Sashe 44
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ya ara da fa in zai ro i Baffa Modibbo ya sassauta mata. Yana fitowa ya kai wa Baffa Modibbo key in sannan ya nufi wajan wayarsa ya auka ya fice daga parlourn kasancewar kowa ya bar parlourn har Baffa. Sai da ya fita gate sannan ya lalubo Number in Maman Meema ya kira. Jin wayar ta i shiga sai ya mayar da akalar kiran zuwa Number in Katifa. ```The Number you're trying to call does not exist, please check the number and try again.``` Wani murmushin kun raina min wayau ya yi tare da furta, "You must be joking, MTN!" Tare da sake kiran layin. Wannan karan mamaki ne ya kama shi sosai jin abunda suka sake maimaitawa. "Ke! Tataya? Ko sake Number ta yi ne?" Ya watsowa kansa tambayoyin da bai da amsar su. Bai ha ura ba ya dunga kiran layin kamar zararre but still the same abunda MTN suke ce masa kenan. Sai ya koma idan ya kira layin Laushi, sai ya mayar da kiran zuwa layin Ladi Katifa har sha ayan dare amma babu labari. Haka nan ya ja sakakken guiwarsa ya koma ciki da niyyar gobe da sassafe ya sake kira, idan bai shiga ba, sai ya bazama nema da kansa. Daren ranar barcinsa ragagge ne don duk juyi sai ya yi tsaki. Idan kuma ya farka sai ya jawo wayarsa ya kuma danna kiran duka layukan biyu amma still bai shiga. Jawaad na jin duk wani motsinsa amma ya yi kamar bai san da ruwansa a akin ba. Sosai daren ya yiwa Habib nisa don osawa ya yi gari ya waye, sai dai bai san Jawaad in ya shuka masa tsiya ba tun jiya. Don tuni ya yankar masu tikitin jirgi, karfe takwas jirginsu zai tashi daga Lagos zuwa Abuja. Kuma ya sanar da Baffa Modibbo bayan ya shirya masa aryan Baffa Chuba o ya ce goma ta musu a Abuja saboda meeting in da za ayi da na family a gidan Babiyo. Hakan ya sa Baffa Modibbo ya ce da kansa zai kai su airport in gobe. Washa gari kuwa, tun bakwai da an mintuna Baffa ya azalzala masu da su fito akwai nisa daga nan inda suke zuwa airport. Mamaki ne ya kama Habibu sosai ya shiga tambayar Jawaad mai za suyi da sassafen nan a airport. "Mai zai hana ka fita ka tambaye sa da kanka!" Jawaad in ya fa i yana gyara zaman belt in wandonsa. "Na ro a da girman Allah ka fa a min mana Jawaad," ya fa i da damuwa a fuskansa ganin Jawaad in na gyara akwatinsa. "To, Baffa Chuba o ne ya yi kiran gaggawa a kan goma ta yi mana a Abuja saboda meeting in da za ayi a gidan Babiyo. Hakan ya saka zai aje mu a airport." Ragwajab Habib ya zauna a bakin gadon tare da ri e kai don har ga Allah ya so zuwa ganin Laushi yau in nan domin ya shaida mata sirrin zuciyarsa kamun ya tafi ya in amincewa daga familynsa. Kuma yasan cewa aryansa ya i amsa kiran Babiyo. "Wai jiran uban mi kuke haka? Tare za mu tafi fa. Don yanzun nan Gi o ya kira ni a waya ya shaida m in taron kuma ni ma ana son gani na a can in." Fa in Baffa Modibbo. Da sauri Habib ya mi e, don Jawaad har ya kai ofa. Akwatinsa ya ja suka nufi akin Inna arama wacce da ita za ai tafiyar. Umma da su Marwanat kawai za a bari a gidan. "Ai mu tafi kawai ma gaisa a cikin mota, jirgi bai jira sai dai a jira shi," fa in Inna arama tare da bin bayansu. angaren Laushi kuwa, wannan amshi ya tsaya mata a rai sosai. Duk mintuna sai ta ji gabanta na fa uwa. Hakan ya saka gaba aya ta kasance suku-suku. Meema kuwa ko da wasa bata fa a mata zuwan Jawaad Huzaifa Kaita gidan ba don ya gargadeta da hakan. A daren ranar Sabo da Kaza ya mata waya tare da shaida mata anjima da daddare za a kawo kaya ta sallami kowa a gidan ya kasance daga ita sai arta. Hakan kuwa aka yi. Ladi Katifa da Salma nice suka tafi gidan Hajja Lanti. Salma ya kwana a akin Sadiya an daudu, Katifa kuwa a daren customer ya zo ta tafi kwana gida. Da daddare wasu maza kusan su goma gaba aya fuskokinsu a rufe suka shigo gidan tare da manya-manyan makawai, Cocaines, tabar wiwi da kuma kwayoyi. Sai da suka jera komai a wannan akin da tun tarewarsu a rufe yake. A gaban Laushi su kai komai sannan suka jawo akin suka rufe. *_Abuja_* Estate ne guda mai suna *_Ar o Barkindo Family_*. A cikin wannan estate wanda ya kasance unguwa guda, akwai gidaje sama da ari biyu. Kowani layi yana da sunansa. Akwai irinsu; Gi o Street, aleri Street, Gaab o Street, Barkin o Street, Modibbo street, Bel o Street da sauran su. Ko wani sunan layi, mai sunanne da iyalansa a cikin gida. Kuma gaba aya an uwan juna ne