← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 143

Sashe 106

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga aryan da ya dage ya shararo mata tamkar wannan ranar baza ta zo ba. "Gaskiya ban yi dabara ba sam! Da na san wannan ranar za ta zo da wuri haka da wallahi ban shirga miki wannan aryar ba. Gashi nan dai yanzu duk girma ya fa i." Duk a cikin zuciya ya yi maganar. Ya kusan mintuna talatin a haka bai iya ce mata komai ba, ita kuwa Khairat wani irin ba in ciki ne ya mamaye zuciyarta da kuma mugun haushinsa da ya ninku a zuciyarta ganin kamar bata ma kai ya bata ha uri ba da yi mata magana masu kwantar da hankali ko da kuwa aryar zai kuma shirga mata. (Fisabilillah mu fa mata muna aunar lallashi da magana mai da i. Muna da wani irin raunanniyar zuciyar da duk iya girman acin ranmu da an tarairaiye mu an nuna mana so da auna, musammam ma namiji ya an yi wallar nan sai mu ji duk fa in duniya babu kamar mu. Nan da nan dai zuciyarmu ta narke tamkar kitse a wuta. Haba maza, ku gane mana! Shi kuwa Jawaad mi ewa ya yi ya nufi bayin da ke akin sabida zuciyarsa da ta raya masa cewar yale Khairat in for now saboda a wuya take kuma komai zai iya faruwa idan ya ce zai mata wani bayani. Sai kawai ya shige ba yi ya yo wanka tare da auro alwala ya tada sallah ya yi raka'a biyu ya ro i ubangiji akan Allah ya sassauta fushin matar tasa ya kuma baiwa Babiyo da Zeenah lafiya. an le awa ya yi sai ya ga bacci arawo ya kwashe Khairat in. Ajiyar zuciya ya sauke mai arfi don shi fisabilillah tsoranta ya ji yana yi a yau in. Lalla awa ya yi ya gyara mata kwanciya tare da kashe wutar akin sannan ya hau gadon ya kwanta bayan ya yi addu'a ya shafa ma kansa da ita Khairat Rufe idanu ya yi amma sam bacci ya i zuwa masa, abubuwa hu u ne su kai masa tsaye a rai. Na farko idan Babiyo ya samu labarin Zeenah na cikin estate in nan bayan ya farka, na biyu kuma cikas in da Habib in ya ke son kawo masa, na ukun Khairat insa da ya ke matu ar so don kamar yadda ya ke jin ba zai iya ha ura da Zeenah ba, haka ya ke jin asa da sama za su ha e ba zai iya rabuwa da matarsa da take da wani special waje a zuciyarsa ba, sai na arshen ita kanta Zeenah in. Yadda ya ga rana dai haka ya ga dare. Kiran sallar farko ya tashi zaune ya ri e kansa saboda wani nauyi da ya masa. Idanunsa ya an juya ya kalli inda Khairat ke kwance a udundune. Hannu ya kai ya ta a goshinta da kanta, sai ya ji ya au zafi alamar zazza i ya rufe ta. Bargo ya ja mata da kyau ya lullu eta sannan ya sauka ya kunna wuta ya kashe mata AC. Bayi ya shiga, da ya kalli kansa cikin madubi sai da gabansa ya fa i saboda wani irin ulu- ulu da idanunsa suka yi, ga wani ja tamkar gauta da suka koma. Duk wanda ya gansa a haka ya san bacci bai wadace sa ba. Alwala ya aura ya dawo kan dardumar da ya yi sallah akai jiyan da daddare ya yi raka'atal fajri tare da wuturi. Zama ya an yi shuru a kan dardumar. Sai a wannan lokacin ya soma jin idanunsa na nauyi alamar baccin ya soma zuwa. Sosai ya yi ya i da zuciyarsa ya nanna e dardumar sannan ya fita daga akin bayan aukar key in mota kasancewar da nisa dagaa gidansa zuwa masallacin Ar o Barkin Yana fita da mintuna goma aka kwa a kiran sallar asuba a masallacin wanda ya auki ilahirin Estate in gaba aya tamkar a kunnuwan jama'a ake yinsa. Khairat ma da ke bacci a wahale sabida zazza i, kiran sallar ne ya farkar da ita. Ji take hatta asusuwanta ciwo suke mata. Da kyar ta iya yaye bargon sannan ta zuro afafunta ta sauko ta shiga bayi. Bata damu da rashin ganinsa a akin ba, don ta tabbata yana masallaci. Sai dai abunda ya kuma ata mata rai shine fitan da ya yi ba tare da ya tashe ta. Shaa! Wasu hawaye suka zubo mata tare da jim dana sanin auren sa don ta fahimci shi ba sonta ya ke ba, tun da can ita ke haukanta. Da ruwan zafi ta yi alwala sannan ta dawo falon ta canza kaya zuwa doguwar riga ta saka safar afa. Da sauri ta ago tana ara saurara dakyau jin muryan da ke karatun sallah a cikin speaker. "Tabbas da matsawa! Hamma Abdul-Hameed da jan sallah ba Babiyo ba." ta fa i a bayyane jikinta na wani irin rawa. Don ta tabbata abu biyu ne zai hana Babiyo jan sallah a duniya, na farko mummunar rashin lafiya da ba zai iya mi ewa ba, ko kuma mutuwa. Don tun da ta tashi tai wayo a Ar o Barkin o ba ta ta a jin wani murya na jan