yace"Ina kwana Babban yaya"Amsawa yayi yana girgiza kai kafin yayi sallama Dakin Inna ya shiga gefen Saifudeen ya zauna Lokaci ya basa Hannun sukayi musabaha suka gaisa Sannan ya Juya yana kara gaida Inna duk da sun gaisa da ya Dawo sallar asuba.

Inna kanta na kasa tace"Auta sai ita..Tare da mijinta suke tafe ta shigo Tana shiririta"
Ya Habibu yace"Nima Zeenatu ta shiga tana Fadamin"
Sai wajen yayi shuru agogon Hannunsa Saifudeen ya Duba yaga goma tayi sai ya laluba aljihunsa ya Fito da Bandir din kudi Sabbin ya Mike ya je har gaban Inna ya Duka ya ijiye mata sannan ya mike yana Fadin"Inna ni zan wuce"
Inna tace"A"a kada mu yi haka dakai kazo ka kwashe kudin ka"
Bai juyo ba ya mikama ya Habibu Hannu suka sake musabaha Lokaci daya yana Fadin"Inna ni D'anki ne in Sani yayi miki kyauta nasan karba zaki yi ki saka mai albarka"
Sai Inna ta ji kunya kanta na kasa ta shiga sakamai albarka ya amsa da Ameen Ameen tare suka fito da Ya Habibu har kofar gida shi da Sani sun yi mai Rakiya Ya Habibu ya kalli Sani yana Fadin"Sani shiga kayi ma Auta mgana ta fito su tafi"
Da Sauri yace"A"a ya kyaleta sai an juma zam zo na Dauketa"Haka ya samu kansa da Fada ba domin haka yayi niyya ba Sai dai haka kurum yaji bazai ce tazo su tafi ba ganin yadda take Murna shi kuma cikin Abu zai shiga yana Da Karatu da yan Masters.

Ya Habibu shigewaa ciki yayi ya bar shi da Sani Musaba suka karayi Saifudeen na Fadin"Barrister muna jiran ka fa"
Sani yace"In sha Allahu Ranka ya Dade'
Saifudeen yace"Ranar Monday zan koma Kaduna da Safe.

Sani yace"Shikeman gobe zan shigo in sha Allahu"
Saifudden ya amsa da suna jiransa Kafin su yi sallama acikin aljihun Sani ya saka mai kudi Sani na Fadin bazai karba ba Saifudden ya shiga mota ya wuce bakin Hanya ya Tsaya ya Kira su Bama ya yi musu kwantance in da yake suka zo suka Same shi suka Tukasa zuwa Cikin makaranta.

Ita kuwa Muhibba sai daga baya ma tasan Saifudden ya tafi ya barta ta Yini murna har da Tsallenta ita kanta Inna taji Dadin haka matuka.

Ita da Inna sun sha Hira sosai kamar sun shekara basu Hadu ba,Anty Habiba ta Kira Inna Muhibba ta Dauka suka yi mgana tace ba Domin bata jin Dadi ba da tazo Muhibba tace in sha Allahu zasu zo gidanta shima Da haka sukayi sallama.

Muhibba ta sha na gida Tun Safe har shidda na manya sai kuma Hankalinta ya koma gida bai kirata ba itama bata kirasa ba bayan ta Idar da Sallar mangariba suna zaune da Inna ta kalleta Tana Fadin"Auta ya kamata ki koma gidan ki fa dare yayi.."
Muhibba ta muskuta kafin tace"Inna ai bai zo ba har yanzu"
Inna na Hararanta tace"To ba sai ki kirashi kice kin shirya ba kin barsa da yunwa Auta ko kin yi wani abu ne kafin ku fito.?

Kai ta girgiza kafin tace"Inna ni fa bai gayamin nan zamu zo ba"
Inna tace"To maza ki kirasa kin bar bawan Allah da yunwa sakarya kawai"
Tana Tura baki tana komai ta Dauko Wayarta ta kirasa har ta katse bai Dauka ba Lokacin kuma yana masallaci ne wayar sa kuma Tana gida Tana ganin bai Dauka ba tace ma Inna"To bai dauki wayar ba"
Saboda Haushi Inna ko tanka ta batayi ba,bata jirga daga wajen ba Sai ga Kiransa ta Dauka da sallamarta Cikin Siririyar muryanta ya amsa mata Cikin yanayinsa shuru yayi bai yi mgana ba, itama kuma sai ta kasa mgana Cikin Dauriya tace"Arm na shirya ina ta jiran ka"
Cikin Kasala yace"Ok su bama zasu zo Daukan ki"
Da toh ta amsa mai sannan suka kashe wayar da Inna ta tambayeta zai zo ne Eh kawai tace mata tashi Tayi ta shirya tace Inna ta Dibar mata garin Tuwo data ga tana dashi sai Innar ta Hada mata har da kuka da Kubewa Domin Muhibban tace nata duk sun Lalace bata taba amfani dasu ba.

