Sashe 52
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya Habibu yace"Bani da abun zence Baba..Abunda Inna tace shine daidai."
Kawu yaji dadin wannan karamci Har sai da ya nuna akan Fuskar sa Cikin Bayyana jin Dadinsa yace"Nagode sosai da wannan karamcin..Allah yasa ace gwara da akayi "
Inna ta aamsa da Ameen ta Zarce da Fadin"Ai ko mallan na raye na Tabbata ka ga bazai shiga mganar Auta ba."
Kawu yace"Hakane Tabbas..Allah ya kyautata tamu."
Suka amsa da Ameen kawu ya gyara Zama yana fadin"Ina ita Autar taki..?Tazo mu yi mgana da anincewarta zan yi amfani in dai bata so yadda ban Taba yima ya"yana dana Haifa Dole ba itama bazan mata ba."
Inna tayi saurin Tare Ya Habibu dake Shirin mgana da cewa"Kada ka damu da wannan Alhaji bata nan tana gidan Habiba batajin Dadi..Sai dai na kirata munyi mgana tun ajiyan da Habibu yazo min da mganar ta kuma Amince Dari Bisa Dari."
Kawu yaji Dadi ya washe baki yana Saka albarka Ya Habibu bai ce komai ba Saboda yasan Dalilin Inna ammh yaso ta bari anemi jin ta bakin Ita Muhibba saboda gudun abun kan je kuma ya dawo.
Kawu na jin Dadin yadda al"amarin yazo da sauki yace"To ina zamu zo mu gabatar da mganar..?Ni ai na fita Daga Tsagin Ango ina tsagin Diyata."
Inna na Dariya tace"Abun ai naku ne Alhaji..Chan gaya ga ku ga iyayan nata su yaya Surajo"
Kawu yace"Madallah shikenan ma.Kai Habibu dakai za"ayi komai ko..?
Ya Habibu ya girgiza kai kafin yace"A"a Baba ina nan ni ku ne ai iyayan nata ni nawa saka albarka ne."
Kawu ya jinjina kai yana saka albarka Daganan suka cigaba da Hirar zumunci,Inna tayi kawaici bata tambayi sunan surukin nata ba Habibu kuma yaga ba Hurumin nasa bane ita kuma Inna ta Dauka Mudansiru ne shiyasa bata Damu da Tambayan karin bayani ba.
Kawu yana yin sallar azahar yayi Shirin Tafiya Inna tayi tayi ita da Ya Habubu kan ya tsaya yaci abinci yace bazai Tsaya ba yana Sauri ne Dole suka kyalesa Ya Habibu ya kaisa bakin Titi ya hau adaidaita zuwa Tasha indai zai samu Mota har cikin Garin Gaya,shi kuma Daman da Shirin Fitarsa Kawu na wucewa shima ya Hau mashin ya tafi kasuwa ya bar Inna acikin gida tana Murna Da alkawarun gari na wayewa sai tayi Sadaka.
Haka kuwa akayi washegari da Safe ta siya waina tayi Sadaka dashi Shi kan shi Habibun yasan Inna na cikin Farincikin da ya kasa Boyuwa a saman Fuskarta har Zeenatu na Tambayansa Inna daga jiya zuwa yau sai Faman Fara"a take yi shi dai bai ce komai ba yana Jira sai mgana tayi Girma sosai.
Kwana uku tsakani Baba Surajo ya Kira Inna yace kawu Sunusi yazo ya Sameshi da mganar Muhibba ammh yace Cikin Satin nan mai shiga Waliyan angon zasu zo Inna bata kawo komai ba Sanin daman yace mata shi Uban Auta ne sai ta Dauka Cikin yan"uwanasa ne na Bungudu ko kuma abokan arziki sai tace ma Baba Surajo tasan da mganar sun rabu akan in sun zo sun gana mgana zai tako har nan Zaria din..
Bangaran kawu kuwa Har Lere ya taka yaje sukayi mgana da Iya da su Baffa Hashimu Iya taji dadi matuka da kawu ya nuna shi Uban Muhibba ne Baffa Hashimu sune Uban Saifudeen daman Iya na bala"in son Taga komai an saka su akan gaba jin haka yasa tace Hashimu da Hayatu su zasu Biyama Saifudeen Sadaki Kawu na Yar dariya yace"Hajiya a Diyar tawa mai Tsada ce ko kwandala bazan yafe ba Harta kudin gaisuwar iyaye da kayan sa rana sai an kawo mana zamu bada auran nan.."
