← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 118 OF 144

Sashe 118

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin mamaki suke kallon sa Har da ni da Kalaman sa suka Dauremin kai a Ina yasan Saifudden..?ban manta dashi ba sai dai Tunaninsa ne ya Shafe q kaina abun mamaki yanzu sai naji ina gane abubuwa kad'an kada'n..

Umarni ya bada akan k
owa ya koma ya zauna jiki ba kwari suka gyara zama Mallam Surajo yace"abun da yasa nace bIbiyar Ahali ne..Ba ita Kadai ya ke Bibiya ba..Gabadayan ku ne..Sai dai ita kadai ce ya Bude ma Ido tana ganinsa saboda ita yarinya ce karama alokacin'
Ya Habibu da Anty Habiba suka kalli juna kafin su hada baki wajen fadin"Bamu gane ba mallam'?

Fuskarsa da Mirmishi yace"Zai yi bayani da kansa ai yana nan Wajen acikin Dakin nan"
Gabadaya sai kowa ya fara waige waige cikin Tsoro da Firgici ganin haka yasa yace"Kada ku razana shi din ba mai cutarwa ba ne.

Waye kai..?

Wata kakkausar murya tayi mgana acikin Dakin"
Sunana SAIFUDDEEN Kuma ni ba Mutum ba ne ina Daga cikin jinsun Aljanu"
Gabadaya Dakin kowa sai yadan Samu salama jin muryan cikin kamala da Dattako sai dai Firgici na jin mgana da kuma rashin ganin wanda ke mgana.

Cikin Sanyin murya Shima mallam Surajo ya kara cewa"
Miye hadin ka da wannan baiwar Allah..?me yasa kake Bibiyarta..?

Ko zaka cutar da ita ne..?

Shuru dakin ya Dauka na wani Lokaci kafin wata iska ta taso ta Tirnike Dakin kamar Hayaki Hatta da Tafin Hannunka baka iya gani Cikin abun da bai fi mintina goma ba sai Dakin ya washe gabadaya su Ummi sun Tsorata
Kada mujaheed yaji labari kamar yayi fitsari a wando saboda firgita.

Abun da ya bama kowa mamaki Daya sa suka Zabura gabadayan su ban da Saifuddeen dake zaune gaban Mallam Surajo shi da Muhibba Yana kamkame da ita kamar wani zai kwace mishi ita.

Cikin wata irin murya wacce daga jinta sai jikinka ya yi sanyi in ma bai Fara rawa ba yace"Ni ba mai cutarwa bane..Amana ce Sannan Alaqa ce mai Girma Tsakanin Mahaifina Abu Gaddaz da mahaifin Muhibba tun Lokacin yana Raye..Aminci ne da Girman alkawari Tsakanina da wannan Ahalin"
Zabura Muhibba tayi Daga jikin Saifuddeen idanuwanta na kallon sa Ta nuna sa da Hannu cikin Rawar murya tace"SAI..F..DDEE...NN...!

Sai ta juya ta kalli na kusa da ita kawai sai tayi luu ta Fado jikinsa a Sume cikin wani yanayi ya fara Girgizata yana kiran sunanta bata riga ta sume gabadaya ba yasa ta Farfado a firgice tana nuna inda taga mai kama da Saifudden abun mamaki yana Tsaye a wajen hatta da komai nasu iri daya ne hatta kayan jikin Saifudden Da komai babu bambamci ba ita kadai ba kowa a wajen sai da ya Firgita yana makyarkyata.

Daga sun kalli Saifudden sai su koma su kalli wanda ke chan nesa da su,Idanuwana kamar zasu fado kasa Saboda Firgici ni kuma sai naji Tsoron ya sake ni na mike da Taimakon Saifuddeem na sake Nunasa ina Fadin"SAIFUDDEEN..!

Kai tsaye ya gyada min kai Lokaci Daya yana fadin"Da gaske Sunana SAIFUDDEEN muhibba..'
Muryan ma iri daya la'illaha haka suke Fadi acikin ransu mallam Surajo bai yi mgana ba shima Saifudden ya Shiga Rudani cikin Fitan Hayyaci yake fadin"Kai kai ne..Saifuddeen din da ke zuwa ma Muhibba da Suffata.?

