← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 140 OF 143

Sashe 140

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kin mance irin ganawar azabar da kika yiwa shi Nura tsoron mijin nakin ne don kawai Allah ya aura masa aunarki? Kin hana sa kwanciyar hankali, kin i ba shi farinciki kuma kin hana shi auro wacce za ta ba shi, kin ga kuwa kin ba shi lasisin bin matan banza. Kuma bugu da ari Zeenatu ba ita ta bi Nura ba, Nura ne ya bita har inda ta ke zama. Naka fa naka Zeenatu. Zeenatun dai ce naki ba Asma'u. Kuma ba wai ina rabaa ala arku bane don ita Asma'un ba cikin zuri'a ta bace. Itama ta riga ta shigo cikin zuri'a ta tun ranar da shaidu suka shaida aurenta da jikana. Kuma kar ki manta ni da kaina na za o masa ita matsayin mata saboda sanin wanene mahaifinta. Mutun ne na gari sosai." "Ki yafe min duk abunda na miki 'yar uwataaaa!" Marwanatu ta fa i bayan ta fa a jikin Zeenah ta rungume tare da fashewa da kuka. Itama Zeenatun kuka ta ke yi tare da fa in, "Ni ma ki yafe min 'yar uwata!" arfaffiyar ajiyar zuciya Babiyo ya sauke yana mai jin kamar ya sauke wani babban nauyi da ke kansa. Burinsa kamun ya bar duniya shine ha uwar kan zuri'arsa kaf. "Allah ya maku albarka tare da zuri'arku. Nagode sosai da ku ka ban ha in kai na gyara tsakaninku. Ke kuma Marwanatu zan kiya duk wa a kika lissafo min da suke in yi miki magana na yi magana da su. Shi kuma His Excellency zai zo ya same ni sai na ji dalilinsa na hana ki shiga Villa. Idan ya kama na mammaka masa sanda ma zan yi." Dukkansu sai da suka dara sannan suka mi e hannunsu ri e dana juna sannan suka fice daga akin. A ranar dai Mama Hafsat mahaifiyar Zeenah in bari ta yi su tafi da Meema a gidanta ta kwana. A cewarta gobe idan Abdul-Hameed ya zo shi da matarsa kamar yadda Babiyo ya ce sa tafi amma yau dai tare za ta kwana da jikarta. Shi ma baffa alerin hakan ya ce. Su Muhaysim ma sai suka buga tsalle suka ce suma can gidan za su kwana domin ba su gaji da ganin Addarsu ba. Daren ranar Zeenah bacci ta yi ita da Abdul-Hameed mai cike da farinciki da annashuwa. Sun raba dare suna hira da soyayya kamun su kai bacci. Washa gari da daddare kuma ya tasa Asma'u da ya ke matu ar jin haushinta a gaba su ka tafi Ar o Barkin Gaba ayansu suka natsu gaban Babiyo barin ma Asma'u da jikinta ke rawa da kuma acin ran abunda Babiyo ke fa i a kanta. "Ban sa mijinki ya kawo nan don komai ba son don in miki nasiha tare da jan kunnanki don kema tamkar jikata haka na ke kallonki ba sirikar gidan nan ba. Ina sane da duk abunda ki ke aikatawa. Sai dai ina so ki sani, idan ki ka yi abunda zai zubar da ima da mutuncin mijinki ba shi ka ai kika tozarta ba har da ke in nann domin duk inda kika shiga za a ce ga matarsa can. Ki daina bari shai an da tsokar da ke cikin irjinki suna cin galaba a kanki saboda kishi. Na san kece kika sa aka fitar da zancen nan a gidan radio sannan kuma kika kuma fitowa gaban an jarida ki ka aryata. To na baki uzuri a wancan, amma idan kika kuskura kika kuma yin wani abu da zai atawa zuri'ata da gidana suna, to a wannan karon zan auki mummunar mataki a kanki kuma baza ki ji da i ba. Sam albasa ba tai halin ruwa ba domin iyayanki mutanan kirki ne ainun. Saboda haka ki kiyaye. Kai kuma (ya mayar da maganar a kan Abdul-Hameed) ka ji tsoron Allah ka kwatanta adalci a gidanka. Kar ka yarda ka kasance cikin mazan da Allah zai tashe su ranar gobe arin jikinsa aya a shanye. Ka bawa kowacce ha inta, kar ka kuskura ka fifita soyayyar wata a gaban wata. Wannan shine iya maganar da na kira na yi muku. Allah ya sa ya shiga kunnunwanku." "In sha Allah!" Abdul-Hameed ya fa i yana zunguran Asma'u da afa domin ita ma ta furta wani abun. Da yar ta iya bu e baki ta ce, "Mun gode Babiyo." a kansa ya yi tare da fa in, "Allah ya muku albarka, ku tashi ku tafi dare na yi." Tare su ka mi e suka fita zuwa tsakar gidan, da sauri bodyguard suka bu e musu mota suka shiga. Gidan Mama Hafsat suka fara isa su ka auki su Meema sannan suka wuce gida. Asma'u tamkar za tai bindiga tsabar yadda maganganun Babiyo ya soki zuciyarta. Sai dai ta san ko giyar wake ta sha bata isa ta ara yun urin yin wani shirme a media ba don ta san tabbas Babiyo zai iya sakawa ai mata checking out. Yau ba a akin Zeenatu yake ba, sosai ya ciji yatsa don ya san za a sha hira babu shi, amma gudun shiga hakkin Asma'u kamar yadda Babiyo ya tunasar da shi, karfe goma saura ya yi masu sallama ya haura akin Asma'u. Washa garin ranar tun sha aya aunty Ladi Katifa ta iso gidan jikinta har rawa ya ke. Tana arba da Meema ta fashe da kuka tare da rungume. "Meemata ke ce kika girma hakaa? Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un Allah ka tsinewa Yasaar da Sabo da kaza!" ta kuma fashewa da kuka. Meeman ma kukan ta ke yi sosai har da shasshe a kamun ta ce, "Aunty Ladi......" Rufe mata baki ta yi tare da fa in, "Aunty Ru ayya, no more aunty Ladi har abada kin ji Daughterna." a kai ta yi tare da fa in, "Aunty Ru ayya ina aunty Salma nice?" "Ban san inda Salmanu ya ke ba. Tun ranar da aka raba mu da ke shi ma bamu ara ganinsa ba. Amma ina fatan yana cikin oshin lafiya da kwanciyar hankali." "Ameen" Meemah ta amsa. Daga nan kuma hira ya alle tsakaninsu a can falon Zeenatu. Sun yi kuka tamkar idanunsu zai tsiyaye. Musamman da ta ji wai Meema ta yi auren coci don har hotonta da Leo ranar aurin auren sai da ta nuna masu. Nan su kai mata nasiha tare da nuna mata illar abunda ta aikata da kuma arin cire mata Leo in a ranta. Ita Zeena ma tun a daren jiya ta fakaici Meema ta auke wayar tda ta dawo dashi daga colombia ta cire sim in ta kakkarya don kar ta kwashi numbers in da ke ciki ta kira Leo ta allo masu aiki. Don a yadda Meeman ta ba su labarin Leonardo in zai iya aikata komai a kanta. Sannan kuma ta cire zoben da ya saka mata ta yi flushing insa. _3 months later_ Meema hausa ya an fara zama a bakinta duk da dai ba iyawa ta yi ba. Don namiji mace ta ke mayar dashi, mace kuma namiji. Haka ma angaren koyarwar karatun addini, Aizaad ne ya kawo masu wani malamin da ke koya mata har gida kuma Alhamdulillah tana fahimtar komai. Akwai sha uwa sosai tsakanin su da Aizaad sosai duk da bai fito fili ya fa a mata ba saboda soyayyar da ya fahimci ta fa a da wani ma'aikaci a wani babban super market. Wani rakiya da ya ta a mata domin sayo mayukanta ne suka ha u, shikuma ya gwada yana son ta har su kai musayar number. Wata biyu kenan da ha uwarsu da Hamza, sai dai bataa ta a yadda ta fa a masa ita iyar shugaban asa bace don acewarta tana son ta auri wanda zai aunace ta a yadda ta ke ba don matsayin mahaifin ta ba. Duk lokacin da za su ha u a gidan aunty Marwanatu su ke ha uwa. Yayin da shi kuma ta ke jira wani lokaci domin bayyana masa ko ita wacece. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, ranaku suna ta wucewa haka satuttuka da watanni. A yanzu watannin Meema takwas da dawowa cikin zuri'arta. Komai yana tafiya mata daidai a rayuwa. angaren Aizaad kuma yana nan ma ale da soyayyarta a cikin zuciyarsa sai dai ya yi al awarin burne halan a zuciyarsa domin farincikin Meema shine farincikinsa. Kwatsam wata rana Meema na zaune a kan kujera tana yankan farce wayar ya yi ringing. Dubawa ta yi sai taga masoyinta Hamza ke mata waya, cike da farinciki ta auki wayar ta kara a kunne tare da rera sallama. Sai dai abunda ta ji Hamza na fa i ne ya saka ta mi e tsaye dafe da irji sannann ta zazzaro idanu. "Kana ina? Don Allah ka zo mu ha u a gidan auntyna. Zan maka bayanin ta yadda za ka fahimta. Wallahi ba da niyyar yaudara na yi hakan ba sam!" it ya kashe wayarsa ba tare da arisa sauraranta ba. Da sauri ta nufi hanyar akinta ta canza kaya sharp-sharp cikin doguwar rigar abaya tare da na e kanta da gyalen don dama sune shiganta don yawanci kayan nata abaya ce. akin Zeenah ta tafi ta shaida mata za ta je gidan aunty Marwanatu amma baza ta jima ba. Sai Zeenah tai mata Allah ya kiyaye ita kuma ta fito ta shiga mota driver da ja kariyarta suka mata rakiya har gidan aunty Marwanatun da bama ta gida ta je aikin amma ta kusa dawowa. Har aunty Marwanatun ta dawo amma Hamza ya i zuwa gidan. Da yar da su in goshi ya zo bayan la'asar yana cika yana batsewa. Da kuka ta isa gabansa inda ya kr tsaye har e da hannun wayarsa a gaban aljihu camera na saita tahowarta. Kuma dama ya yi hakane domin ya auki duk wani abu da za su tattauna tsakaninsu. "Ka saurare ni Hamza in maka bayani. Wallahi ba niyyata in yaudare ka ba. Na yi hakane domin ka soni a matsayin yar kowa ba 'yar shugaban asa ba." Wani kallon banza ya watsa mata tare da fa in, "...Tir! In ha a iri da ke. Ni salihin bawa ne da bai ta a kusantar zina ba. Don haka ba zai ta a yiwuwa ba in auri iyar da ta kwanta
Chapter 140 · 0% Book details