← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 144

Sashe 15

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bello bai Dawo har sai da Fatima ta Haihu achan bakori Lokacin ba Waya ya Dawo ne yaga bata nan sai yaji mganar Tana Bakori abakim Hajiya Tafisu tana kuka tana fadamai batanan sanda komai ya faru sai da ta Dawo da bata ga Fatima ba ta shirya taje Bakorim Shine Babani ke Fadamata abunda ke Faruwa sai a wannan Lokacin take fadin irin Dibar albarkar dasu Firdausi ke mata Ran Bello da yayyinsa suka baci nan take suka Tasa matan nasu zuwa gida akan sai sun horu tukunna sannan gabadayansu suka tafi Bakori barka Dayake Babani ta tada mutum yazo har Gaya ya Fadi Haihuwar Fatima sun je sun iske yaron Fatima kamar Bello yayi kaki basu baro garin ba sai da yamai Huduba da sunan Habibu bayan sun Taru sunta bama Marikan Fatima da ita kanta Fatiman Hakuri da alkwarim Daukan mataki sannan suka baro garin Bello dai ya koma Sannan yayi ma Fatima duk abunda take so ita da Habibu Ranar suna kuma sai ga su Firdasu suka nuna Nadamar su suka ce Fatima ta yafe su tace ta yafe musu nan suka kwana sai Washegari suka koma gaya.

Fatima a bakori ta cigaba da jegonta babani na kula da ita,sai da tayi wata Biyu sannan Bello yaje ya Dawo da ita da kayan arziki niki niko na kayan abinci da su Dake Dake har da su Firdausi ta Dibarmawa da suka dawo Domin sun nemi gafaran mazajensu da Hajiya Tafisu har da Bello shi
ya ma Saka baki suka dawo Dakunansu.

Sanda Fatima ta Dawo ba wata matsala tana cigaba da Kula da Danta Cikin Salama da kwanciyar hankali,Hauwa ita ta rika Shige mata Sosai Firdausi ce sama sama itama Hauwan saboda abun duniya ne domin irin matan ne dake da bala'in son abun wani ko da yaushe Cikin Sammin kaza Fatima take yi ita kuma in tana dashi ta Dauka ta bata sannan tayi ta kawo mata Gulmar Firdausi Fatima dai bata bi ta kanta Domin ai Tasan Bakinsu Daya.

Habibu nada shekara Hudu a Duniya Fatima ta sake Haihuwan Mace aka saka mata suna Habiba zuwa Lokacin zamansu ya kara rikicewa Saboda Surajo ya kara aure da Amaryar mai suna Naja"atu,ita kuma Firdausi da Bala'im kishi,ballatana da suka ga Naja"atun ta kama fatima ta rike ita da ya"yanta shikenan sai suka Dawo da Halinsu na Baya,wulakanci iri iri ba wanda basa mata acikin gidan nan Don ma Naja"atu nada Baki shiyasa suke Ragama mana Hajiya Tafisu kuma basa mutumtata ballatana har tayi mgana su jita.

