← Book details Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 144

Sashe 57

Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dakuwa tayi mai tana fadin"Bana son sakarci maza in ka koma kaje ka ganta kuyi mgana tunda Lokacin da aka saka bamai yawa bane sai ku Tsara yadda Bikin zai kasance.

Shi dai ta toh ya amsa mata ammh Gabansa Fadi yake kawai sai yaje gidansu kuma wajenta..?.abunda bai taba yi ba kenan ammh yasan in yayi ma Ummi gaddama sai ya raina kansa yasa ya amsa mata.

Yaso sai monday ya koma ammh Fadan Ummi yasa Lahadi ya koma Kaduna,Ita kuwa Ummi ta Kira Inna sun yi mgana har da ita Muhibba din data dawo gida,Duka sai hankalunsu ya kwanta suka samu salama kan al"aMarin
Tunda ya koma kaduna da zarar sun yi mgana da Ummi sai ta tambayesa ko yaje yaga Muhibba yace A"a ramar dai tace wlh in ta kara kiransa bai je sai tayi mai rashin mutumci daman Ummi bata zagi kololuwar Bacin ranta Dundu ko tace sai yaga Rashim mutimci yana jin haka bai da Zabi illah ya Kira Mujaheed yace Ranar asabar zasu shiga zaria Mujaheed na jin haka sai da ya shekamai da Dariya sannan yace Allah ya kaimu da yazo ya Fadama Sadiya taji Dadi tace zata basu sako su kaima Muhibba.

Mujaheed ne yace ta fada mata suna Tafe saboda yasan Gogan bai damu ba kila bai da ma lambarta..muhibba sai da ta razana da taji labarin zuwan Saifudeem adaran jumm"a ta kwashi sauri Zuwa Dakin Inna ta sanar da ita Inna ta washe baki tayi tana Fadin"Maraban sa..Sai ki gyara gida ki kuma gayama yayanki.!"
Muhibba sai ta kasa mgana ta koma Daki tana fama da faduwar gaba tana ji da ya Habibu ya dawo Inna na Fadamai sannan Anty Habiba ta kirata ta san Inna ce ta fadamata sai faman gayamata take ga yadda zatayi Da kuma abunda zatayi domin Tarbansa jin ta kawai take ita abunda ke damunta ma Dabam ta rasa da wani ido zata kallesa.."
*Janafty*
*SFD0021*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko'ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada'i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan'da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*Ki biya ki karanta cikin salama kiyi ma girman Allah in baki biya ba, kada ki karanta min littafi sannan kada ki yada'min shi don Allah pay N500 via jamila umar gtb 0552179550 ko katin waya ta wannan lambar 09069067488*
In tace tayi wani barci ta yi karya gabadaya barcin nata rabi da Rabi ne,Saboda zullumi Tun safe Anty Habiba ta kirata tana tambayanta me zata dafa na tarban bakinta tace bata sani ba sai Anty Habiba tace tayi musu Shinkafa da miya da Salad manyan mutane bakasafai suke cin abincin sosai ba,saboda sai ayi kyale kyalen zamani Suci bai burgesa ba.

Tun Asuba ta shigo Dakin tana mata Fadan kada Inna ta koma barci tatashi ta fara gyara gidan kafin Ya Habibu ya fita ya karbo mata Cefane dole ta tashi Domin in bata tashi ba Mitar Inna kadai ya isheta.

Ita ta share duka Dakunan ta goge ta saka Turaran wuta,sannan ta share Tsakar gidansu tas daman a share yake Daya ke ba yara gare su ba,Ballatana su bata sa da wuri.

Ya Habibu wani yaron makota ya bama Sako yace Muhibba ta fadi abunda za"a siyo mata ta Fada Cikin Lokaci kankani ya je kasuwa ya Dawo da Cefananta ta Zage ta fara aiki a Shashen Anty Zeenatu itama har da ita tana taya ta Daya ke tana da Aya sai tace zasu hada kunun Aya tana da Zobo data yi jiya sai su yi amfani Dashi.

Muhibba duk a Sanyaye take komai ita bai kirata ba Sadiya ce ta Fada mata bata kuma da Tabbacin zai zo din da gaske ko kafin sha daya tayi sun gama komai sun jera a Coolers,na sakawa a Frige sun saka su ta bar Anty Zeenatu na gyaran shashen nata Tunda nan Ya Habibu yace ta sauke su Da yake itama Anty Zeenatu gidan su za taje Matar yayanta ta Haihu yau suna.

Ita kuma ta koma Dakinta tayi wanka tazo ta shirya ta Dade ta gama shafa mai ammh ta kasa Shiryawa sai da Inna ta shigo ta ganta zaune tayi Tagumi Fada ta hau ta dashi yasa ta mike ta fara Laluban kayan da zata saka wata Sabuwar Atamfarta ta saka Holladan ce mai ruwan ja da baki wanda ta Dinkata kwanaki bata taba Sata ba Dinkin Riga da Sikat ne yayi ma Cif a jiki kamar an gwadata daya ke Telan Anty Habiba take bama Dinki Sosai ya iya dinki matuka ko bai gwadaki ba daya ganki sau Daya an gama mgana rigar irin mai tashin nan ne ta kasa sai abun yayi mata sha"awa balle da Kirar jikinta ya fito sosai ba tayi kwalliya ba ta dai shafa Hoda da man baki sai tayi amfani da bakin mayafi da Takalmi baki ta koma ta zauna zaman jiran Tsammani tana zaunen ne taji Wayarta na neman agaji har gabanta ya fadi sai dai tana Dubawa taga Abban Walid da Sauri ta Dauka suka gaisa Yace mata ta fito yana Kofar gida zata karbi Sako in ji yayarta ba ta yi mamaki ba sanin Anty Habiba ko da bata Fada mata ba tasan akwai abunda take shiryawa.

