← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 143

Sashe 59

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidan Abdul-Hameed in ya nufa, a ofar gate ya yi parking tare da fitowa ya yi cikin gidan da sauri bayan ya an waiga kudu da arewa. Tun daga farkon gidan ya ke kallon jini kasancewar tarr gidan ya ke da haske kamar rana saboda dogayen fitilun solar da suka awata gidan. Gabansa ne ya yanke ya fa i ganin babu alamar mutum a kaf filin gidan sai dai ga jini nan ya yi layi alamar ya fice daga gidan. Da sauri Hafiz ya juya tare da fita waje yana kallon asa domin tabbatarwa, aikuwa aro- aro ya yi arba da ishi- ishin jinin Abdul-Hameed in. Wani wawan ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi wanda ke nuni da tsoro da kuma tashin hankali. Jim ya yi na kusan mintuna biyar kamun ya nufi mota ya bu e ya shiga sannan ya lalubo Number in Mamiyo ya danna mata kira. Ringing biyu ta aga tare da fa "Hafizu, kar ka yi arin fa a min abunda zai buga zuciyata cikin daren nan. Don alamu sun nuna ba ni tare da nasara a yau." Ajiyar zuciya Hafiz ya sauke tare da fa in, "Hajiya, babu Abdul-Hameed a cikin gidan nan sai jininsa da ya bari kawai. Alamu sun nuna ya bar cikin gida don na ga sahun afafunsa da kuma jinin da ke zuwa a jikinsa har bakin gate ta waje." "Inna lillahi wa'inna ilaihir! Wallahi da badan ina tsoron harshena a kan ana ba, da yau babu abunda zai hana ni tsinewa Jibrila," tana gama fa in haka ta katse kiran tare da mayar da hannunta biyu a baya tana zaga akin. Su kuwa an nata sai bin ta da idanu suke kowanne irjins a na luguden tashin hankali idan har asirinsu ya tonu a cikin Ar o Barkin o. Don babu abunda zai hana Babiyo tsine masu tare da fatattakar su a cikin family na har abada. Wayar hannunta ta kalla bayan wani tunani ya fa o mata cikin ranta, cikin gaggawa ta kira layin Hafiz, bugu aya ya aga kiran. "Yanzu-yanzun nan ka tafi Ar o Barkin o specialist hospital ka duba min ko can ya tafi, kar ka yarda wani ya ganka. Idan can in ya nufa, ka kira ka fa a min sai kai tafiyarka kawai," tana gama fa in haka ta yanke waya tare da kallon an nata ta furta, "Dukkan ku ku wuce gidajanku, kar ku yarda ko a fuska matanku su fahimci wani abu bare kuma wani a cikin Ar o Barkin o. Da safe kuzo nan akwai wata muhimmiyar magana da zan tattauna da ku." a kai su kai gaba aya, aya bayan aya suka fice daga akin kowa da abunda ya ke sa awa cikin zuciyarsa. angaren Hafiz kuwa, nesa da asibin ya yi parking motarsa tare da fitowa bayan ya saka takunkumi (face mark) sannan ya doshi cikin asibitin. Yana tura kai ya dawo baya da uban sauri ganin Babiyo tsaye yem a ofar emergency room yana kaiwa da komowa, Baffa Gi o, Baffa Modibbo, Baffa Bobbo da wasu da bai ga fuskansu da kyau ba suma tsaye hankulansu a tashe. Tun da ya juya ko waigowa bai yi ba ya hau tsana uban sauri har ya isa wajen mota ya bu e ya shiga. Nisa sosai ya yi da asibitin sannan ya kira Mamiyo ya shaida mata abunda ya gano a asibitin. Wani wawan ajiyar zuciya Mamiyon ta saki tare da wani kasalallan murmushi sannan ta furta, "Ka je gida, aikinka ya kammala. Sai na neme ka da safe," it ta yanke wayar. "Ni Hafizu na shiga uku!" Ya fa i a bayyane yana urawa titi idanu tare da fa a dogon tunani akan ganin da ya yi wa aleri a cikin Ar o Barkin o, kuma tabbas ya san ba zuwan banza ya yi ba, don yanda ya yiwa aleri farin sani akan ba ar zuciyarsa wacce ya yo gatonsa gaba da baya wajen Babiyo, ba zai ta a kyale ko yafewa duk wanda ya cucesa ko kuma ata masa suna ba. Sai dai kuma abunda ya bashi mamaki shine; ya san aleri tunda ya ce ya bar Ar o Barkin o har abada a gaban idanun Babiyo wanda a yanda ansa ke shakkarsa da tsoransa, ko cikin mafarki babu wanda ya ta a kwatanta abunda alerin ya yi, to kuma abunda ya bashi mamaki shine, shin mai ya kawo alerin cikin adda kama a Ar o Barkin o, kuma mai ya taho yi? Tsahon shekaru goma sha sha bakwai zuwa sha takwas kenan da koran karen da Babiyo ya yi masa. Wata zufan tashin hankali ce ta yankowa Hafiz in duk da Ac da ke cikin motar, don har gangarowa take zuwa bayan kunnansa. Da kyar ya iya fuzgo hankalinsa waje guda ya nufi gidansa da ke nan cikin Ar o Barkin o wanda Babiyo dakansa ya ware waje guda ya gina masa 2bedroom duk kuwa da insa da bare a cikin zuri'arsa. Washa gari gagaruman abubuwa biyu ne suka faru a cikin Ar o Barkin o wanda ya tada hankulan jama'a sosai; na farko, kai wa rayuwar Abdul-Hameed harin