Yafada yana kara Tabbatar ma da kansa ba bambamci komai nasu iri Daya tamkar shi anan.

Saifudden ba mutum ba ya yi kayattaciyar Dariya kafin ya kalli Mallam Surajo yana fadin"Ko da basu zo wajen ka daman zan bayyana kaina a gare su duk da ba Umarnin da aka bani ba kenan..Ni Umarnin Mahafina nake bi akan wannan Ahalin..Mahaifin su mallam Bello ya Taba taimakon wani Tsoho a Garin Lagos agege da Daddare ya gansa yana Tafiya yana rawan sanyi sai ya Cire babbar Rigarsa ya sanya mai yana Fadin"Baba ka daina yawo ba Rigar sanyi..Sanyi zai yi ma Lafiyar ka illah"
Sai Tsohon yace"Yaro bani da ita kayan jikina Kadai suka Ragemin"
Da jin haka sai Mallam bello ya Ruga masaukinsa ya kawo ma wannan tsohon duka kayansa ya basa yana Fadin"Baba gashi ka tafi dasu..Ni ina da wasu kai kuma baka dashi"
Tsohon ya dafa kan mallam bello wanchan lokacin yana Fadin"In sha Allahu zuru"arka bazata taba Tabewa ba"
Basu rabu ba sai da ya bashi kudi a hannunsa sannan ya rakasa har bakin Hanya inda ya nuna wani waje yace nan ne masaukin su shi da yan'uwansa to wannan Tsohon ba kowa ba ne illah Mahafina Sarkin Aljanun Masar Abu Gaddaz"
Sai Dakin ya Dauki wani Shuru kamar ba kowa aciki Mallam Surajo yace"Allahu akbar cigaba da bayanin ka Bawan Allah Saifuddeen!

Saifuddeen ba Mutum ba,ya cigaba da Fadin"Tun daga wannan Ranar Mahaifina ya nada ni a matsayin wanda zai rika bin bayan Ahalinsa.
ni dansa ne daga cikin ya"ya Dari da Mahaifina yake da su kuma yafi ji Dani.Sannan ne ni kadai ne Namiji Sunana YARIMA saifuddeen.

Na zabi na rika bibiyan su ta Hanyoyo Dadama da su basu sani ba Sai dai nafi Shakuwa da Muhibba saboda itace karama sai na Bude mata ido da yasa take ganina mun shaku matuka da ita ina Daukan ta na kaita duk inda naga Dama kuma na Dawo da ita Har ga Allah mu bama su Cutarwa ba ne..na Daina bude mata ido ne Tun Sanda Hankalin Inna ya fara taahi a kaina Sai Ta daina ganina ammh Tana jin kamshin Turare na sannan tana gane ina waje saboda kaifin Basirarta Faduwar da tayi sau biyu a makaranta Duk ni na Shafeta Saboda akwai wani aljanni daya ganta yaso ya shiga jikinta na hanasa na Biyu kuma Ta taka musu yaron su a bayin makaranta suka so su shiga Jikinta na Hanasa da yake mu Sarakai ne na Musulunci Kafiran cikin mu Suna bala'in Tsoron mu sannan Masarautar mu tana da karfi Sosai acikin Duniyar mu ta aljanu"
Dakin sai ya kara Daukan Shuru kwakwaran motsi ba wanda ke yi ammh Daga gani Kowa ya samu natsuwa ba kamar abunda ya faru dazu ba.

Mallam Surajo yace"Abubuwa Dadama sun faru da wannan yarinyar..Daga gani baka da masaniya ne sannan meyasa ka zabi ka rika Fitowa a sufar wannan Saifuddeen din dashi ne mijinta a yanzu..?

Ka san shi ne..?ko ka na da wata boyayyiyar alaqa da shi wanda mu bamu sani ba..?

