Sashe 96
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Halima. Banza ya yi da ita tamkar bai ji abunda ta ce ba, don idan da sabo ya saba duk ya shigo akin sai Marwa ta yi masa wannan tambayar. Kallon Nenne ya yi tare da fa in, "Ba mu gaisa ba Saudatu. Ina yini ya Hamma Bel o? Har yanzu ba mu samu lokaci mun zanta sosai ba irin na tsakanin an uwa da an uwa. Ina son zuwa ina tsoron kada Babiyo ya fusata." "Lafiya alau, ka san iyaye dole ne a bisu a hankali ai saboda a rabu da su lafiya." Nenne ta fa Daidai nan Mama Halima ta fito daga kitchen hannunta ri e da plate in abinci. Da mamaki ta ke kallon Baffa Gi o don sam bata ji shigowar motarsa gidan ba. ama! (sannu da zuwa)" ta fa i tana kallonsa da mamaki. "Kin ganni nan ban jima da shigowa gidan ba, a waje na bar mota ma saboda fitan zan kuma yi. Dama dai 'yarki ce ba lafiya na kawo mata magani." fa in Baffa Gi Da kallo Mama Halima ta bi an matanta da ke zaune tare da fa in, "Wacece ba lafiya a cikin ku?" Girgiza kai suka shiga yi tare da ha a baki wajen fa i, "Lafiyanmu alau Mama." Sai ta mayar da dubanta gun Baffa Gi o tare da fa in, "To wacece kenan?" "Mardiyya fa na ke nufi!" ya fa i shima yana kallonta. Murmushi Mama Halima ta yi tare da fa in, "To ai wannan anwa ce ba ata ba. Kar ma ka sake wannan kuskuren don 'yata babu aure a tsakaninku. Kar ka sake atin ata aurenka." iye miyau ya yi na kunya tare da mi ewa ya ce, "To ni bari na koma wajen aiki." "Ka tsaya mana in zubo maka abinci ka ci." Mama Halima ta fa i tana kallonsa ganin yanaa ta abu tamkar mara gaskiya. Ita kuwa Nenne sai umshe dariyarta take a zuciya don ba aramin dariya Baffa Gi on ke bata ba. Yanayinsa kawai ya isa ya ya fallasa shi. "A'a saurai na ke yi, idan na dawo anjima na ci. Yanzu ma kiran da Mardiyyan ta min ne akan in kawo mata magani ya dawo da ni. Sai na dawo, Saudatu ki gaida gida." a masa kawai Nenne ta yi bayan ta kawas da kai don iris ya rage ta fashe da dariya. "To zan shiga ni ma in duba jikin nata. Allah ya ara sauki sai ka dawo." Mama Halima ta fa i tare da nufar Nenne da abincin da ke hannunta ya aje mata. "Hu'um! Wai mama ba ki lura gaba aya tamkar Baffa bai da gaskiya ba? Allah sai kame-kame ya ke yi. Wa ya sani ma ko aryar Mardiyyan ne da ta ce bata da lafiya kawai ganinsa take son yi don ta ata miki rai." fa in Marwanatu. "Oh, ni ma kashe min auren za kiyi kamar yadda kika kaso na ki auren? Shi baffan sa'anki ne? Ku tashi ku bar falon nan dukkanku ku wuce akinku." Mama Halima ta fa i fuska a aure. Gaba aya suka mi e suna turo baki tare da ficewa daga akin. Ita kuma Mama Halima ta bi su da harara. _DENMARK_ Zaune suke a falo suna kalon wani film in america, sai dai Zeenah ce kawai ke kallon. Khairat tagumi ta yi ta zuba mata idanu, don ita dai idan ba gizo idanunta suke mata ba, sai ta ga kamar tana mata kama da Mardiyya (Amaryan Baffa gi o). Sannan kuma a fizge tana yanayi da Babiyo. Amma da zarar ta tuna da labarin da Hamma Jawaad ya bata sai ta kawas da shirmen da take kawowa cikin zuciyarta. Wayarta ce ta yi ara alamar shigowar kira. A tare ita da Zeenah suka kalli wayar kamun Zeenah ta mi e ta auko wayar ta mi a mata kasancewar tana kusa da wayar ne. Da wani irin farinciki Khairat ke amsa wayar kasancewar da mahaifiyarta ta ke waya. "Haba! Sati mai zuwa? Hmm lallai, wato da yake Hamma Abdul-Hameed ne ai dole Babiyo ya ce haka." fa in Khairat tana ta e baki. Ita kuwa Zeenah tunda Aka ambaci Abdul-Hameed haka nan gabanta ya fa i raaas! Sai ta yi ta maimaita sunan cikin zuciyarta. Har Khairat ta kammala wayar Zeenah na wata duniyar daban na tunanin abunda ita kanta ta rasa ko menene. a ta Khairat ta yi, sai ta waigo a firgice tare da zubawa Khairat in idanu. Can kuma ta motsa baki tare da fa in, "Abdul-Hameed!" Da mamaki Khairat ta ke kallonta kamun ta ce, "Eh, Abdul-Hameed ne zai yi aure sati mai zuwa. Kin san shi ne?" Girgiza kai Laushi ta yi tare da fa in, "A'a ban san shi ba. Amma kuma........." sai ta yi shuru tana mai aga kai samaa kamar tana son tuna wani abu, si ta yi saurin girgiza kai tare da fa in, "Ban san shi ba." Ko kamun Khairat ta kuma cewa komai, sai ga Jawaad ya shigo auke da sallama a bakinsa. Amsawa Khairat ta yi tana kallonsa, nan da nan annurin fuskanta ya soma dusashewa ganin wani irin kallo da ya bi Zeenah da shi don sanye take da skirt wanda ya kama ta, sai riga mai hannun vest sannan kuma kanta babu ankwali, gashin kanta har kafa a sai yalli ya ke yi. "Welcome!" Zeenah ta fa i tare da auke kanta daga kallonsa tanaa mai aure fuskanta. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali tare da shafa kansa sannan ya yi kamar zai kulle idanu sai kuma ya yi saurin bu e su tare da kallon Khairat da sauri kamar wanda ya dawo cikin hankalinsa. Ganin ta yi kicin-kicin sai ya saki murmushi tare da fa in, "My girl! Ba magana ne?" ala bata ce masa ba, sai ma mi ewa da ta yi a hankali ta wuce bedroom insu. Shi kuwa sai da ya ara kallon Zeenah don sosai ta masa kyau sannan ya bi bayan Khairat da ya fahimci kamar fushi take. Yana tura ofar ya ganta zaune a bakin gado ta ha a kanta da cinyoyinta tana shasshe ar kuka. Jikinsa ne ya yi sanyi. A hankali ya taka ya isa inda take tare da aura hannu a kan kafa arta. A hankali ta zame tana mai ara sautin kukanta. Zama ya yi tare da jawo ta jikins gaba aya ya shiga fa in, "Wa ya ta a min wife ina? Fushin na menene, U'hm?" Kamar baza ta yi magana ba sai kuma ta turo baki tare da fa in, "To ba kai bane, kana shigowa ka kafe ta da idanu ko jin sannu da zuwan da nake maka ma baka ji ba. Ni dai yaushe za ta tafi?" Waro idanu ya yi tare da fa in, "Ikon Allah! Ashe ana sona haka? Ban da ke da abunki, ina dake wacece za ta burge ni kuma! Ni kin ishe ni a duniyar nan. Kuma fa wancen in matar aure ce fa, ina ni ina matar abokinaaa!" ya ja abokina in har da karyar da kai. "To ni dai gaskiya zan fa a mata kar ta sake irin wannan shigar da ta yi don gidan akwai mijin wata." ta arisa maganar har da ara turo baki. "To a dai huce, Jawaad na ki ne ke aya!" (In Allah ya yarda ba amin ba) ya fa i hakan a zuciyarsa. "To ni don Allah yaushe za ta tafi ta bar min gidana?" ta fa i tana kallonsa. Kallonta ya ri a yi kamun ya marairaice tare da fa in, "Haba one and only wife! Na riga na miki bayanin yarinyar nan. Yanzu idan na ce ta bar gidan nan ina za ta nufa da shafaffen walwa. Habaa, kar ki zobe ladanki mana. Mu ara jira ka an har ta samu lafiya kuma tunaninta ya dawo." an shuru Khairat ta yi, sai kuma can ta furta, "Allah ya bata lafiya!" "Ameen my wife," ya fa i tare da rungumeta. azu mun yi waya da mamana, ta ce min bikin Hamma Hameed sati mai zuwa, kenan mu muna nan za ai auren?" Kumatunta ya ja tare da fa in, "Albishirinki to!" "Goro fari al!" ta fa i cike da za uwa. "To kakanki ya kuma kira na azu wai mu dawo kuma kwana biyu ya bamu kacal domin isowa Nigeria saboda ai biki da mu tare da shagalin murnar Abdul-Hameed in zama ministern Abuja." Waro idanu Khairat ta yi tare da fa in, "Har an na a su ne?" Girgiza kai Babiyo ya yi tare da fa in, "A'a, amma ke ma kin san yadda Babiyo ya ke a wajen mai girma shugaban asa, to babu tantama Abdul-Hameed ya gama zama minister in Allah ya yarda." Jinjina kai Khairat ta yi cike da zumu i tare da fa in, "Can't wait to see me in my country. To wait, ya za mu yi da Zeenat?" an jim ya yi tare da fa in, "Tare za mu tafi, sai dai ni da ke ne kawai za mu san da zamanta a cikin Ar o Barkin o. Kin min al awari za ki ri e min wannan sirrin matata?" Jinjina kai Khairat ta yi tare da fa in, "In sha Allah mijinaa!" _SWEDEN_ Cike da zallar farin ciki Habib ke ha a kayansu cikin akwati, Amatul Kareem sai kallonsa take yi cike da mamaki ganin wani irin zumu i da farincikin da yake yi. "Sweetheart wannan farincikin duk na komawa Nigeria ne? Ni zan iya cewa ko daren aurenmu ban ga irin wannan farincikin a fuskanka ba wallahi." agowa ya yi ya kalleta, sai kuma ya aje jibgegiyar rigar sanyin dake hannunsa a kan gadon tare da fa in, "Baza ki gane bane, honey. Amma ni ka ai na san farincikin da nake ciki. Ni dama tamkar a kan aya nake a wannan asar wallahi. Ki sauri kar mu yi missing flight." Girgiza kai kawai Amatu ta yi tare da fita daga akin, cikinta an wata uku ya an soma turowa ka Fitarta ya saka ya fiddo waya da sauri ya shiga neman wata number ya dannawa kira, buga biyu wanda ya kira ya aga wayar. Cikin sauri Habib ya soma magana, "Kana ji na ko?