Sashe 6
Saifuddeen Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Agogon Dake kafe a Dakin ya Daga kansa yana gani Lokaci ya tafi yau in bai manta ba suna da Meeting da Gwamna Saboda tun last week Sakataransa Michel ya turomai Gabadaya Jadawalin aikinsa na satin nan daya shiga.
Tashin Hankalin abunda ya tunkaraesa ne yasa ma ya manta da komai a gurguje ya shafa Lotion cikin wani irin sauri ya taje suman kansa ya shafa mayukan daya saba shafama kansa,Wardrope din dake kafe a Bangon Dakin ya nufa ya wangale sai ga suit a jere iya kallon ka iya zaban ka Kala kala na kamfanoni da Dadama masu ruwan toka da bakake.
Baki da Fari ya ciro Cikin abun da bai yi minti goma ba, ya tsuke cikin Suit baki da Fari Lokaci Daya yana kokarin matse wuyansa da Tie din Daya Dauko baki,Wajen ma"ajiyar takalmansa ya nufa gasu nan kala kala bakake da Farare da masu ruwan toka da duhuwa,Masu iya baki ya Dauko wani Rufaffe mai kama da Fatar Damisa ya saka bayan ya dawo gaban madubin yana Feshe jikinsa da Turare mai kamshi sai alokacin naga Tabon sallah a saman goshinsa sannan in ka duba sosai Wandonsa bai Sauka kasa sosai ba Har kana ma Hango bakar safar daya sanya ma Kafarsa Daga yanayin kamewarsa kai Tsaye sai ka iya kiran Saifuddeen din da Ustaz saboda yanayinsa da yanayin Shigarsa.
Komai bai Kauda ba ya fita Daga D'akin sai gashi ya bayyana a wani Falo mai Fadi da girma da Tsaruwa shima kamar ciki ne kalan Fari da Baki ne bai Tsaya ba Wayoyinsa guda Biyu da tun jiya ya zube su saman Center Table din Dake falon ya kwashe Tab dinsa tana mota chan ya barta wayoyin nasa duka suna kashe ne tun jiya da ya baro Lere ya Datse su sai wata yar karamar Kirar Samsumg daya barta a Bude saboda sako kawai itama ta wajen aiki ce Daga chan gida ba wanda yasan shi da wannan layin personal ce saboda yanayin aikinsa..
Key din motarsa ma yana Hannun Excort dinsa jiyanan a Firgice ko nace a gaggauce ya iso zaria shiyasa bakomai ya tsaya ya Duba yadda ya kamata ba Cikinsa yana ta Kiran Ciroma ammh sanin ka"idansa na rashin son Cika alkawari da kuma Sabama Dokar aikinsa yasa ya maze ko a Fuska Yunwa ko jigata bai bayyana a yanayinsa ba,da Wani irin Takun Sarsarfa ya fice Daga falon batare da yayi waige ba.
Yana fitowa wasu Samudawa dake tsare bakin kofar Falon suna Sanye da suit suma bakake da wasu manyan gilasai na ba mutumci su ka nufesa Cikin Harshen Turanci suke gaisheshi ya amsa yana mikama Daya Daga Cikinsu tarkacen kayan Hannunsa kafin ya Kallesu yadda suka natsu agabansa suna Jiran Umarni.
Motarsa ya kallah Baka Kirar prado wanda Daman da ita yaje lere duk tayi kura alamun tasha gwagwarmaya sam ya manta bai ce su kai wanki ba Dayar Motar tasa tana Gidansa na Kaduna Sauran kuma suna da Muhalli ne agidan Ummi Dake Abuja.
Megadin Dake kulamai da gidan tun da ya siyeshi ya fito da hanzari ya Rugo ya zo ya zube gabansa yana kwasansa gaisuwa Matashi ne mai jini ajika shima..
Cikin irin mganarsa ta koyaushe yace"Junaidu ka kula da gidan nankamar yadda ka saba zan koma kaduna.."
Da ido kawai yayi mgana naga Daya Daga Cikin Escort dinsa ya nufi motar ya Bude ya Dauko Kudi bandir Daya yan Dubii ya mikama Saifudeen shi kuma ya bama Megadi ya karba kamar zai mai Sujjada Saif yayi kayattacen mirmishi jin Sanda Junaidu ke fadin"Nagode Yallabai Allah ya Tsare gabanka da bayanka..Allah yasa ka gama da Mahaifiyarka Lafiya.."
