← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 143

Sashe 79

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sake fa i, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ga link nan a sama ku yi joining link in da ke sama domin samun labarin addarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* _Mu an waiwayi abunda ya faru a baya da kuma tarihin gidan Babiyo ka mun saukar Meema a jirgi_ _WANENE BABIYO_ Abubakar wanda ake kira da Lami o haifaffen garin Adamawa yola a aramar hukumar Mayo-Belwa. Cikakken bafulatani ne kuma makiyayi. Mutum ne mai matu ar zafin zuciya da ri o tamkar mahaifinsa Isiyaka. Idan ya zana abu a cikin zuciyarsa, to fa babu uban da ya isa ya canza shi ko da kuwa mahaifin nasa ne, hakan ya saka basu fiye jituwa ba. Yana da dukiya mai unbin yawa domin yana da shanaye da tumakai fiye da dubu. Yana da anne maza biyu da mace aya. Musa, Jafaru da Lawisa. Musa, Jafaru da Lawisa ba aramin shakkar Lami o suke ba, ko gigin tsallake umarninsa ba su ta a yi ba, sun ma fi jin shakkarsa fiye da mahaifinsu. Matan Lami o na aure biyu, Hure da Sakina. Hure ita ce matarsa ta fari, sun kwashi shekaru goma sha aya da aure amma babu haihuwa, hakan ce ta saka ya sake aure ya auro iyar abokin mahaifinsa wato Sakina. Sai dai ita ma haka ta kwashe shekaru uku ko ari bata ta a yi ba. Hakan ce ya sa aka aura rashin haihuwar a kan Lami o. Sai dai cikin hukuncin ubangiji, Sakina bata rufe shekaru hu u a gidan Lami o ba sai ga Hure da ciki. Ba aramin da i Lami o ya tsinci kansa a ciki ba. Wani mahaukacin kulawa ya shiga baiwa Hure tamkar zai su e ta tare da yi mata al awarin osassun shanaye biyar idan har ta haifa masa a namiji. Haka rayuwa ta yi ta tafiya suna kula da cikin Hure daga shi har Sakinar don ita ma ta yi farin ciki da samun juna biyu da ar uwar tata ta yi. Sai dai me, ciki na shiga wata hu u ya ta soma ciwon ciki tare da ba ar azaba mai tafe zubar jini. Wahalar da Hure ta ke sha tamkar za ta bar duniya. Hankali tashe Lami o ya sayar da aya daga cikin osasshiyar naggensa ya kai matarsa babban asibitin gamnati da ke cikin Yola. Sai dai tun kan su isa cikin ya riga da ya zube. Gashi Hure ta yi zubar jini sosai wanda ya saka dole aka ara mata jini har leda biyu. Sosai Lami o ya yi ba in cikin fitar wannan ciki da ya wallafa rai a kai, amma sai ya auki dangana. Bayan sati biyu aka sallami Hure suka tattaro suka dawo Mayo-Belwa. Sai dai bai manta garga in likita a kan duk lokacin da matarsa ta kuma samun ciki ya tabbatar ya kawo ta asibiti akai-akai domin a ri a duba ta da kuma abunda ke cikinta. Bayan watanni uku sai ga wani cikin jikin Hure. Wannan karan tsabar farinciki da zumu i sai ya tattara matansa duka biyun suka dawo cikin birnin Yola da zama bayan kama hayar ciki ai. Amma shi ya kan koma Mayo-Belwa domin duba dukiyoyinsa duk da cewar mahaifinsa na can garin, mahaifiyarsa ce shekarunsa hu u da auren Hure ta amsa kiran ubangiji. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya har cikin Hure ya shiga cikin na wata tara, kuma a wannan karon ma ya yi mata al awarin shanaye goma idan ta haifa masa namiji. Kuma tun da cikin ya yi wata 9 bai kuma komawa Mayo-Belwa, a cewarsa kada wani abu ya faru bai kusa. A wani daren litinin na uda ta kama Hure, da taimakon Sakina su ka kai Hure asibitin da bai da wani nisa da gidan da Lami o ya kama masu. Nan da nan aka amshe ta a kai akin haihuwa da ita. Sun kawo ta arfe sha aya na dare, ta sauka arfe uku da mintuna hamsin. Da farin ciki nurse ta fito ta shaidawa Lami o matarsa ta sauka, don Shi da Hure ko matsawa zuwa ofar reception ba su yi ba balle su fita. Da wani irin ma aukakin farinciki ya nufi nurse tare da fa in "Mai aka samu? Ta sauka lafiya?" "Alhamdulillah! Ta sauka lafiya, kuma suna cikin oshin lafiya ita da an da ta haifa." Sujada ya yi a gabanta kamun ya ago tare da fa in, "Kina nufin Hure ta sauka ta haifi namiji?? Kai Allah nagode maka." Daidai nan wata nurse ta fito hannunta ri e da jariri tana dariya. Rige-rige aka shiga yi tsakanin Sakina da Lami o wajen aukar an. Shi ya riga kai hannu ya amshe sa. Tamkar ya yi kaki domin babu inda ya baro sa. "Kalli Sakina, Barkin ona da ni ya ke kama!" Murmushi Sakina ta yi tana ara le en fuskan Jaririn. Da kyar Lami o ya bawa Sakina iyar ta ri e sabida yadda yake ji tamkar ya tsaga jiki ya mayar