Sashe 135
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baffa. *_VILLA_* Tana saukowa daga kan gado ta mufi wajen madubi ta gyara fuskanta kasancewar ta yi wanka. Role on mai matu ar tsada ta shafa sannan ta fesa bodyspray ka an saboda fita za su yi. Gaban closet inta ta zaro wata asheshiyar less kalar fari mai ratsin dark green. inki doguwar riga ce ta ji stone work tun daga asa har sama. Bayan ta gama sakawa sai ta kalli kanta a madubi tare da sakin murmushi don fitowa ta yi tamkar wata yarinyar yar 25 bayan kuma shekarunta na haihuwa 41 ne cif, don ko Meema a yanzu shekarunta 24 da haihuwa. Gyale babba ta auko dark green ta yafa, haka takalminta ma dark green ne mai ma matsakaicin tudu na kamfanin Calvin Klein. ofa ta nufa ta bu e tare da soma saukowa zuwa asa daidai lokacin da His Excellency ke haurowa zuwa akinta. Cak ya tsaya yana kallonta don ba aramin kyau ta yi masa ba sosai. Wani murmushi ta sakar masa da ya kusan tsayar da bugun numfashinsa, ji ya yi kamar iska ta auke shi don kawai ganinsa ya yi a gabanta ya ri o hannunsa yanaa kallon wayar idanunta. "A kullum ara kyau da zama very young kamar 'yar sha takwas kike yi a wajena wallahi. You look very very pretty Zee-meed." Wani juya idanu ta yi (irin na 'yan bariki ) tare da furta, "Really?" "Goodness! Allah kwalliyar nan za ta aci yanzun nan. Kin san fa ni ban sanya wajen kashe arna." ya fa i yana mai jawo ta jikinsa sosai. "Don Allah ka yi ha uri kar ka ata min kwalliyata!" ta fa i da wani salo na shagwa a da ya kusan zautar da tunanin His Excellency. "I need water!" ya fa i yana kama ma ogwaransa har da an tarinsa. Hannunsa ta kama suka koma bedroom inta. aramin fridge in da ke akin ta bu e ta fiddo bottle wata ta bu e tare da kaiwa bakinta ta gumtsa sannan ta matsa daf da shi ta karkato da kansa ta juye masa ruwan kaf a bakinsa ya shanye. Kuma dama ta san abunda ya ke so kenan shiyasa ya ce he need water. Sai goran ruwan ya yi rabi sannan ta rufe tare da fa in, "Na san dai ka oshi!" Marairaicewa ya yi tare da fa in, "Ina son ari." Lakuce masa hanci ta yi tare da zame suit in jikinsa ta tayasa unbottuning shirt insa ta cire. "Malama ba wanka zan yi ba, kaya kawai zan canza don ni kaina a age nake na son nuna miki wannann tukuicin." "Ni ma haka Lovey-Dovey, amma ban san mai yasa irjina ke bugawa ba." ta fa i a marairaice. Kunnensa ya aura a irjin tare da fa in, "Kai! Saurara ka daina agawa matata hankali. Abun alkhairi da farinciki za ta gani a yau innan." yana gama fa in haka ya ago ya kalleta yana nuna mata closet da idanu. Wajen ta nufa tare da auko masa shaddarsa fara al sai mai o take yi ta ji inki mai aukar idanu. Ita ta taimaka masa ya saka sannan har links sannan ya kallesa tare da janta zuwa wajen mirror ya yi masu hoton nan da ake yi ta gaban mirror da tsadaddiyar iphone insa. Ba aramin kyau su kai ba. Sai suka fito tamkar wasu yara. "Ina su Muhaysim?" ya fa i yana saka takalminsa half cover farare "Suna Barkin o Estate wajen mama (tana nufin mahaifiyarta)." a kai ya yi tare da fa in, "Mu ma Barkin o za mu je yanzu ai!" Rass! Gabanta ya kuma bugawa da arfi amma kuma bata ce komai ba kuma ta yi arin calming kanta don kar ya fahimci halin da take ciki. Tare suka jero suka sauko har babban falon da ke asa wanda a nan inne za ka bi hanyar corridor in da zai kai ka sama sashen Queen Elizabeth wato the only first Lady of Mr President. "Wait for me here, will be back in lessthan 10minutes." ya fa i yana shafa kumatunta. a masa kai ta yi tare da masa murmushi shi kuma ya nufi hanyar da za ta sada shi da akin Hajiya Asma'u uwargida a wajen His Excellency. Knockin ya yi a ofar akinta sannan ya har e hannu yana jiran ta zo ta bu e masa ofa. Sai da ta kwashi mintuna biyar yana tsaye sannan ta taho ta bu e a yangance. Ta ci uban kwalliya cikin arniyar shadda alar maroon da ya sha inkin kece raini. aurin walin nan ya zauna a kanta as kana iya hango gashin dokin da ta saka daga ta eyarta wanda ta yi parking insa da ribbon. "You're highly welcome your Excellency!" ta fa i tana murmushi tare da masa kallon asa- asa don ba aramin kyau ya yi mata ba, take lokaci guda wani irin kishi ya turni eta tamkar zuciyarta za tai bindiga. Danne zuciyarsa ya yi ya shiga akin saboda wani irin haushi da takaicinta da ya ke ji. Mutunci da girman mahaifinta da