← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 144

Sashe 28

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Inna ta washe baki Tana Fadin"Yauwa hakan ya kamata Allah yayi muku albarka."
Suka amsa da Ameen ita Muhibba bata Dakin suna shashen Ya Habibu suna kallo ita da yaran sai da ya bar Dakin Inna ya shiga shashen nasu suka gaisa yana ta tsokanar da ta yi yaji tana Dariya,dawowarsa ne yasa ta tarkatasu siyama suka koma Dakin Inna Abban Walid sai goma yazo Daukansu yana chan babban gidan su sunyi Taro Inna Sai Fada take sun yi Dare Muhibba ta kalleta tana Fadin"Inna bafa motar haya bace ta gida ce .ai ba"a dare a gida.

Inna ta harareta tana fadin"To Sarkin Tsari gayamin yana da mota tunda bansani ba."
Yana Tsungunne yana Dariya shi da Anty Habiba sukayi musu sallama suka fita har waje Muhibba ta rakasu sai da taga tashin motarsu sannan ta koma gida,Dakin Inna suka kwana Daman haka suke watarana su kwana Dakinta watarana Dakin Inna,Muhibba ke hayewa gado Inna ita bata Damu da gado ba tana kan Darduma ma sai barci ya kwasheta Muhibba tayi tayi ta hau gado taki shiyasa take kyaleta inna itama akwai kafiyar tsiya.

Washegari Muhibba bata je ko"ina ba, kayanta ta wanke ta hada dana Inna suna kawo wuta ta hau guga bata gama ba, aka yi sallar la'asar tayi wanka tayi sallah ta shirya tatafi islamiya ta Dade bata Leka ba Dagachan ta wuce gidan mallam Haruna baya nan ma agidan tayi sallar mangariba sai da ta jira ya Dawo tasan in ta koma bata gansa ba Inna sai ta kusa sakata kuka da Mita.

Bayan ya dawo Matarsa ta fadamai zuwan Muhibba yace ta turota bayan tazo suka gaisa yamata tambayoyi tana mafarkin Saifudden..?

Tace A"a yace ta karajin kamshin Turaransa..?

Tace A"a tana jin wani alamu duk ta amsa mai da a"a yace tataba mafarkin ana Saduwa da ita..?

Tace bata tabayi ba,Mallam Haruna ya jinjina kai kafin yace taje gida zai zo gobe da yammah yama Inna bayani haka ta koma ta Fadama Inna Duk ta Damu tana Tunanin wata matsalan ne sai da ya zo washegarin Hankalin Inna ya kwanta daya Jaddamata Saifudden ya Rabu da Muhibba sannan shi bamai cutarwa bane gareta da taimakon Addu"a da Qur"ani ya bar Bibiyatan Ranar Inna Har Sadaka tayi saboda Murna Muhibba ta kalleta kawai batace komai ba sai chan tace"Inna wannan murnan kamar an biya miki makka..?

Inna tace"Ai yafi ma kujeran makka Auta..Allah ya taimakemu Wannan Aljanin ya daina Binki..ai dole nayi murna banda mugunta ina mutum ina Aljani abu ba jinsi ba hallita daya ba..Ai sadaka Dole ne Allah ya raba nagari da mugu..!

Shi kuma yaje shi da Allah."
Muhibba tayi dariya har da rike ciki Inna ta kalleta tana kyafci kafin tace"yarinyar nan baki da hankali.
*Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar 09069067488 ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye 09069067488 mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke*
*NIMA MATARSA CE*
*NIMA MATARSA CE*
*NIMA MATARSA CE*
*NA*
*HABIBA IMAN IKRA shahararriyar marubuciyar nan ne da kuka sani YAR GIDAN IMAN wacce ta dad'e tana Nishadantar da ku cikin Labaran ta masu Dadi da Ma"ana a lokacin Publishing sosai ta taka rawar gani Wajen baje muku kolin basirarta da Dad'ada'n Labaran ta masu* *Fadakarwa da Nishad,antarwa game da Wa"azantarwa nasan bazaku manta da GARIN KALLO RUWA BA,Ko kun manta da Labarin Khaleesat da Faruk..?*
*Nasan ko kun manta dashi bazaku manta da MUSABABBI ba, Nasan ma bazaku taba mantawa da Labarin MUGUN BUTULCI ba labarin Samiha da Nasir ga BAKIN DUHU,Irin su BABBAR ILLAH labaran ta suna da yawa na sani kun sani alkalaminta bai zo da wasa ba,Saboda yadda komai na zamani ya koma ta Harkan wayoyin zamani sai itama Saboda masoyanta a wannan karon ta fara Rubutu muku SOFTCOPY na Sabon Labarinta mai Taken NIMA MATARSA CE..labarin da zai tabo bangaran zamantakewa har da ma soyayya da Fadarkarwar duka akan Farashi mai sauki N300 Acct: 0673978719*
*Acct name:* *Abubakar Habiba Imam*
*Bank name:GT bank ko kuma a Tuntubi wada'anan Lambobin domin karin bayani 08033484021 ko kuma* *09069067488*
*Janafty*
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah,haka rayuwar ta cigaba da gangara da dad'i babu dad'i bawa ya amsheta yadda Ubangiji mai sama ya tsaramai.

