← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 144

Sashe 96

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta Karishe Fada Cikin kuka Anty Habiba ma jikinta duk yayi sanyi Tun Sanda aka kawo Muhibba inna ta Kirata tana kuka ta Fadamata ta Taho Abban walid ma Da Daddaran nan yazo ya Sameta jinta shuru bata Dawo ba yazo ya iske Lamarin ba Dadi.

Mallam Haruna ya gyara zama yana Fadin"Haka suke Inna suna irin wannan al"amarin su yi Lambo kamar sun tafi sai daga baya su dawo..Tabbas bai bar Bibiyanta ba yana Tare da ita kuma abunda ya nuna Zaman aure ne bazai barta tayi ba Matukar ta cigaba da zama awannan gidan sai ya Illata Lafiyar kwakwalwarta ta hanyar Firgitata"
Gabadaya Salati suka saka Anty Zeenatu tana Tsakar gida ta kasa shiga Tana da tsoro sosai jikinta sai rawa yake yi,Ganin yadda yaga sun Rude ne Inna ta fara koke koke yasa ya Dagatar da su yana Fadin"kada ku damu da karfin Allah zamu koresa Daga Rayuwarta,yanzu dai mafita Daya zata zauna anan gidan zamu cigaba da bata mgunguna Na tsarin aljanu har zuwa wani Lokaci mu gani"
Inna tace"Daman ai bazata koma ba..Habibu sai ya kira megidan nata ya Sanar dashi Halin da ake ciki"
Mallam Haruna ya mike yana Fadin"Yanzu zan koma Garzali zai kawo muku wani mgani ku saka mata a Ruwa ta sha..Biyu zaku raba yanzu da kuma da Safe,gobe in Allah ya kaimu zan zan bada ruwan addu"an da zata sha tayi wanka dashi na kwana bakwai gefe daya kuma kada mu zauna mu rika gayama Allah Itama ta Daure tana zama da alwala Sanya karatun alqur"ani da azkar din Safe da maraici da yardan Allah sai ya Rabu da ita"
Jin bayanin Mallam Haruna sai suka ji salama kadan,Ya Habibu ne ya mike ya fita rakashi Inna na bin sa da Godiya,har ya fita Muhibba kuka take yi,Tana jikin Inna Anty Habiba ta matso kusa da Inna ta Dafa kaina Tana Tofa mata addu"a Abban walid ma sai gyada kai yake yi al"amarin akwai Tausayi aciki.

Ya Habibu da kansa yabi Mallam Haruna gida ya karbo mganin Ko da ya Dawo na kara rikicewa,Shi ya jika mganin a ruwa,suka Rikeni suka bani,na sha ban jima ba na Bingire da barci Inna da Anty Habiba suka Daukeni suka sauke ni kan gadon Inna Anty Habiba na kaina tana ta Faman Tofamin addu"a.

Ya Habibu tattaunawa suke yi da Abban walid,Sai ga kiran wayarsa yana Dubawa yaga Saifudden ne Cikin Damuwa ya kalli Inna yana Fadin"Ga megidan nan nata na kira kila ya kirata bai Same ta bane"
Yana gama Fadin haka ya Daga kiran cikin Ladabi suka Gaisa kafin Saifudden yace"Ya Habibu muhi tana gida ne..?

Nayi ta kiran wayarta a kashe yau bamu yi mgana ba Dayake ban samu zama bane"
Ya fadi haka ne Saboda ya Kira Junaidu ya fadamai muhi bata Dawo gida ba sai yayi Tunanin tana gida..

Ya Habibu bai boyemai komai ba ya Zayyanamai abunda ke faruwa,Sai yanzu yasan Dalilin kiran D.Musa daya gani ya Firgita ya shiga Tashin hankali cikin Firgici yace"Yanzu tana ina..?

Ya Habibu yace"Gata tayi barci..Ta sha wani mgani da malamin da ke Dubata tun shekarun baya ya bada yace zata zauna anan zuwa sati daya"
Saifudden ya Sauke Numfashi kafin yace"Zan taho yanzu"
Da Sauri yace"A"a Dare yayi ka bari sai gobe Sabo da Dare..Duk muna nan zamu kula da ita da yardan ALLAH"
Bazai iya mai gaddama ba ne yasa ya amince da mganarsa ammh Barcinsa Kusan Rabi da Rabi ne Hankalinsa ya Tashi da gaske gaske dai Muhi dinsa aljanu na Bibiyanta.

Anty Habiba gida ta koma ta kwana Duk da taso ta kwana Inna ta Hanata ammh da Sassafe ta Dawo gidan Lokacin Muhibba ta tashi har ta Rama Salolinta sai dai bata mgana sai kuka Sannan abu kadan sai ya Firgitata.

Karfe Takwas da wani abu na Safe Saif ya Diro gidan Ina ganinsa kamar naga Wanda zai min gafara ban ji kunyar su Inna ba na Nufesa da gudu na malakesa ina Kuka shi kuma ya Rikeni cikin Fitan Hayyaci da Damuwa sai da suka bamu waje kuka nake yi mai ina Fadin"Na ganta tana min Dariya tana miko min hannu..Jini ajikinta ko"ina"
Bayana yake shafawa yana Fadin"Relaz bata isa tayi miki komai ba Domin ina Tare da ke"
Sai da nayi barci ya samu Ganawa da su Inna Ya Habibu yayi mai bayainn da mallam Haruna yayi musu shifa ba Domin kada yayi gaddama ba da yace bai amince ba malaman nan wasu duk macuta ne ammh sai da yace ma Inna"ko asibiti zamu kaita ne suma su duba su gani.?