Ta shiga shashen Ya Habibu sun yi sallama Tana dakin Inna suna Hira da Sani ya Kirata yace suna waje suna Jiranta kwatance yayi musu duk da sun Taba zuwa sau daya basu manta gidan ba.

Sani ya Rakata Har Bakin mota sukayi sallama akan gobe zai zo ta hada mai Gara suna Hanya aka kira sallar isha"i suna shiga gidan shi kuma ya Fito da Shirin tafiya masallaci har ga Allah taji Dadi ta tabbata ko bata a kusa zai iya taayawa kam Ibadarsa ba kamar baya ba da Rauninsa yafi bayyana..

Tana shiga itama alwalan ta Dauro ta Gabatar da Sallah ta kai kayan da Inna ta bata Kitchen ta sanar ma Inna kyautan da Ummi ta bata akawo mata Inna nata saka albarka tace Sani in yazo Gobe sai ya taho mata dashi Inna nata Hamdala tana Fadin ashe zata ga auran muhibba har da abun alheri Daga mijinta da Danginsa Dubu Talatin Saifudden ya bama Inna Sani kuma Dubu ashirin don Sani har yayi Rubutu ya ijiye Saifudden a matsayin wanda ya taba mai kyauta mafi Girma da Daraja.

Tasan bai ci wani abu ba yasa ta Fara kokarin Sarrafamai abu mai Sauki Taliya tayi Jallop mai kifi ya shigo tana Saka Taliyar jin kamshi yasa ya leka Kitchen din yana ganin abunda take yi ya Sauke ajiyar rai ta juyo tana kallonsa tayi mai Sannu da zuwa ya amsa Lokaci daya yana Fadin"Kamar kin san tun breakfast din Safe ban kara cin wani abu ba"
Ya fada yana Ficewa Daga kitchen din kai ta girgiza ai ta sani daman shiyasa bata baro kitchen din ba sai da ta kamallah ta zubomai ta kawo mai sai ta Hado mai da Ruwan zafi tasan duk Dare sai ya sha Tea yake iya barci ita bataci ba,ta koshi tun abincin da suka ci ita da Inna agida.

Yau Hirar tasu batayi tsawo kawai ya Fadamata Sani zai zo gobe tace sun yi mganar Daganan yaga ta fara gyangyadi sai yace taje ta kwanta shima Labaran karfe tara ya kalla sannan ya kwashe komai ya koma Daki yayi shirin barci.

Kamar wadanda sukayi barcin wahala Dukkansu sun makara sai shidda na Safe suka tashi ita taje tashinsa ta iske sa har yayo alwala zai Tada sallah shi ya zata ta ta shi ne ya makara ganin haka yasa ta shigo Dakin Daman da alwalanta da Hijabinta yana ganinta sai ya kalleta itama ta kallesa kafin yayi mgana ta Rigasa da Fadin"Nima makara nayi..Kayi mana jam"i"
Kamar yace"A"a sai dai ba Dama hakanan ya jasu jam"i tun a wajen karatun ta Fahimci akwai matsala Sabbi ya karanta a Raka"ar Farko ammh haka ya Dinga Tsallake ayoyi sannan karatun bai zauna ba Tajweed har sunan Allah ya na sauya ma Ma"ana a raka"a ta Biyu Abasa ya karanta ai bai gama ba Tayi gyaran murya yana jin haka sai yace Allahu akbar suka tafi Ruku"u"
Lokacin daya sallame ta ya kasa Hada ido da ita yau yasan ta gama Fahimtar komai bayan Raunin Ibada a bangaran Addini bai san komai ba,Itaa kuma sai Tsausayinsa ya kamata Allah Sarki bai samu Tarbiya uwa yadda ya kamata ba ballatana ta Kula da Tarbiyansa kamar yadda tayi ma Ummi da Adda Sadiya alkwari sai ta cika shi da yardan Allah.
Chapter 86 · 0% Book details