Cikin Farimcikin dayake ji in akayi masa addu"an gamawa da Ummi Lafiya yace"Ameem Junaidu ka kara kayi Cefane kafin na dawo..
Bama muje.."
Yafada yana yin gaba suka bisa a baya Junaidu kuma na Durkushe kamar zai yi kwallah Saboda godiya.
Daya Daga cikin su ya Bude mai bayan Mota ya shiga,Dayan kuma ya shiga bangaran Direba,wanda kuma ya Bude mai motar ya kame agaba.
Cikin Lokaci kankani suka saki Hon junaidu ya mike jiki na rawa ya wangale bakin karkakkafan bakin get din suka Sulale suka Fice Daga gidan yana Daga musu hannu tare da Fatan alheri Domin har ga Allah bazai iya kwatatan girman Alherin Yallabai garess ba,ba domin yana masa aikin gadi ba abunda yake biyansa yafi karfin aikin da yake masa Allah dai yasa ya gama lafiya.
Sai da suka Hau shimfidad'den Titin Dake Gra sannan ya karbi wayoyinsa bai kunna ko Daya ba Tab din ya kunna kamar ana jiransa sakonnin suka Fara Tururuwan shigowa na Michel kawai ya fara Dubawa ajiyar rai ya Sauke ganin an Daga ganawar su da gwamna sai karfe goma na Safe,jin haka yasa yayi amfani da karamar wayarsa ya Tura ma parmanet Secatary Sakon dayake son ya turamai yana da Tabbacin ya nemesa bai same sa ba.
Jingina bayansa yayi a jikin kujeran motan,lokaci Daya ya Rufe Tab din batare da ya bi ta kan sauran Sakonnin Dake shigowa duk da yasan har da na bangaran karatunsa dayake yi a kasar California,Unites State University,San-Diego,California
domin samun kwarewa kan abunda ya shafi Na"ura mai kwakwalwa.
Tunani ne birjit suka shiga kansa Daya sa saida ya Dafe kansa ya gangaro da Hannunsa yana Shafa Zagayenyen Sajensa zuwa gemunsa daya Ragesa kadan bai yi yawa ba kuma sannan bai yi kadan ba.
Yasan Ummi nachan ta cika dashi Ya kuma sani ana chan ana ta Uban cigiyarsa,Mujaheed yasamu labarin yanzu sai dai ko ya nemesa bazai samesa ba sai dai in ya shiga kaduna yau,mganan su Baffa Hashimu da Iya kuma tunda ba Dukansa zasu yi ba Hakuri ne Zai shiga tsakaninsu Ummi ce babbar Damuwansa yasan Halinta kan abubuwan da suka Faru zatayi Fushi mai Tsanani dashi.
Ammh bakomai yasan Lagonta zasu gyarota Tsakaninsu ammh bazai yarda su hadu ba sai komai ya lafa zuwa Sati mai zuwa in ta koma Abuja.
Dadinsa Daya ma Addarsa Sadiya gidan mijinta zata koma Sauran yaran nan munafukai su kuma suna ganinsa ai baza su iya motsi ba,ba Raini a Tsakaninsu,sai dai su gaji da zuga Ummi bayan idonsa Daya bayyana yayi amfani da kalaman bakinsa komai zai zama kamar bai Faru ba.
Da ace yayi auran da Hakki zai hau kansa Allah ya kamasa da Rashin Sauke hakkin yar yarinyar nan ai gwara Allah yayi fushi dashi Saboda yayi Saki sannan gwara Fushin Ummi na dan Lokaci da Fushin Ubangiji,sanman gwara Fushinsu Baffa na dan Lokaci da girmam Hakki da zai Daukan ma kansa.
Shifa ahakan ma yana ganin bai yi wani Laifi ba,gwara sabama Mutum sama da Sabama Allah.
Yana kwance a bayan Mota,Sai sharara gudu suke akan Hanyar Zaria zuwa Kaduna zuciyarsa ta cunkushe waje daya babu wani karsashi ko kadan.