dashi ciki. Washa gari aka sallame su, kuma a ranar suka tattara suka wuce Mayo-Belwa. Ai kuwa dangi sai tururuwa ake wajen ganin an Lami Tun kamun suna Lami o ya cika al awarin da ya auka na bawa Hure Nagge har goma saboda haifo masa namiji da ya yi. Ranar suna kuwa ba aramin bidiri a kai na, domin sosai Lami o ya saki aljihu. Mahaifinsa shi ya ra awa jariri suna Adam (sunan maigari garinsu), amma kowa yana kiransa da Ar o saboda kara wa maigari. Mahaifinsa kuma yana kiransa da Ar o Barkin Shekarun Ar o Barkin o uku ya soma wani irin masassara sannan uraje suka feso masa a jiki. Lokaci guda sai ya suma fin biyar. Duk wani abu da aka bashi jiki bai sau i. Hakan ya saka Lami o ya ebe shi tare da Hure suka tafi cikin garin Yola domin duba shi a asibiti. Tashim farko gwaji ya nuna yana fama ne da akon dauro. Nan da nan aka soma bashi taimakon gaggawa, don cutar har so ta yi ta auke masa jinsa, amma cikin ikon Allah sai ya samu sau i bayan jinyar sati biyu a asibiti. Zama Lami o ya yi ya yanke wani shawara bayan an kai ruwa rana akan zai dawo da zama cikin yola, don sam mahaifinsa in amincewa ya yi da hakan, a cewarsa bai yarda da zamansa cikin yahudawa ba, kasancewar lokacin turawa suna ta ya a ilimin boko, yana gudun an nasa shima ya fa a harkar don babu babba babu yaro wajen karatun wanda a ganin mahaifin Lami on kafurci ne ilimin bokon. Negge hu u ya sayar ya shigo birni tare da sayan fuloti, sai dai dukgirman gidan nana akuna ciki ai ya yi guda hu u. Sai kuma Nagge da ya taho da su guda sha biyar da tumaki takwas daga cikin dukiyoyinsa. Sai ya barwa Jafaru da Musa su cigaba da kula masa da dukiyarsa ha e da na su don suma suna da dukiyar daidai gwargwado. Sam mahaifinsu Isiyaka bai ta aunar barin an nasa zuwa garin yola zama ba, haka ya sa ko sau aya bai ta a taka afarsa domin zuwa ganin inda ya tare ba. Isiyaka na da zafin zuciya da ri o fiye da tunanin mai tunani. Ko tafiyar Lami o birni sai da Ar on Mayo-Belwa ya saka baki tukun ya ha ura, shima don ba zai iya musu da Ar on bane don ban da shi shugaba ne tamkar uba haka yake kallonsa. Amma cikin zuciyarsa ji ya yafe wa cikin Yola Lami on. Kuma tun daga wannan rana Lami o bai sake ganin fara'ar mahaifinsa ba. Shekarun Ar o Barkin o takwas a duniya Sakina Matar Lami o na biyu ta samu ciki, lokacin Hure har ta sake haifan a biyu Isiyaka (sunan mahaifin Lami o sai suke masa inkiya da Ciroma) da kuma Ahmadu. A wannan lokacin hauhawar dukiyar Lami o ya kusa ninka na garin Mayo-Belwa, don tuni ya kuma saye filoti biyun da ke suka da ginansa ya ha e da nashi ya zama fuloti uku. Kuma jama'a sai tarewa suke a unguwar tana ara cika da mutane. Kasancewar Lami o shine kusan mutum na farko da ya fara tarewa a unguwar, sai aka sawa unguwar sunansa, wato _Unguwar Lami o Barkin o da annansa biyu duk suna zuwa makarantar boko wanda Lami on ne ya sakaa su don hakaa kawai sha'awar karatun boko ta shigesa sosai ganin yanda turawa ke koyar da ai kun a. Sai dai ko ka an Lami o bai sanar da mahaifinsa haka ba. Lokacin da cikin Sakina ya shiga wata tara, sai ta haifo kyakkyawar arta mace. Ba aramin da i Lami o ya ji ba, don dukkan su kuma sha'awar a mace suke a gidan. Ranar suna yarinya ta ci suna Firdausi. Mutanan Mayo-Belwa sun zo sosai domin taya Sakina da Lami o murya, kuma a wannan lokacin ne suka fahimci an Lami o suna karatun kafurci (boko). Da yawan su sun agu su koma Mayo-Belwa domin aras da abunda idanunsu ya gani wa mahaifin Lami Shi kansa Lami on jikinsa ya bashi hakan, amma saboda taurin kai da arfin zuciya ko gezau bai yi kuma bai jin ko za a hau sama a fa o zai cire ansa a makarantar boko. Illai kuwa, matanan suna suna isa Mayo-Belwa suka sanarwa mahaiifin Lami o abunda ke faru. Ba aramin girgiza ya yi ba kuma ransa idan ya kai dubu duk sun aci. Abunda bai ta a burin ya yi ba shi ya yi, wato tafiya cikin birnin Yola domin gane ma kansa abunda aka fa a masa. Tare suka tafi da Musa anin Lami o don shi ya san inda Lami on ke zaune kasancewar suna zuwa shi da Jafar. Lami o bai wani mamakin ganin mahaifin nasa ba don ya san za a rina. Tarba mai kyau ya yi masu tare da umartar Hure ta soye masu zabbi tare da kawo masu damammiyar hura. Sai dai ko kallon kufin ruwan da Hure ta ajiye bai yi ya hau jero masa tambayoyi. "Ina Ar o Ciroma da Ahmadu?" Ko kamun
Chapter 79 · 0% Book details