da aka yi wanda kaso tamanin daga cikin zuri'ar gidan suka amince akan abokan takara ne suka nemi ganin bayan Abdul-Hameed in ganin tun ba a je ko ina ba jama'a su amshe sa hannu bibbiyu saboda yanda jaridu ke ta yawo da hotunansa da kuma jawabai akan kyawawan halayensa da kuma sanyin halinsa akan talakawa. Na biyu kuma fashewar kwarye a ofar akin amaryar baffa Gi o wanda ya jawo cece kuce a tsakanin wannan family domin sosai fa a da bala'i ya alle tsakanin an uwan amarya Mardiya da kuma an uwan Baffa Gi o, don kowa na bin bayan nasa ne. an uwan amarya basu yarda da cewar Mardiya ba kai budurcinta ba, su kuma an uwan ango, sun ce sam Baffa Gi o ba zai ta a yiwa arsu arya ba. Aunty Samira da tafi kowa za ewa, sai ura ashariya take don zargin Mama Halima take akan da saka hannunta da na mijin suka fasa kwarya don ya muzanta Mardiyan saboda bai aunarta kuma bai da damar cewa a'a ga umarnin Babiyo shiyasa ya bijiro da wannan wula ancin musamman ma da shi har yanzu bai ce ala akan cece kucen ba, ita kuma angaren Mama Halima suna ganin ta yi hakan ne saboda tsabar kishin an auro mata wacce ita ce ta raine ta da hannunta shiyasa suka ha a baki da mijin domin warware auren cikin sau i kasancewar sun san doka ce a cikin Ar o Barkin o duk wacce bata kawo budurcinta ba, za a saka mijin ya rubuta mata saki sannan a mayar da ita auye ba za ta ara shigowa birni ba har arshen rayuwarta. Mamiyo zaune a katafaran akinta babu abunda take yi sai girgiza afa, fuskanta auke da lafiyayyar murmushin da ke fitowa har asan zuciyarta saboda plan inta ya tafi a yanda ta tsara. Shigowar Nadiya aya daga cikin jikokinta ya saka ta ajiye afar a asa still murmushin bai gushe a kan kyakkyawar farar fuskanta da ta tsufa ba. aura afan Nadiya ta yi a kan cinyanta tana mammatsa mata kamar yanda ta saba a kowacce safiya irin wannan lokacin. "Nadiya!" Mamiyo ta yi kiran sunanta ba tare da ta kalli fuskanta ba kuma murmushin nan na kan fuskanta har wannan lokacin. "Na'am, Mamiyo," Nadiya ta fa i respectfully. "Idan kika kalle ni, da mai nake maki kama? Misali; idan aka ce ki fassara ni a cikin kalmomi mai za ki fa "Mace ke shu'uma, muguwa, makira, azzaluma, mara imani kuma mai san ganin komai ya zama sannan kowa ya uka a ashinta," Nadiya ta fa i cikin zuciyarta kanta a asa. "Nadiya!" Mamiyo ta kuma kiran sunanta a karo na biyu kuma a kausashe. an razana Nadiya ta yi tare da fa in, "Afuwan, Mamiyo! Na fa a kogin tunanin ta yanda zan fassara ki ne kamar yadda kika bu ata. Don ke in babu wani halce da zai iya bayyanar da tsantsan mulki da haibarki a kaf fa in Ar o Barkin o. Ke in sarauniya ce wacce ake shakka da jin tsoro fiye da yadda sauran aukacin dabbobi ke jin firgici da ma aukakin tsoron yayin da suka ji kukan ZAKI kawai. Babu wani mahalu in da zai iya gaba da gaba dake, idan na ce kowa kuwa ina nufin har da mai wannan katafaran Estate in, wato Ar o Barkin o (Babiyo), don ko shi yana shakkar ki." Wani irin da i ne ke tsirga tun daga ma igan Mamiyo har tafin kafanta. Ko awar da Nadiya ta mata ya ratsa ta sosai kuma ta ji da in haka. "Tashi ki shiga akina, za ki ga wata sar ar zinari a kan madubi, ki auka na baki matsayin tukuicinki," Mamiyo ta fa am ta ri afar Mamiyo tana ta koro godiya kamun nan ta mi e ta shiga ta auko sar ar da nauyinta zai kai gram shida da igo uku. Jiki na rawa Nadiya ta fito tana ara kwararo godiya sannan ta fice daga akin. A can Asibiti kuwa, Babiyo bai bar asibitin nan ba jiya sai da numfashin Abdul-Hameed ya daidaita wajajen arfe biyun dare zuciyarsa na susa da kuma tunanin wani mara kwalli a idon ne da har ya iya takowa ya shigo har cikin Barkin o domin cutar masa da Abdul-Hameed insa. Sosai ya auki alwashin bincike mai tsauri domin aukar mummunar mataki akan koma wanene d ya yi arin kashe masa mafi soyuwa daga cikin jikokinsa maza. Da sassafe kuma maganar fashewar kwarya ya riski kunnansa daga sashin Baffa Gi o. Wani irin rintse idanu ya yi yana jin una a cikin zuciyarsa jin wannan mummunar labarin. Zina yana aga daga cikin mafi munin abunda Babiyo ya tsana a samu daga cikin zuri'arsa musamman ma ga wa anda ya aura yarda da aminci a kan tarbiyarsu. Wayarsa ya jawo a fusace tare da kira Mamiyo a waya. Mamiyo da ke parlourn zaune tana jiran kira daga wajen Babiyon, kiran na shigowa ta yi saurin aga kiran ta kara a kunnenta. Babiyo ko amsa sallamarta bai tsaya yi ba, a kausashe ya furta, "A tattaro
Chapter 59 · 0% Book details