sallah ba face na Babiyo. Sallar ta tada gabanta na mugun bugu tana kuma fatan Jawaad ya dawo da wuri duk da tana matsanaicin jin haushinsa tai masa tambayar da ke zuciyanta wanda bata fatan aya daga cikin abunda ta raya ya tabbata. (Sai ha uri Khairat don tabbas Babiyonku na can kwance a kan gadon asibiti bai san inda kansa ya ke ba.) _MAMIYO_ Tana shiga akinta ta rarumi waya ta dannawa malam mai hula kira, yana ringing ji take tamkar zuciyarta za ta faso irjinta. Sai da ya kusa katsewa ya auka tare da yin sallama. Ko amsa sallamarsa ba ta yi sai ta soma kora masa jawabai. "Malam ka fa a min in kwantar da hankalina ni ce da nasara, amma a yau komai ya kwa e min. Yau Ardo ya san ko ni wacece. Sannan kuma ya kama 'ya'yana dumu-dumu da arin kashe mahaifinsu! Ka fa a min menene mafita!?" ta arisa maganar da arfi. an jim malam ya yi kamun ya furta, "Na fa a miki tuntuni kar ki warware ala ar da kika raba na wancen yarinyar da Abdul-Hameed amma idanunki sun rufe, na fa a miki warware farra'un yana nufin warware duk wani shirinki amma ki ka i saurarena balle na miki bayani dalla-dalla. Na fa a miki hakan zai jawo mace-mace amma kina nuna duk wanda zai mutu ke dai bai dame ki ba in dai akan cikar burunki. Kuma irin aikin da nake maki ayine koma kan mashe iya!" "What? Mai kake fa i haka? Kasan kuwa mai kake fa a min?" Mamiyo ta fa i jikinta na rawa tamkar mazari. "Eh, ranki shi da e. Tun farkon aikin nan da na miki sai da na garga e ki kar ku sake da dai da rana aya ku yi kuskuren da shi mai gidan na ki zai gane abunda kike shiri a kansa. Don suna da wani kafi tun kaka da kakanni. Duk wadda ya nufe su da sharri to zai koma masa gwargwadon abunda ya nufe su da shi. Kakan mijinki shahararren malami ne da ke da taurin kai da kafiye kuma bai yafiya sam! Ya riga ya yiwa zuri'arsa wani kafi na kan gidansu akan duk wanda ya cuce su ya koma masa ko shi wanene." "Mai ya sa baka ta a fa a mini haka ba? Kenan kai ma yaudarata kake duk tsayin shekarun da muka auka tare? Menene ban maka shi a duniyar nan? Har hajj sau biyu ina kai ka. Kai da iyalanka duk ni nake ci da ku, irin sakayyar da za kai min kenan?" an murmushi ya yi sannan ya ce, "Na miki iya arin da zan miki. Kuma ke ma kin san kin buga na ki irin mulkin a cikin Ar o Barkin o domin Allah ya ara miki lokaci. Kin cutar da mutane da yawa haka kuma kin salwanwar da rayukan da ba su ji ba su gani ba. Kin kashe uwargidanki, kin kashe mahaifin Mardiyya, kin yi sanadiyar da aka kori aleri da Bel o. Kin sa Abdul-Hameed ya yi zina ya kuma samar da 'ya. Kin cuci rayuka da dama. Hatta shi kansa Babiyon kin cire masa jin an 'ya'yansa a zuciyarsa kuma kin wawushe dukiyarsa kin gina tafkeken kamfani tare da arin janye masa masu hannin yarinsa, kin....." "Enough!" Mamiyo ta fa i a tsawace tare da cigaba da magana, "Ban kira ka a wayaa domin kai min duk wannan lissafe-lissafen ba. Na kira ne domin ka ba ni mafita. Ina son ka kashe min Babiyo a wannan daren! Ka tura aljanunka su tsinke jijiyar ma ogwaransa ni kuma na yi maka al awarin miliyan hamsin idan na ji kukan mutuwarsa gobe." Wani mahaukacin dariyar ya arke da shi tare da fa in, "Ki saka a ranki aikin ki ya kammala, sai na ji sa o goben!" it ya kashe wayar yana fa in, "Wawuya!" a zahiri. Ajiyar zuciya mai arfi Mamiyo ta saki tana jin zuciyarta wasai yanzu. Kashe wuta ta yi bayan turawa 'ya'yan nata sa o a waya sannan ta hau gado ta kwanta. Bayan idar da sallar asubha da kyar Khairat ta shiga kelaye wani irin amai ana kan darduma don ta kasa motsawa daga inda take. Tun tana saka ran ganin Jawaad immediately after the prayer har ta cire rai. Ba aramin galabaita ta yi ba. Sai 7:14 ya shigo gidan don daga masallaci ha uwa su kai gaba aya suka tafi asibiti wajen Babiyo. Babu wanda bai zubda hawaye ba saboda yadda Babiyo ya koma a dare aya kawai. Ya samu matsalar shanyewar arin jiki saboda mummunar hawa da jininsa ya yi. Maganarsa ma sam ba ta fita sosai. Sai dai yai ta kallon 'ya'yansa nasa hawaye na zubowa daga kurmin idanunsa. Hannunsa mai lafiyar ya aga a hankali yana nuna Baffa aleri da Baffa Bel o. Da sauri suka nufe sa tare da du awa suka kamo hannunsa. Wani irin kuka suke yi tamkar zuciyarsu za ta fashe lokacin da yake shafa kawunansu yana arin yin magana amma bakin ya i
Chapter 106 · 0% Book details