*******
A garin lere har alokacin Ranar Safiyar Litinin din da sukayi wayi gari Cikin wannan Alhinin,Ummi tayi kuka har bata san ina adadin hawayenta ba, Mama zuwaira da Adda Sadiya sun gaji da bata baki sun hakura ganin yadda wannan karon Lamarin Hamman yafi koyaushe Tabata abu kadan sai ta Dago kanta ta Share hawaye tana fadin"Ba dai ni yaro zai ma haka ba Zuwaira..?
Yaje bani yayi ma wa ba kansa yayi mawa..Tijaran Dangin Ubansa ne yake so yajamin kuma Burinsa ya cika Nagode..!
Sai kuma ta saka kuka Adda Sadiya da tayi Tagumi abun Duniya ya isheta tace"Ummi don Allah ki daina wannan kukan mana.
Kada jininka ya hau kin fa san baki da Ishaahiyar lafiya.."
Ummi ko Sauraranta batayi sai sharan kwallah take yi su kadai ne adakin Sadiya ta kora su Laala Dayan Bedroom din ganin zasu kara ma Ummi Damuwa.
Mama Zuwaira data fito Daga Tiolet Dake cikin Dakin Fuskarta da Ruwa alamun alwala tayi ta kalle yayar tata Da tun data koma ta zauna Saman Darduman nan bata tashi ba sai Sharan kwallah take faman yi da mganar burin yaro ya cika ya jawo mata Tozarci.
Sadiya ta koma ta kalla da Duka Damuwa ya bayyana Saman Fuskarta Allah yasa Nihad na wajensu Sauda Dayake bata ma da Rigima.
Cikin kulawa tace"Addan su Mujaheed din ya same sa..?
Sadiya ta Dago tana kallonta Cikin wani yanayi kafin tace"Mama yace duka wayoyinsa daya sani suna kashe ne..Sannan yaje Office dinsa Sakataransa ya tabbatar mai da cewa Rabon sa da Office tun Ranar Laraba sannan bai samesa a waya ba.."
Mama Zuwaira ta jinjina kai kafin ta wuce wajen wani karamin jaka ta Dauko Hijabinta tana Fadin"Uhm..Daman nasan baza"a same sa nan kusa ba.."
Sadiya tace"Ammh yace suna da Meeting da gwamna yau din da Safe kuma yana da Tabbacin zai hallata so yace min zai je office in ya gama abunda yake yi zai koma chan ya gani ko za"a dace su hadun.."
Mama zuwaira tace"Allah yasa ya bari su hadunn Addansu.."
Sadiya ta amsa da Ameen kafin tayi mgana Mama zuwaira tace"Dubamin Lokacin Walha ya tafi ne..?
Sadiya ta Duba agogon Wayarta kafin tace"A"a mama zaki iya yi yanzu goma tayi.."
Ba musu ta isa gefen yar"uwanta ta kaikata ta tada sallah bayan ta saka Dogon bakin Hijabinta kamar ana Jira Tana Tada sallah Sadiya ta jiyo Hayaniya da Sababin Iya sannan kuma Lokaci Daya da Muryan Baffa Hashimu na kwalama Ummi kira Cikin Cikakken sunanta.
"Zaliha.."
Ina zalihar take.."
Ummi ta Dago Jajayen Idanuwanta ta Sauke kan Sadiya wacce itama ta Kalleta Cikin wani yanayi kafin ta samu Zarafin mgana Ummin ta mike tana Fadin"Ga su chan sun iso..Abunda nake jira ne bari naje na same su.."
Mama zuwaira na sallah tana ta umh uhm da gyaran Murya Ummi bata Saurareta ba kafin Sadiya tayi wani yunkuri Ummi ta Fice da Dogon Hijabinta Dauke da Carbi a Hannunta Fuskarta har ta kumbura Saboda kuka.
Sadiya ta Dafe kanta daya fara sara mata,Daman tasan ai hakan zai Faru,Iya bazata yi shuru ba koda kuwa wannan karon Baffa Hashimu bai yi mgana Majeeda wajenta ta girma duk cikin jikokinta tafi sonta kamar yadda Baffa Hashimun yake Dan lele awajenta.
Bata yi kasa a gwiwa ba ta bi bayan Ummi mama zuwaira kuma sai Allah Allah take ta idar ta je Falo saboda tasan Yayar nata nachan duke Dangin Uban Saifuddeen suna kare mata Tanadin da suka saba.