Anty Habiba tace"Matsalan Muhi bata asibiti bace gaskiya"
Yana ji inna na kara mai bayanin wannan aljanin ne mai zuwa da Sufaffarsa bai Daina Bibiyan Auta ba Shi kuma bai amince da mganar ba cewa yayi yana son mgana da Mallam Haruna din Ya Habibu ya rakasa gidan sa suka shiga har Dakinsa yana ta wanke Rubutu a Allona Saifudeen duk
sai yaji wani irin barin ma dayake musu bayanin Rubutun na Muhibba ne.

Ya tambayi Saifudden an taba yin saukan alqur"ani agidan da suke yace mai A"a nan ya bada Shawaran ya kamata ayi din kafin komai ya Daidaita bai bar gidan ba sai da ya bada kudin Sadakar Sauka din da kuma na almajiran da zasu je su yi sannan suka bar gidan,karo na Farko Daya taba Kiran Ummi ya Fada mata wani abu na Faruwa Ummi ta Shiga Damuwa sosai ita ta Kira chan Gaya ta sanar da Kawu shi kuma ya fada ma su Mama zuwaira suna ta jajanta Lamarin.

Aranar sai ga Adda Sadiya da ya Mujaheed sun diro gida ya cika da makota da yan"uwa Ni dai sai barci nake yi mganin kamar mai saka barci,sannan an kawo ruwan Rubutun na fara sha da wanka sai dai in bi mutane da ido kawai duk na Rame na lalace sai wuya da zuru zurun ido,Sai washegari aka fara Saukan alqur"ani Adda Sadiya nan ta kwana Saif da Mujaheed gida suka kwana sai da Safe suka zo in naga Mijina sai naji kamar shine waraka naa agaban mutane nake makalesa da kuma shi kadai nake mgana sauran mutane sai dai na bisu da ido kawai.

Aranar Ummi ta iso ita Kadai,Mama zuwaira da Umma babba da kawu sun zo aranar suka Dubamu kowa da irin nasa mganar Sai dai an fi Raja"a akan Saifudden ne ya Dawo Rayuwata Domin ya Hanani zaman aure ni kuma bana jin haka ina Hango wata Kaddara ce ta Dabam take Faman Bibiyata.

Su ummi basu kwana ba su Adda Sadiya tabi zuwa kaduna zata kwana washegari ta koma Abuja su kawu ma da yammah suka tafi chan gidan su Baffa Surajo dai ya Habibu yace kada a Sanar dasu Saboda sai a Tada musu Hankali shiyasa aka kyalesu kamar yadda Mutanen Lere ma ba wanda yaji,Ranar Litini da rana malaman makarantar mu suka zo gaisheni har da D.Musa kwan su da kwarkwatan su suke bada Labarin abunda ya Faru Tun
ballatana ma Anty Debora da agabanta komai ya faru sai jajanta Lamarin ake yi ana Fadin sharrin junnu ne.

Kwana Hudu akayi ana sauka Qur'ani agidan mu na Gra sannan aka gama,Ni kuma ina gida ina amfani da mgunguna su Habbatus sauda judda,jikina har ya Saba da warin irin mgungunan ga na Rubutun da nake sha ina wanka dashi Sannan karatun Qur",ani da shi muke kwana Ni da inna Alhamdulillah Sauki ya fara samuwa Ranar Larabara Saifudden ya koma kaduna Da niyar sai Friday zai dawo.

Ranar da na cika Sati da Dawowa gida ni kaina nasan na ji sauki sannan ban kara jin komai ba ko ganin komai ba mallam Haruna ya jaddadama su Inna Cewa komai meke Tare dani da Yardan Allah mun rabu kenan zan iya komawa gidana ba matsala.

Sai dai Kowa ya aminta da Nemo min yarinyar da zata tayani zama Saboda in wani abu ya taso,Gida kuma su Anty Habiba sun je sun share ko"ina sun gyara,Saif kuma yace a barni agida na kara Hutawa.

Duk wannan al"amarin da ya Faru Sani bai sani ba yana makaranta Ya Habibu ya hana asanar dashi kada yace zai baro karatunsa yazo.
*Janafty*
*SFD0035*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
Sai da na shafe sati biyu a gida sannan aka samo min yarinyar da zata tayani zama mai suna wasila yar kimanin shekara goma sha biyar a duniya karamar yarinya ce nan saman mu suke Mahaifinta ya rasu sai mahaifiyarta mai suna Lami,Asalin su mutanen zamfara ne.

Inna taje da kanta ita da Hajiya karima mahaifiyar Anty zeenatu suka mata bayanin Komai nan da nan ta amince har da kukanta tun ballatana ma da taji cewa duk watan duniya dubu Talatin za'a rika biyan diyar tata sannan ba wani aiki ba ne kawai zata taya mai gidan zama ne,su Inna sun fada mata duk karshen mako in megidan ya dawo wasila zata Dawo sai in ya koma sai ta koma gidan Lami tayi ta godiya daman rayuwa tayi musu Tsanani matuka abinci ma na neman gagaransu.
Chapter 96 · 0% Book details