Sai da ya Dauki Lokaci kafin yace"Nayi Takaicin Lokacin da na dawo Daga aikin da Mahaifina ya bani Ragamarsa ban iske wannan Azzalumar ba da sai ta raina kanta..Dawowata kenan Daga Wata Duniya Birnin Sin naje wani Fadan Rikice ne wanda ya barke Tsakanin Masarautarmu da ta kafiran cikin mu Shekara kusan Uku ban san abunda ke Faruwa ba kuma mahaifina ya sani ammh bai sanar dani ba Saboda baya so na Raba Hankalina ammh Tabbas nasan Muhibba tayi aure Domin har Taron Daurin auran ta naje Daganan Tafiyar ta kamani yau din nan nq Dawo sai kuma naji abunda ke Faruwa..Mganar Suffa kuma bani da wata alaqa da Saifuddeen ni Musulmi ne,Nasan Ma"anar Rantsuwa Wlh Tallahi bai sanni ba..Ni dai na san shi Domin ajinsin mutane Shi kadai ne yake Burgeni shiyasa na zabi in zan bayyana kaina a suffar bil'adama nake bayyana a sufarsa..Hatta kayan jikina na shi na ke zuwa na saka na kuma Fesa Turaransa acikin Dakinsa bai Taba Sani ba Saboda ni ina ganinsa shi kuma baya iya ganina ni ba Allah ba ne bansan cewa Allah ya hada Kaddaran Muhibba da shi ba ban kuma san zasu zama miji da mata ba Sannan ban san Aljana na Tare dashi ba Iya abunda Allah ya bamu ikon Sani muke sani bama Tsallake Hurumimu bamu daga cikin masu son sanin abunda zai Faru gobe da Jibi"
Shuuu..Kamar wucewar iska sai Kuma ya bace sai dai muryansa tana Cigaba da amsa kuwwa acikim Dakin Cikin Sanyi da Taushi yace"Ku min gafara na Dauki Lokaci ban zo ba..Ni ba mai cutarwa ba ne..Na tafi ba tafiyar gabadaya ba..Alkawari ne Bibiyar Ahalin ku har jokokin ku da Duka Zuru"arku gabadaya"
Daganan sai komai ya Tsaya cak Dakin yayi Duhu sai kuma Haske ya bayyana Saifudden ya jawo Muhibba ya Rumgume yana Sauke Numfashi kowa ya kasa mgana Mallam Surajo ya Muskuta yana fadin"Ba zasu taba Cutar da ku ba..Kuma baza su bari a Cutar daku ba..Sai dai abun da Allah ya Kaddara Faruwarsa kamar yadda ya Faru yanzu..Shiyasa ko a ina kaga wani na neman taimako ka taimakamai baka san wani irin mutum ba ne shi kuma su aljanu suna Girmama Alheri fiye damu mutane Shiyasa in wani Daga cikin Ahalin mu yayi musu abun Alheri sai su rika Bibiyar wannan ahalin Tunda ga Ya"ya har zuwa karshen wannan zuru"ar"
Kawu ya jinjina kai yana Fadin"Iko sai Allah..Lokacin da abun ya faru tare da shi bello muka je Lagos din Siyar da Dabobbin mu a gabana yazo ya Dauki kayansa yaje ya kyautar daya Dawo har ina mai Fada kallo na kawai yayi yace"Sunusi mu gode ma Allah ya bamu Ni"imomi ta Hanyar da bamu zata ba..Mu muna da kaya fin kala goma wani Daya garesa fa"
Alokacin sai nace mai"To kai wanne zaka sanya baka da ko daya fa sai na jikin ka..?

Mirmishi yayi min kafin yace"Allah zai kawo..Allah daya bani wada'nan shi zai sake bani wasu"
Allahu akbar Allah ya jikan Bello Alherin sa na gari ya bisa har cikin kabarinsa Da sauran iyayan mu da suka Rugamu gidan gaskiya"
Gabadaya aka amsa da Ameen ni kuwa mamaki nake yi kenan da gaske Saifudden ba Mutim ba ne kamar yadda su Inna suka fada naji kuma nagani sannan na gasgasta.

Ba mu kara awa daya a garin Bazanga ba muka yi sallama da mallam Surajo da iyalansa bayan su kawu sun karbi Lambarsa Domin bazasu taba mantawa dashi ba.

Awannan karon mota daya muka shiga da Saifudden ina manne dashi Sai dai ba na yawan mgana sai dai bin kowa da ido tun muna Hanya Mama zuwaira ta Kira Ummi cikim Fara"a tace muna Hanya da Fatan Dacewar da suka fita nema.
Chapter 118 · 0% Book details