Sashe 49
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta masa saboda wani uban haushinsa da take ji. "Ga magungunanta nan na sayo mata da allura. Ta ta a haka lokacin da muka je Paris, so na kai ta asibiti sun fa a min hawan jini take fama dashi mai saka matsanaicin ciwon kai saboda tashin hankalin rashi Meema da tayi har hakan ya saka jininta ya yi mugun hawa. Amma ya ce idan tana shan wa annan magungunar za ta samu sau i, in Sha Allah!" Ladi ta an ji gamsuwa da maganganun Sabo da Kazan saboda ita shaida ce a kan halin rashin bacci da tashin hankalin da Laushin ta shiga a wancan lokacin. Don baza ta manta da irin kwayoyin, sigari da wiwin da ta yi ta bankawa cikinta ba. Da taimakon Ladi da Salmanu har da shi Sabo da kazan, sannan ya samu nasarar danneta ya mata uren magungunar da ya shigo da su sannan ya danna mata wata allurar. Nan da nan jikinta ya saki ta hau bacci. Da kansa ya kai ta bedroom inta ya jawo ofar. Lokacin da ya dawo parlourn har Ladi Katifa ta yi nasarar farfa o da Meema daga sumar da ta yi. Sai da babu abunda take sai kuka tana fa in a kaita wajan mummynta. "Ki kaita akin ta ganta saboda hankalinta ya kwanta. Ni zan tafi kuma asar zan bari. Ki zo na yi maki bayanin magungunar nan, duk lokacin da abun ya taso mata kina bata su In Sha Allah za ta dawo normal, ciwon kan kuma zai bari." Tashi Ladi Katifa ta yi tare da ri o hannun Meema suka nufi bedroom in Laushin. Tura ofar ta yi a hankali sannan suka shiga ciki. "Kin ga mummyn na ki bacci take yi, ta samu sau i ki daina kukan kin ji daughter?" a kai Meema ta yi tare da fa in, "I want to sleep beside her, please." a mata kai ta yi, ita kuma ta tafi ta hau kan gadon tare da kwanciya a gefen Laushi ta shige jikinta sosai sannan ta aura kanta a kan kafa ar uwar. Wani irin mugun tausayin su duk su biyun ya kama Ladi har sai da hawaye ya zubo mata daga idanunta. Ta jima tana kallon su kamun ta juya ta fice daga akin ta rufo masu ofar ta dawo parlourn. "Ina kuma ita Meeman ta ke?" Sabo da Kaza ya fa i yana kallon Ladi. "Tana can kwance gefen uwar. Ka san ita Meema akwai ulafucin uwa. Yanzu haka sai ka ga tafi uwar rama a kan halin rashin lafiyar da uwar take ciki," Ladi Katifa ta fa Ba tare da ya ce komai ba ya fiddo duka magungunar ciki ya shiga nuna mata yanda za ta ba Laushin. Wasu sai ciwon ya tashi, wasu kuma kullum safe da dare. "Kin gane ko?" Sabo da Kaza ya fadi. "Eh duk na gane. Wannan ka ce asha safe da dare, wannan kuma sai ciwon ya tashi. Wannan kuma kace duk za ta ci abincin ta saka a asan harshenta. "A'a fa, ba haka na ce a wannan na arshen ba, cewa na yi kamun ta ci abinci ta saka. Misali saura mintuna talatin ta ci sai ta saka shi a asan harshenta, life support ne." "Ok, na fahinta yanzu." Ladi ta fa i tana kwashe kwalayan magungunar tare da sakawa cikin leda. "Ni na wuce," ya fa i tare da nufa ofar akin ba tare da juyowa ko sau aya ba. Don har wani sauri yake kamar zai tashi sama.. "Salma, ni fa ban yarda da wannan mutumin ba fa," Ladi Katifa ta fa "Amma ke dai Allah shi ebe miki albarka! Wacece kuma Salma babu da in ji? Tuf! Maza tofar wallahi. Bar tura ni jinsin an maza. Gandareran saurayi majiyi arfi ne a gabanki," fa in Salmanu an daudu. Waro idanu Ladi ta yi tana dariya tare da fa in, "Yau kuma? Menene ya canza maka ra'ayi haka yau?" "Dama ai daudu riga ce, da na cire shikenan na dawo gandareran aton saurayi. Tuni, na cire shegiyar rigar na yasar a asa. Kin ga, bar ni na mutu maza an uwana su kai ni ba mata ba." Wannan karan dariya Ladi Katifa ke yi har da zaman an bori a asa. Eh, lallai maza anji anani an tuba an koma ga Allah!" "Annabi umar da annabi Abubakar uban Nana Aisha duk suma tuban suka yi, don da ba musulmai suke ba, zuwan manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya basu kalmar shahada suka amsa," Salma nice ya fa "Kai! Iya bakinka. Ba annabawa bane Sahabbai ne. Sayyidina Umar da Abubakar za ka ce," fa in Ladi Katifa. "Yauwa su, hakan in nake son fa i sai na yi mistin (Mistake). To kin gani. Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne kawai bai ta a laifi ba a wannan duniyar. Kuma billahi na karanta a hadisi lokacin Iyan mai danko tana tura ni makarantar allo kamun na yi murabus na auki tsinanna rigar daudu na saka a jikina. Ni ya ma hadisin ya ke, yauwa na tuna _Wallahi inni la astagfirullaha, wa'a tubu ilaihi, Astara min saba'ina marrat (wallahi Ni ina naiman gafara Allah, kuma ina tuba a gare shi fiye da so saba'in a rana)._ Idan Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da bai yi laifin komai ba har ya bar duniya zai nemi gafarar Allah da tuba zuwa gare shi, Ni atoto mai ti en zunubi ai sai sau dubu malala gashin tinkiya. A'a wallahi, bar ni na tuba zuwa ga mahalicina. Wallahi daga yau babu wata sallar jam'i da za ta ara wuce ni sai dai idan ban da lafiyar da jikina baza ta iya motsawa ba." Jinjina kai Ladi Katifa ta yi ganin dagaske Salmanu ya ke tare da fa in, "To, Allah ya sa dai tuban ba na muzuru bane. Harararta ya yi tare da fa in, "Ba in ciki kike da wannan tuban nawa tabbas! To yau kamun rana ta fa i sai na tofe ki da Li'ilafi quraishin afa ari hu u da uku, sannan in biki da ul'uhiya afa dubu, wa'innahu Sulaimanu afa casa'in don ga dukkan alamu jinnin ba in hali ke tattare da ke, kuma ba zan dakata ba har sai na rufe da Alamtarakaifa afa saba'in da takwas." Dariyarta ne ya auke if tuno da abokin wasanta Mu'awiyah kasancewar shine da anyi abu zai ce to wallahi Alamtarakaifa afa saba'in ya kama ku idan har kuna so Allah ya yafe muku. *_Bari mu an koma baya ka an muji wacece Ladi Katifa_* Asalin cikakken sunanta shine Rukayyah Shafi'u. Ita ar asalin jihar Kano ce a wani auyen da ake kira kunya. Ita ka ai ce a wajan mahaifinta mai suna malam Shafi'u da mahaifiyarta Uzaibatu. Ta kasance abun so a wajen iyayanta kasancewar ita ka ai Allah ya basu bayan tsawon shekaru goma sha biyu da aure. Malam Shafi'u wani aramin mai ku auye ne, domin ko a wannan zamanin gidansa ba a cin shinkafa ar Hausa duk da kuwa yana noman ta. Idan ya yi girbi sai dai ya sai da ya kyautar da na kyautarwa wa dangi. Yana da annai biyu duka maza, Labaran da Mashakur. Dukkan su suna da mata da a don Mashakur ma ya riga shi aure don a cikin ansa manya maza suna masa aikin gona. Bai da yashi ko kuma rowa. Hannunsa a bu e ya ke ba ga an uwansa kawai ba har da mutanan gari. Yana hidimtawa an uwansa sosai saboda tamkar uba haka yake a wajensu saboda iyayan duka biyu asa ta rufe idanun su. Amma duk da wannan hidima da yake masu har da iyalansu, basu ganin hakan ko ka an sai ma mugun halinsa da suke gani saboda hassada da ya rufe idanun su. A duk sa'ar da Rakiya ta je gidan annan mahaifinta, daga matansu har su kansu sun dunga zaginta da dungurinta kenan suna fa in ga aruna nan wacce gidansu ba a cin ar Hausa da taliyar murji sai ta leda saboda an auki rayuwar arya da ji da kai. Haka za ta koma gida tana kuka sannan ta fa awa mahaifiyarta abunda aka mata, amma sai mahaifiyar ta garga e ta akan kar ta saki ta fa awa mahaifinta saboda a gaban idanunsa nuna wa suke ko ansu na cikinsu ba sa auna kamar yadda suke aunar Rakiya. "Haba Rakiya, ke dai kwanaki ka an ya rage maki ki tafi ki koma makarantarki ta bodin (boarding). Ki rabu da su wata rana sai labari. Kuma su in iyayanki ne. Misali yanzu a ce babu mu, dole wajen su za ki koma." Wannan magana ita Uzaibatu mahaifiyar Rakiya ta ke fa a mata a duk lokacin da ta dawo tana kuka daga gidan annan mahaifinta. A can cikin garin Kano take zuwa makaranta kwana mai suna Rumfa College. A duk lokacin da za ta koma, sayayya malam Shafi'u ke mata da yawa dangin su, madara, sukari, cornflakes, sabulun wanka, wanki, kwai, milo, magi star, couscous da sauransu. Idan annan mahaifin nata suka koma gida haka za su bajewa matayansu irin hidimar da Shafi'u ya yiwa Rakiya da za ta koma makarantar da su a wajansu karuwanci ya tura arsa. Sosai Rakiya ta tsaya masu a rai kuma sun mugun tsanarta musamman makarantar da take zuwa wanda ya tsaya musu a rai saboda an su ba sa zuwa sai aikin talle kawai. Lokacin Rakiya na Form 3 Allah ya auki rayuwar malam Shafi'u sakamakon ciwon ciki na kwana uku kacal. Labaran da kansa ya tafi cikin Kano har makarantarsu Rakiya ya auko ta. Tun a hanya ya fa a mata mahaifinta ya mutu ba tare da wani lalama ba ko dabara ta yanda ko mutuwar za ta dake ta ba kamar yanda ya fa a mata kwatsam haka ba. Har suka shigo Kunya kuka kawai Rakiya take yi. Uzaibatu kuwa ko idanunta ba ta iya bu ewa saboda tsabar kukan da ta sha na tashin hankali. Kukan bai kuma zuwan mata ba sai da ta yi arba da arta da ta shigo a gigice tana fa "Innarmu shikenan Baba ya tafi bazan ara ganinsa ba? Shikena babana gatana kuma mai sona ya tafi ya barni?" Babu wanda bata saka kuka ba da wannan