Azuwa lokacin duka Mazajen sun san Abunda ke Faruwa hatta kuwa da yan"uwansu mata su Barira domin suma suna gidansu ake kawo musu mganar irin abunda ke faruwa agidansu akwai wani lokacin Fatima nada Cikin Sani,Fada ya hada Naja"atu da Firdausi akan wai ita da Fatima suna shiga Daki suna gulmarta ita kuma Naja"atu tace an yi sai ta Dauki Mataki Firdausi ta saka ma Naja Hannu ita kuma tace bazata yarda ba suka Fara Fada da junansu Hauwa na gefe taki Rabawa ne fatima ce taje Rabo Firdausi ta Nausheta aciki sai da ta Fadi tana murkukusu Hajiya ma tazo zata Rabasu Firdausi ta Bangajeta ta fadi kanta ya Bugu da Randarta dake kofar Dakinta shikenan kanta ya fashe ganin haka yasa Hauwa ta zari mayafi ta ruga gidan mai garin Gaya ta sanar ma Da Barira ita tazo taga Halin da muke Ciki ta aika aka kira mata su Surajo Dayake Bello baya gari ni da Hajiya sai da aka kaimu asibiti,Fatima Allah ne ya Tsareta da Firdausi ta kasheta Mgana har Wajen maigari domin Bello yana shigowa garin aka Taresa da Labarin abunda ya faru ransa ya baci Duk da Ya Surajon ya saki Firdausin Saki Daya bai ji ya wuce ba batare da ya Fadama su Surajo ba ya Fara Neman hanyar da zai bar Gaya gabadaya Da Sunusi kadai sukayi Shawara shi yace ya Nemi mazauni a zaria saboda suna yawan kai Raguna chan da Taimakon abokan kasuwancin su na chan Zaria ya siya wani gida a Dogarawa gidan an kai linter sai dai ba"a rufesa ba ahaka sukayi Ciniki ya siya ammh sai da ya Saida gonakinsa na Gaya ya kuma Hada da Ma"ajiyarsa na asusun banki Sannan ya Fara Buga kwano da Sauran Gyare gyare ko Fatima Hakuri ya bata bai Fadamata Tsarinsa ba..

A gaya Fatima ta saae Haihuwan Sani,Kuma shine na karshe Daman Bello yayi ma kansa alkwarin Daga kan Sani Fatima bazata kara Haihuwa a cikin gidan nan ba domin ya Fita ransa kwata kwata tun balle ma Daya ga Yayansa Surajo ya Dawo da Firdausi dukcda am mata Tsakani da Fatima Sannan itama Najan an ja kunnenta sosai ita kuma Hauwa daman Zulwaje Haini ce baka gane gabanta ballatana bayanta.

Sani da na shekara Daya da wani Abu Bello ya sanar da yayyinsa mganar tashin su zasu koma Zaria duk da Habibu da Habiba sun fara zuwa makaranta anan cikin garin gaya yace duk Ciresu zai yi yan"uwansa basu ji Dadi ba Har matan kada ma Hajiya Tafisu taji Labari tana ta kuka Tana ganin kamar Laifinta ne da ta kasa zama uwar miji ga Fatima shiyasa Bello zai tashi Su kansu su Surajo sun Zargi Bello zai yi musu nisa tun ma Daya saida gonakin Daya gada guda Daya kawai ya bari wacce suka gada Dukkansu har matan sai dai yadda Bello ya Kudura ba wanda ya isa ya Hanasa Tafiya sati daya suna Shirin su Har Bakori suka je Fatima tayi ma iyayan rikonta sallama Sannan Matar
Sunusi abokin Bello da ita suka koma Zaria,sannan Tare da Naja"atu da Hauwa"u Firdausi ce bata samu zuwa ba Hatta Barira da Fa"iza da su aka koma suka ga waje masha Allah Dayake kayan sawansu kadai suka Taho dashi Saboda kada Su kwashe kayansu duka Yan"uwan Bello suga kamar in ya tafi shikenan shiyasa suka barsu a zuwan in sun zo garin anan zasu rika sauka wannan karamcin nasa yasa sai hankalinsu ya kwanta Daga baya.

Gida fa yayi sai masha Allah bayan ma Shashen Fatima akwai Fili sosai acikin gida,Ga inda Fatima zata zauna Falo da Bedroom biyu sai Dakuna Biyu Daga waje sai kitchen da Bayuka Dake waje gida ya sha Siminti da Filista fenti ne bai samu yi ba,Saboda matsalan kudi sannan ya siya musu yan kayan amfani su katifa da kayan Kitchen sai abunda ba"a rasa ba yace a Hankali komai zai Daidaita duk nan suka kwana sai washegari suka koma Gaya Cike da Labarin irin gidan da Bello ya gina.

