Sashe 128
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ma'aikin Allah (s.a.w) yanzu mutum ya zagi iyayensa? Sai ya ce: haka ne mana, idan mutum ya zagi iyayen wani, shi ma wancan sai ya zagi iyayensa . Ba Wa Iyaye Dukiya 'Ya'ya na gari masu imani su ne wadanda suke sanya komai nasu a hannun iyayensu, kuma ba su taba fasa bayar da dukiyarsu ga iyayensu ba, komai nasu suke bukata sai su ba su. Imam Ridha (a.s) yana fada a wata wasiyya mai hikima da ya yi ga 'ya'ya yana mai cewa: Farin ciki ya same ka idan ka yi biyayya ga babanka, ka kyautata masa, ka kaskan da kai a gabansa da girmama shi da darajanta shi, ka yi kokari kodayaushe muryarka ta yi kasa da tasa, saboda shi ne asalin samuwarka da dalilin zuwanka duniya, kuma kai reshe ne daga gareshi, idan da babanka ba ya nan da ba a same ka ba, don haka sai ka ba wa babanka da babarka dukiyarka. A wata ruwayar an ruwaito daga manzon Allah (s.a.w) cewa; Da kai da dukiyarka duk na babanka ne . Biyayya A Kan Tafarkin Gaskiya A bisa koyarwar Kur'ani wani abu ne wajibi a yi biyayya ga iyaye, kamar yadda Imam Ali (a.s) yake fada cewa; "Hakkin uba a kan da shi ne ya bi shi a komai banda a sabon Allah madaukaki" . Kuma haka nan wani mutum daga kasar Yaman ya zo wajen manzon Allah (s.a.w) domin ya tafi yaki tare da shi, sai Annabi (s.a.w) ya umarce shi da ya koma ya nemi izini da yardar iyayensa, " idan sun bayar da izini ka yi yaki, idan ba haka ba to sai ka yi musu kyawawan halaye, ka sani wannan aikin gareka ya fi dukkan biyayya ga dukkan umarnin Allah bayan kadaita Allah" . Kamar yadda dai muka yi nuni ne a baya cewa; kiyaye dukkan wadannan hakkokin yana kasancewa ne idan bai saba da keta hakkin wasu ba, don haka idan wani ya tauye hakkin 'ya'yansa da matarsa da 'yan'uwansa da sauran jama'a da sunan kare hakkin iyaye da biyayya garesu wannan bai dandani imani ba, kuma maimakon ya samu lada zai samu zunubi ne. Don haka ne ma muke karfafa cewa: Biyayya ga iyaye tana kasancewa ne banda inda ta saba wa Allah madaukaki da umarninsa. Lokacin Tsufa Wani babban bala'in da ya hau kan al'ummun da suke da'awar ci gaba a wanan duniya shi ne rashin kimanta tsofaffi, a wasu al'ummu idan iyaye sun tsufa sai a kai su gidan kula da raunana, sai iyaye su rasa samun mai nuna musu kauna a kusa alhalin suna bukatar haka daga 'ya'yansu kamar yadda 'ya'yansu suke bukata daga garesu yayin yarintarsu. Haka nan zaka ga iyaye tsofaffi suna cikin dandana azabar rashin samun wannan tausasawa da tausayawa, kai akwai wanda na ga yana kuka a gidan irin wadannan raunana a talabijin yana cewa; yau shekara bakwai ke nan sai dai dansa ya aiko masa da kayan abinci amma bai gan shi da idanuwansa ba, har ma yana neman hukuma ta tiamaka masa dansa ya zo ya gan shi da idanuwansa. Irin wannan rayuwa tana da daci matuka ga iyaye tsofaffi: Wannan abin takaici da yake wakana a wasu kasashen har na musulmi yana da zafi da zogi a zukata matuka, iyayen da suka dora dukkan rayuwarsu ga hidimar 'ya'ya da al'umma amma bayan duk wannan wahala sai sakamakonsu ya kasance tsarewa da kullewa kamar 'yan gidan yari, suna masu kirga kwanakin mutuwarsu har zuwa wafatinsu, a irin wannan duniya mai da'awar samun ci gaba da 'yancin dan'Adam. Idan mun yi dubi zuwa ga abubuwan da muka kawo zamu ga yadda addinin musulunci ya yi umarni da girmama iyaye ta yadda ya haramta gaya musu ma fi karancin kalmar da take nuni zuwa ga wulakanci . Ibrahim dan Shu'aib ya ce da Imam Sadik (a.s): Ina da uba wanda ya tsufa ya yi rauni matuka