Ta bangaran Muhibba ta cigaba da zuwa aikinta gefe daya kuma suna ta shirye shiryen Speech and price givingday din da zasu yi a makarantar tasu karo farko tun bayan fara kafuwar makaranta shekaru shida da suka gabata in akace Speech and price giving day ana nufin Rana mai muhimmanci domin Dalibai,Ma"ana yaye su da za"ayi da sauran shagulgulan da makaranta ta tsara musu a karo na farko zasu fara sallaman Yan SS3 da kuma Primary 6 dalilin haka yasa suka shirya hakan Saboda karrama Daliban da kuma Taya makaranta murnan Shekara shida da kafuwarta sannan da Jadawalin Cigaban da suka samu a cikin wad'anan shekarun
Gabadaya suna ta shiri ne ba Daga primary section ba daga secondary Section ba,Saboda taro ne da basu taba yiba sai wannan karon suna bukatar Tsari mai kyau yadda akaron Farko abunda zai kayatar fiye da Tunanin wanda ya samu Hallatar Taron.

Daliban yan SS3 tuni sun fara zana jarabawar ta WAEC,Sannan kuma wasu Daliban ba"a makaranta iyayansu suka biya musu ba sai dai an biya da yawa tunda Sabuwar Center ce sune First bach din da suka fara zana Jarabawar Secondary acikin makarantar shiyasa sai aka shirya a bari sai sun gama Neco gabadaya suma yan primary6 din sun yi Common Interest din sai ayi Bikin Gaddamarwa din kamar yadda aka Tsara komai..

Dalilin haka ne ma Director Musa ya Kira Meeting na malamai gabadaya Ranar Alhamis bayan an tashi Makaranta gabadaya su muhibba sai da suka jira sai uku aka fara Taron a Babban Hall din na cikin makarantar suka zauna Director musa da kansa ya fara Jawabi tunda shi ke da alhakin kula da makarantar gabadaya a Hannunsa malaman duka suna zaune saman kujeru suna Fuskarsa shi da Head Teacher da Sakariyarsa,Sai wani Uncle Abdulwasi bayarbene shi ke kamar mataimakin Director musa,Ammh shi Musa Bahaushe ne Tsantsan Cikakken bazazzagi ne.

Ya fara da jawabin yanayin Tsare tsaren da suke dashi kan abunda kowa ya sani zasu gudanar sannan yace yana Bukatar kowa ya kawo nashi Shawara kan abunda yaga ya dace a kara kan abubuwan da aka Tsara za"a gudanar aranar.

Acikin Malamai akwai Wadanda ba musulmai ba su hudu mace Daya sai maza Uku,sauran duka mata da mazan musulmai ne Muhibba na kusa da Anty Jidda Malamar Jss2 Teacher din Su khalipa sosai suke mutumci da Muhibba tana rike da karamar yarinyarta fatima suna kiranta Batula tana Sanye da bakar abaya mai Ratsin Blue ajikinta sai tayi amfani da Blue din mayafi tayi Rolling dinsa sai glass data sanya saboda yanayin iskar garin Dayake ba amabociya kwalliya bace tana nan yadda take sai liptick data Sanya a bakinta saboda kada ya Bushe mata.
sakatariya ce ta tashi ta Rabama kowa Wata Takarda mai Dauke da Jadawalin tsare tsare da shirye shiryen da zai gudana aranar saboda kowa ya gani kuma ya karanta Muhibba ta karbi nata kuma ta Duba bayan Tsawon mintina goma d aka basu sugama Dubawa sannan Head teacher ta mike tace kowa zai iya mgana in yana da abun cewa Uncle Hafiz ne ya fara Daga hannu aka bashi Dama ya mike yayi gaisawa ga Hukumaer makaranta kafin yace"Sir na duba duba Tsare tsaren kuma komai yayi sai dai ina da wata yar shawara."
Nan da nan Director Musa yace ya fadi shawarar sa daman ai abunda yasa suka tara meeting din kenan saboda ataru abama juna shawarar da ta dace Cikin Girmamawa Uncle Hafiz yace"Sir me zai hana ayi katin gayyata na waya da printing one saboda gayyata da zamu yi zuwa ga iyayen yara da sauran manyan baki da muke ganin in suka Hallaci wannan taron zasu yabama wannan makaranta da Tsarinta gabadaya"
Yafada cikin yanayin mganarsa cikin Harshen Turanci kamar yadda kowa ya sani Director Musa ya jinjina kai yana cema Sakatariyarsa ta Rubuta abunda Hafiz yace sannan ya juyo garesa yana mai jinjina Uncle Hafiz yayi mirmishi kafin yace"Sir sai na gaba shine me zai hana shima shugabar wannan makaranta mu gayyatosa ya zama shine babban bakom mu..?
Chapter 28 · 0% Book details