don an mutum aya ne wato Ar o Barkindo. Ko wani gida a estate in irin tsarin gininsa aya ya ke da na an uwansa. Suna da wani irin abilanci da nuna soyayya ga na su kawai. Su in idanu ne wanda basu san ba o (ma'ana bare) a cikinsu. Fararene sol, asalin Fulanin Yola. Wani atoton gida wanda shi ka ai ya fita daban da sauran gidajan cikin estate in saboda ya fi kowani gida tsaruwa a ciki. Gidan ne tamkar gidan wani hamsha in sarki ko kuma bafullace. Motoci ne a harabar gidan nan wanda yawansu ya fi gaban a irga su kowanne na wane wannan. A cikin wani mahaukacin parlourn mai matu ar girma kamar fada, mutane da za su kai hamsin a ciki kuma duk maza kuma dattijawa. Sai wani tsohon farin sol in bafullace wanda zai iya kaiwa tamanin da oriya zaune a kan wata kujera irin ta sarauta hannunsa ri e da wata kyakkyawar farar sanda a hannunsa. Gefensa a kan irin kujerar da yake zaune, wata farar kyakkyawar farar tsohuwar bafulatana ce mai isa da ta ama itama. Tsohon nan yana da masifar kwarjini domin da wuya ka iya kallon cikin idanunsa ka masa magana. Wasu ma cewa suke idan ko da tsautsayi suka kalli idanunsa gani suke ya koma kamar idanun zaki. Kallo aya za kaiwa yanayin zamansa ka fahimci yana cikin matsanaicin fushi. Don shi ba ka isa ka kalli fuskansa ka fa i yanda yake ba. Sai da ka fahimta a yanayin zama ko kuma gyaran muryansa. o Barkindo kenan wanda wasu daga jikin ansa da jikokinsa suke kira Mamiyo wasu kuma su ce masa Babiyo. Kowa daga cikin akin nan gabansa bugun uku-uku ya ke suna fatan Allah yasa ba aya daga cikin ansu ko jikokinsa bane ya tafka wani babban laifin da yasa a kai masu wannan kiran gaggawan. Da wani irin asaita da isa Babiyo ya ago ya zubawa ansa da wasu daga cikin jikokinsa idanu tare da fa in, "A bu e taro da addu'a!" Nan da nan aka bu e taron da addu'a mai an tsayi saboda irin addu'ar da Babiyon ke bu ata kenan. Gyaran murya ya yi wanda ya saka cikkuna mutanen da ke zaune a wajan da yawa ya ka "Modibbo!" Babiyo yai kiran sunan Baffa Modibbon da tun da muryan Babiyo ya sauka a kunnansa ya ada har ji ya ke kamar zai zagaya. "Na'am Babiyo!" Ya amsa har da rusunar da kai jikinsa na rawa. "Zaman barikin ne ya saka ka kasa baiwa arka cikakkiyar tarbiya har ta iya taka afa ta tafi gidan karuwa? Sannan kuma ta nai mi kashe mijinta da wu a ta hanyar caka masa a ciki ko?" Wani irin zufa ce ta shiga kwaranyowa daga goshin Baffa Modibbo, gashi babu damar musu bare kare kai. Idan kuma ka yi shuru babu amsa haka yana nufin tsantsan nuna rashin biyayya ne ga shi Babiyon. "Ai min aikin gafara, Babiyo!" Ya fa i still kansa na asa. afa Babiyo ya yi tare da rausayar da kai ya mayar da kallonsa izuwa kan Baffa Gi o ya ce, "Mai Habibu ya ke jira har yanzu ba a tsayar da ranar bikinsu da Amatul kareem ba? Ko kuma yawon bin karuwa ya fiye masa auren ne?" Lokaci guda zuciyar Habib da ke kusa da Jawaad ya yi wani irin tsinkewa ya fa i. Duk da yasan kakan nasa da bin wafi da bincike, bai ta a tunanin zai binciko har ya gano yana bin mata ba. Don bai ta a yarda ya nai mi mace a garin Abuja ba. Baffa Gi o kuwa jin abunda Babiyo ya fa i game da halin da Habibu in ya jefa kansa, sai da aramin fitsari ya kufce masa don ya san dole Babiyo ya yi hukunci a kan haka kuma hakan na nufin shi ma ta shafe sa. "Babiyo duk abunda ka ce shine daidai. Ai hukuncinka kawai muke jira na yanke ranar auren tsakaninsa da Amatul kareem in. Sannan don Allah ina neman alfarmar ai min afuwa kar a hukuntani akan mummunar ta'addancin da Habibu ya ke aikawa, sam babu hannuna a ciki." Wani ajiyar zuciya akin suka aje don sun san Baffa Gi o ya taro match babu kwallon bugawa saboda sam Babiyo bai lamuntar ya yi magana ka nemi kare kanka don ya fi ka sanin kana da hannu a laifi ko babu. Ajiyar zuciyar da an uwansa su kai ne ya dawo dashi hayyacinsa a kan ta argazar da ya yi. "Kai kuma Bobbo, ba ka isa da anka Jawaad bane da har yanzu ka zuba masa idanu ya kasa fidda matar aure?" Babiyo ya fa i zuciyarsa na tafarsa da abunda Habibu ya ke aikawa na atawa suna gidansa da kuma abunda mahaifin Habibun ya aikata yanzu na kare kansa da ya yi. Don a wajan Babiyo ka kare kanka a gabansa daidai ya ke da ka kira sa mara adalci. "In Sha Allah yau in nan zai fidda matar aure sai a ha a da bikin Habib in duka." Fa in mahaifin Jawaad. "Hakan na da kyau!" Babiyo ya fa