Iya cikin Fara"arta tace"ai muna jininmu jinin Saurata ne da Girma da arziki..Hashimu ku shirya komai muma Mutanen lere jinin Larabawan Sanjaha ne musan karamci da karramawa."
Kawu nata dariya suna Hira da Iya Harta Baffa Hashimu yaji kansa ya Fashe sai bayan Tafiyar kawu ne Goggo Atika ta fara kushe Abun Iya ta taka mata Burgi Cikin Fada take fadin"Ban da Tsegumi irin naki Atika Ina Laifin wannan bawan Allahn..Daya ijiye duka uzurin sa yazo mana da wannan mganar kuma ya bamu damar mu ta Dangin Uba wajen wannan yaron in yaso Tunda D'iyar Amininsa ne sai su gabatar da komai bamu sani ba yanzu kuma yazo ya bamu dama kina wata mganar banza".
Baffa Hayatu ya bude baki yace"Gaskiyan ki Iya ya karrama mu matuka muma kuma zamu rama ma kura Aniyarta."
Goggo Atika na Tura baki ta mike tana Fadin"Ai shikenan iya nayi shuru ammh ko kun ki ko kun so wannan Shigo Shigo ba zurfi ne domin ai dai ya nuna Dangin Zalihar sune masu Muhimmanci ban da haka meyasa yaki namu yaran..?
Ta karishe fada tana Ficewa Inna ta rakata da Harara tana Fadin"Ina ruwana da wata Zaliha..Ni mganar manya nake yi gemu da gemu yadda kuma ya bamu dama insha Allahu bazamu basa kunya ba."
Ita dai Goggo Atika ta fito tana kunkuni Tana Faman Tura baki Iya kuma ko ajikinta ta juya ta Fuskanci su Baffa Hashimu tana Fadin"Ku Tsara yadda za"ayi da ku da su waye zaku je chan Gaya din..?
Baffa Hashimu yace"Iya zan Biya Sadakin da kudin gaisuwa Hayatu kuma sai ya siya kayan saka Rana."
Tafiya kuma ko iya mu sai muje ammh saboda kara sai mu tafi da Baba Gambo Tunda abokin Babanmu ne da Dadewa."
Iya cikin jin Dadi tace"Hakan yayi Allah yayi muku albarka ni kuma zan baku Hatsi ku tafi dashi."
Nan dai suka zauna suna ta Tsara yadda abubuwan zasu kasance sun yanke shawaran asabar mai zuwa zasu tafi chan Gaya din ayi mgana.
Ummi ko Saifudeen balle Muhibba ba wanda yasan Wainar da ake soyawa Ko Mujaheed bai sani ba sai ana gobe zuwan su Baffa Hashimu Gaya ne kawu ya Kirasa ya shaida mai mamaki ya cikasa mamakin da bai Taba Tunani ba balle da yaji kawu na Fadin da bakin sa Saifudeen ya Fadamai yana son Muhibba zai iya Zama da ita sannan kuma da kansa yaje chan Lere da mganarta ga Dangin Mahaifinsa har kawu ya katse waya bai iya motsi ba mamakin Duniya ya Rufeshi,Saifudeen ne zai ce yana son Muhibba yarinyar da ko mgana bata taba Shiga Tsakanunsu ba How comes..?
Yasan waye Saifudeen wannan al"amarin shine abu na Farko Daga garesa da yaji ya iya nuna yana son abu uwa uba kuma har da mganar aure Mamakin yasa ko Sadiya bai yi mganar da ita ba ammh acikin Ransa ya Fara dora ayar tambaya Shin anya Ba da wata Manufa Saifudeen ya shirya hakan ba yasan shi bazai yi wani abu bai da Dalili ba,koma menene bazai tsawaita Tunani ba kuma bazai yi bakinciki ba wannan abu ne na Cigaba a wajensu gabadaya a kallah dai yana Fatan wannan auren zai zama sillar warware abubuwa da Dama game da Rayuwar abokin nashi.