Dawowar Fatima Zaria sai ya sa mata kwanciyar Hankali sosai ita da Bello Yanzu ya Rage Tafiye Tafiye,saboda Harkan nasu tana da yawa a garin Zaria sannan zuwa Lokacin Bello muhammadu mai gaya ya bace sai dai Bello mai rago,wattani Biyar da dawowarsu Zaria Fatima ta fara Laulayin Ciki,Sannan kuma zuwa Lokacin har saka su Habibu makarantar kudi da aka bude nan kusa dasu suna zuwa shi da Habiba.

Duk cikin ya"yan Inna ta sanar dani nafi kowa ganin gata saboda ni Tun Renon Cikina,Cikin kwanciyar Hankali Tayi shi ba Fargaban komai,Sannan kulawa wajen Mahaifinmu ba wanda bata gani ba saboda bai yawan Tafiye Tafiye haka aka Haifeni Cikin gata alokacin Inna na Labarin Mutanen Gaya duk sun zo sunana Har da Firdausi,ganin basa zama waje daya yanzu sai ta saki komai ammh kuma Naja"atu ta sanar da ita har gobe bata daina kishi da ita sannan bata daina jin Haushinn kawancensu ba,Anyi suna na gagara sannan Naci Sunan MUHIBBA.

Alokacin Babani tazo tayi sati Biyu Tana kula dani da Innata kafin ta koma Sannan Hajiya Tafisu da Su Surajo duk sun zo ganina,Da kuma ganin inda Bello suka koma suna saka albarka,Daga wannan Lokacin ne Rayuwata da duk abunda ya faru ni ya fara.

Na taso acikin gidanmu tare da Innata da kuma yan"uwana Ya Habibu da Anty Habiba sai Sani da nike bimawa Tun tasowata Nasan muna da Takun saka na Sako da Sako Tsakanina da Sani Saboda tun Haihiuwata Inna ke kirana da Auta ita da Babanmu Saboda Suna matukar ji dani shi kuma Sani sai ya rika jin Haushin su Inna sun fi sona ni kuma nayi ta masa gwalo,Sai yaji ta jin Haushi baya iya Dukana agaban su Inna sai in ba Idonsu yaci Zalina ni kuma nayi ta kuka shi kuma yana Dariya.

Kafin ni Sani aka fara sawa a makaranta Sai na zama bani da abokin wasa koda muke fada muna zama muyi wasan mu na yara koda kafin wasan tatashi mun yi fada fiye da sau Biyar arana ammh kuma muna tare to makarantar da aka sakashi yasa na koma sai ni kadai agida sai Inna ita kuma suna tafiya makaranta zata fara Kici kicin dora girkin Rana ni kuma sai na tafi Kangon nan na gidanmu inda Babammu ya fara gini bai kai Linter ba ya barshi haka,nan nake zuwa in ta tara kayan wasa ina wasa ni kadai nayi ta maganganu to inna bata Damu ba tunda kowa yasan haka yara suke in suna yara suyi wasa su kadai suna mgana kuma su kadai tun ayayin mutanen da ba ma na yanzu ba Iyaye basu cika Damuwa ba gani suke hakan wani abu ne na yara da Mutum in ya girma zai bari.

To hakan din ne wasu suna bari da sun fara girma wasu kuma in ba"ayi sa"a ba Daganan mafarin matsalarsu wacce ba"iya ganinta da ido sai ta girmama kamar yadda ya Faru dani Muhibba,SAIFUDEEN Wani suna ne da Tun ina yar shekara Uku zuwa Hudu Inna da su Baba suka sanshi abakina,Koda wani Lokaci sai in rika cema Inna Saifuddeen yazo munyi wasa a makaranta da Farko kafin asani a makaranta agidanmu muke wasa da Saifuddeen duk da ya kasance shi din Babba ne ni kuma yarinya ce karama...

In zan Shekara ina ambaton sunan Saifudden bamai tankani wani Lokacin Babanmu ne ma ke kulani yayi ta tsokana na yana fadin ina Saifuddeen din..?su basu gansa ba su yi ta Dariya suna ganin kuruciya ce sai dai Inna ta sanar dani bayan sunan Sani da sunan Saifuddeen mgana ta fara zaunamun.
Chapter 15 · 0% Book details