ya ke gani ne ya hana shi sakinta tuntuni. Amma wannan karan ta yi crossing limit inta shiyasa ya ke son furnishing inta to the extent da sai ta tsuguna tana ro onsa ya sake ta ta tafi gidan ubanta. "Na ganki cikin shiri har da gyale, ina zuwa haka da yamman nan?" ya fa i yana are mata kallo. inkin skirt da riga ta yiwa shaddar kuma ya kamata sosai duk da siririya ce tamkar za ta alle. Gashi ta saka rigar mama irin push up innan, fuskan nan tasha uban make-up kamar za ta gasar kyau. Murmushi ta yi a yangance tare da fa in, "School zan shiga. Ina da class amma test kawai zan basu in kar i attendance in dawo gida. Don ina son mu tattauna game da wancen tsinanna gidan redio da suka fitar da zancen aryar nan tare da ambatan sunana don kawai su ga sun ture gwamnatina a wajenka babu kuma aryansu don ni da kai till death apart us." "Hakan na da kyau! Sai dai ni ban da lokacin jin shashanci magana akan gidan redio. Ki tabbatar magrib a gidana ta miki, zan fita zuwa Family house yanzu!" ya fa i yana kallon agogon hannunsa. Wani irin duum tamkar saukar aradu maganarsa ta yi mata. Dom tun da suke bai ta a bata lokacin da za ta dawo gida ba idan za ta fita ba sai yau. Sai ta ji duk ta muzanta tamkar a idanun duniya ta fa i haka. Ita fa ko fitar ba fa a masa take ba sai dai ta fice tare da convoy tana feeling ita matar shugaban asa. Tana daga cikin matantan masu nuna Feminism a cikin gidansu. Ji take da ita da mijin aya suke. Bata ta a girka masa ko ruwan tea ba bare kuma abinci, gaisuwa idan bai gaisheta ba bai isa ita ta bu e baki ta gaida shi ba. Wani irin girman kai da tsantsan jahilci ke damunta. Kuma ba dai don bata samun tarbiyya ba, daidai gwargwado iyayanta sun bata, sai dai ita in rayuwar turawa da al'adunsu ta aurawa kanta. "What did you mean, your Excellency? Yau ni ce ka ke baiwa lokacin da zan dawo gidan nan kamar wata 'yarka? No no no no.. Don even start that bullshit!. Yaushe mu ka fara hakan da kai? Ni na ta a tambayanka ina za ka je, yaushe za ka dawo ko kuma daga ina ka ke? Babu wanda zai takura min wallahi! Idan ita (tana nufin Zeenah) ta zauna kana juya ta sabida bata san ciwon kanta ba ko kuma tana tsoran saki sabida ta san ba wanda zai auri ragowar azaman Lagos ni ba zan......." Wani ha an marin da ya auke ta da shi ne ya hana ta arisa sauran maganar da ya ma ale mata sakamakon gigicewar da ta yi. Da hannu ya nuna ta tare da fa in, "Sau aya tak idan azamin bakinki ya kuma zagar min uwar 'ya'yana sai na miki shegen duka na kora ki gidan ubanki. Wawuya sakarya!" Ja da baya ta yi gabanta na fa uwa saboda yadda idanunsa suka sauya tamkar na zaki ga su sun canza launi zuwa jajur har mai o-mai on suka yi alamar zallar acin ran da ya ke ciki. A cikin zuciya ta ri urawa Zeenah da shi kansa Abdul-Hameed in zagi tana ayyana irin rashin mutunci da tozarci da za ta yi masu su duka biyun na aukar fansa yatsunsa biyar da ya aura a fuskanta da kuma gorin rashin haihuwar da ya mata a kaikaice. "Ni ka ke gorantawa akan rashin haihuwa Abdul-Hameed?" ta fa i tana mai fashewa da matsanaicin kukan makirci. "An miki gorin ki yadda za ki yi! Kin haihu inne? Ke Allah ne ya rufa miki asiri ma da bai baki haihuwar ba don ba aramin sakaryar uwa za ayi ba. Don baki da tarbiyar da za ki iya ba wani." ya fa i a hasale. "Eh! Shiyasa naga ita 'yar gwal in taka da tana tafiya tarbiya na zuwa ta haihu a gidan karuwai, an daudu ya yiwa yarinyar wanka tare d hu uba ya ra a mata suna ta kuma tashi a gidan karuwai tanaa kallon yadda maza ke kwanciya da mahaifiyarta a gabanta tare da shaye-shaye da sai da miyagun wayoyi. Duk cikin tarbiyar ce ai!" "Asma'uuuu!" ya fa i da arfi tare dasha ar wuyarta ya ha a da bango tamkar zai kasheta. Sai zazzare idanu ta ke yi tana arin janye hannunsa amma ta kasa sabida arfin ba aya ba. Sosai ta yi matu ar tsorata don ta sadakar kasheta Mr President zai yi. "Zan iya kashe ki a nan akin kuma in binne gawarki babu abunda zai faru! Wallahi tallahi wa billahil azim idan bakinki ya kuma fa in mummunar kalma a kan matata sai kin yi dana sanin haihuwarki da uwarki ta yi. Banza 'yar iskar mata!" ya arisa maganar tare da cilli da ita asa sannan ya taka afarta ya fito daga akin yana huci. Kallo aya Zeenah ta masa ta fahimci yana cikin acin rai mai tsanani don yana isowa inda ta ke hamnunta kawai ya kama bayan