Daman da mayafinta ajikinta ta leka Dakin Inna tace mata zata fita waje Inna na zaune tana Dinke wani Hijabin da wuyansa ya warware so take in zataje Bakori ko gaya ta tafi dashi ta Sadakar.

Cikin mamaki ta dago tana fadin"Har sun kari so ne..?

Baki Muhibba ta karkace kafin ta Saki Labulem Dakin Inna tana Fadin"Abban walid ne Anty Habiba ta bashi Sako ya kawo min."
Daga haka ta wuce tana jin Inna na mgana bata ji me tace ba Cikin Tafiyarta na natsuwa ta fito kofar gidan yana Tsaye jikin Motarsa tana Fitowa ya Bude bayan Mota yana Fadin"Ga sakon ki in ji yayarki Auta maza kwashe sauri nake yi muna da Family meeting sai kirani suke yi na makara"
Ba musu ta Duka ta kwaso kayan Faranti ne na Roba mai Fadi guda Biyu duka an yi Rapping dinsu da foup paper,Taji kamshin Snaks kila Cake da Donut sai kuma Dayan taga maiko kila Pepe chicken ne Allah Sarki Anty Habiba sai da ta Rumguma sannan ta Dago tana mai godiya ya amsa mata da ta gaida Inna sannan ya shiga motarsa ya bar kofar gidan sannan ta Juya zata shiga gida kamar a mafarki Taji Dirin mota a bayanta tayi kokarin ta cigaba da tafiya sai taji an Bude kofofin mota an fito yasa ta dan waiwaya domin ganin su waye karaf Idanuwanta sai kan na Saifudden dake tsaye waya sakale a kunnensa ya Juya baya ta chan bangaran me zaman banza daga bakin motar jikinsa sanye cikin wata jikakkiyar Deep Blue din shadda tana maiko da yarari kansa ba Hula ya taje kansa yana kyalli hannanunsa mai cike da Gargasa ta Hango da agogon Fata baki mai kyau gabanta ya yanke ya Fadi tana kokarin juyawa ta shige gida kafin su ganta Mujaheed da kansa ke Duke yana so ya lalubo Lambar ita Muhibban da Sadiya ta basa kamar an ce ya Daga ido sai ko ya ganta tana shirin Shigewa gida da Sauri ya washe baki yana fadin"Shikenan ma ga Muhibba din nan ta fito."
Kaaraf a kunnen Saifudden da ya gama wayar da yake yi yau ba Su Bama Mujaheed yace wlh bazai zo musu da gardawansa ba,Ba domin mujaheed din zai tuko su ba da bazai amince ba saboda shi zai tukosu shiyasa sai bai damu ba.

Bai samu nasaran hada ido da ita ba, Saboda kanta ta maida kasa jikinta na rawa bata da mafita tunda sun ganta,Sai ya samu kare mata kallo Daga sama har kasa gabansa na Fadi kamar kowani lokaci kauda kansa yayi sanda Mujaheed ya karisa kusa da ita suna gaisawa Sai ya juya baya yayi kamar hankalinsa baya kansu nan kuwa kunni ya kasa yaji muryanta sau dai bai ji ba yaji dai Sanda Mujaheed yace"Man bari ta shiga ta Fada musu sai mu karisa."
Sai Lokacin ya juyo sai yaga bata a wajen kenan ta shige gida Tabe baki yayi kawai ya barsa basu wani jima a tsaye ba sai ga Ya Habibu ya fito Cikin Shirin Fita kasuwa a bakin Shashensa suka Hadu da Muhibba Dakyar ta iya Fadamai suna waje shine ya shiga ya Sanar da inna zasu fara shigowa su gaisheta ta mike tana raruman Hijabi Domin ta suturta jikinta.

Cike da Fara'a Ya Habibu ya Tarbesu shima Saifudden din yadan Saki Fuska sukayi musabaha sannan yayi musu Jagora zuwa cikin gida Kai Tsaye Dakin Inna suka fara yada Zango Saifudden kansa na kasa Tunda suka gaisa da Inna bai ko Dago ba Mujaheed ne ya fisa sakewa sai Hira suke yi da Inna Ya Habibu nan yayi musu sallama ya wuce kasuwa Shuru Shuru Inna taji shuru ba Muhibba gashi itama nauyin take ji kamar yadda ta lura Surukin nata naji shi kanshi Mujaheed din Hirar tasu ta Tsaya dukkansu sun kwantar da kai kasa bamai iya cewa komai.

Yake kawai Inna tayi tana hasaso Wauta irin na Muhibba sai ta kalle su tana Fadin"Ina ita Autar ko kun ganta ne..?

Saifudeen bai yi mgana ba ammh a ransa sai da yace Auta kuma..?Shiyasa yanayin ta ya zama mai shagwaba..
Chapter 57 · 0% Book details