Ya yi shuru da bakin sa ne yana jira yaji Daga kawu yadda al"amarin ya kasance bai samu kiran Mama zuwaira ba sai da Safiyar Lahadi tana gayamai jiya Baffanin Saifudeen sun taho Daga Lere Kawu yayi musu Rakiya zuwa gidansu Muhibba sun gabatar da neman iri kuma an basu sun bada Sadaki nan take Dubu Dari Biyu da Hamsi da Dubu hansim na gaisuwan iyaye sun kawo kwalayen minti da alewa guda goma sai Buhun Shinkafa daya da buhun masara da Buhun gero in ji Hajiya iya Kakar Saifudeen itama tana Tambayansa ne yasan da mganar..?Tunda suma sai da kawun ya Dawo yake Fada musu kuma yace Hatta Ummi ma bata sani ba.
Mujaheed mamaki ya kara kamasa Barin da mama zuwaira ke fadamai cewa an saka Lokaci Wata biyu masu zuwa bayan an kira yayan Ita Muhibban na zaria an yi mgana dashi yace a saka shi lokaci kadan Kamar yadda Inna tace shi dai ya nuna ma Mama zuwaira shima kawu ya Fadamai ba Saifudeen din ba sannan ya Fadamata kawun ma yace shi Saifudeen bai san mganar auran ba Sai yanzu in komai ya kamallah.
Sanda suke wayar da Mama zuwaira Sadiya ta shigo Bedroom dauke da Nihad data yi mata wanka ta gyarta ta Fito Tsab da ita.
Bakin gadon ta zauna har suka gama waya cikin dan abunda ta tsinta a mganarsa yasa cikin mamaki tace"Ya Mujaheed mgaar auran wa naji kuna yi..Sai naji kamar kuna ambaton sunan Hamma..!?Ummi ce ko Mama..?
Mujaheed ya sauke Numfashi yana Zaune saman gado ko tashi bai yi ba Saboda yana gida Weekend ne.
Sai da ta kara Nanata Tambayarta sannan yace mata"Eh da mama ne..Auran Saifudeen ne an saka wata Biyu."
Sadiya ta kusa Sakin D'iyarta sai da Uban ya tarota Cikin wani yanayi yana Fadin"Sadiya ki kula fa."
Sadiya ta mike a Firgice Tana Fadin"Wani Saifudeen din ?
Mujaheed na Rumgume da Nihad yace"Wanda kika sani dai."
Sadiya tayi tsaye ta kasa mgana ganin yadda tayi yasa Mujaheed ya fara mata bayanin da shima yaji a bakin kawu Sadiya ta waro ido tana Fadin"Wai kana nufin Muhibba Sister ta zaria.?
Mujaheed ya Daga mata kai yana Fadin"Eh..har an saka rana yanzu Mama ke fadamin."
Sadiya ta Daka Tsallre ta Fadomai dashi da Nihad sai da ta tashi Daga barci Cikin Farinciki take fadin"Ya mujaheed Hamma zai yi aure ya ya Ummi zataji in taji wannan Labarin..?
Sannan da Muhibba wlh sun matukar Dacewa na Dade ina ganin Dacewarsu a matsayim miji da mata..Ya Mujaheed Muhibba tayi sosai Hamma ya yi Dace."
Ta karishe Fada Cikin madaukakiyar Farimciki kafin ta mike ta Diro Daga kan gado ganin Tana Dube Dube yasa ya kalleta yana Fadin"Me kike nema..?
Cikin zumudi tace"Waya ta mana..Ni zan Fara gayama Ummi wannan albishir din"
Mujaheed ya Dakatar da ita da Sauri yana Fadin"A"a kada ki kirata bata sani ba..Ni kawu ya fadamin da Farko tace ma Saifudeen ya bar mganar tasan Halinsa shi kawun ne ya shiga mganar ki barsa da ita yace zai je har chan Abujan ya sameta su yi mgana."
Jin haka yasa sai Sadiya tayi kuma lakwas Ta koma ta zauna tana Fadin"To ammh ai shi yace yana sonta..Ai bazai saketa ba ita ko..?