da gaske, ina goya shi, kuma ina kai shi waje domin ya biya bukatarsa. Sai Imam (a.s) ya ce masa: Duk yadda zaka iya ka yi wa babanka hidima, kai har ma ka dauki loma da hannunka ka sanya masa a bakinsa, wannan ne aikin da zai kasance sanadiyyar kubutarka daga wuta . Hakkokin Iyaye Bayan Mutuwa A mahangar musulunci hakkin iyaye kan 'ya'ya baya karewa da mutuwa, kamar yadda iyaye suke da hakki a lokacin da suke raye haka nan ma suna da hakki kan 'ya'ya bayan mutuwarsu. Wasu daga cikin irin wadannan hakkokin sun hada da: 1- Ziyarar kabarinsu; 2-Karanta musu Kur'ani; 3-Ba su ladan ayyukan alheri; 4-Biya musu basussukansu; 5-Yi musu hajji a ba su ladan; 6-Yi musu sadaka a ba su ladan; 7-Yi musu azumi a ba su ladan; 8-Ba su ladan 'yanta bayi; 9-Yi musu salla a ba su ladan; 10- Yi musu addu'a . Sakamakon Kyautata Wa Iyaye Idan mun koma zuwa ga hadisan imamai (a.s) zamu samu cewa sun yi nuni zuwa ga wani sakamako da za a samu sakamakon kyautata wa iyaye, kuma zamu yi nuni zuwa ga wasu daga cikinsu: Aljanna Wani mutum ya zo wajen Imam Sadik (a.s) ya ce: Ya kai dan manzon Allah! Babana ya tsufa kuma ni ina goya shi kuma ina kai shi ko'ina domin biyan bukatarsa. Sai Imam ya ce: Ka yi masa hidima iyakacin yadda zaka iya, ka sani wannan aikin shi zai kai ka aljanna ne . Ladan Shahada Wata rana manzon Allah (s.a.w) ya ga wani saurayi wanda ya shagaltu da neman abin rayuwarsa sai ya ce masa: "Ya kai saurayi! Shin kana kula da wani da wannan kudin da kake samu? Sai ya ce: E. Sai ya ce: Waye? Sai ya ce: Babata. Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Kada ka daina yi mata hidima, don ka sani aljanna tana karkashin kafafunta". Kuma Manzon Allah (s.a.w) ya kara da cewa: Da ladan shahada ya kasance ga wanda aka kashe a tafarkin Allah ne kawai da ke nan shahidan al'ummata 'yan kadan ne, sannan sai ya kawo mutane bakwai na musulmi da ake kirga su cikin shahidai kamar haka: 1-Wanda ya kone a wuta; 2-Wanda ya mutu a cikin matsatsin mutane; 3-Matar da mutum yayin haihuwa; 4-Wanda gini ya fado masa ya mutu; 5-Wanda ya nutse a ruwa ya mutu; 6-Musulmin da ata dabba ta cinye shi; 7-Da wanda yake kokarin ganin ya yalwata wa iyalinsa dai iyayensa; Wadannan dukkaninsu suna cikin shahidai ; Ya Fi Jihadi Lada Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Shugaban masu alheri ranar lahira shi ne wanda yake yi wa iyayensa abubuwan alheri bayan mutuwarsu. Imam Sadik (a.s) ya ce: Wani mutum ya zo wajen ma'aikin Allah (s.a.w) sai ya ce: Ya ma'aikin Allah! Ni zan yi maka bai'a kan yin hijira da yaki. Sai manzon Allah (s.a.w) ya tambaye shi: shin daya daga cikin iyayenka yana raye? Sai ya ce: E, duka biyun suna raye. Manzon Allah (s.a.w) ya sake tamaya: Shin kana son ladan lahira wajen Allah madaukaki? Sai ya ce; E. Sai manzon Allah ya ce: To ka koma wajen iyayenka, kuma ka kyautata musu. Mafi Kyawun Aiki Cikon annabawa (s.a.w) yana cewa: Duk wanda yake son ya samu tsawon rayuwa da yalwa a rayuwa da arziki, da kuma dukiya mai yawa, to ya kyautata wa iyayensa. Domin kuwa wannan aikin wani bangare ne na biyayya ga Allah madaukaki. Wannan al'amari tabbas yana nuna mana cewa izzar duniya da lahira tana cikin biyayya ga iyaye ne. Kuma ya zo a wata ruwaya cewa: Mansur dan Hazim ya tambayi Imam Sadik (a.s): Wane aiki ne ya fi sauran ayyuka. Sai Imam (a.s) ya ce: Salla a lokacinta, da biyayya ga iyaye, da jihadi a tafarkin Allah" . Tsawon Rayuwa Da Samun Da Nagari Manzon rahama (s.a.w) yana cewa: "Duk wanda ya yi mini alkawarin kyawawan halaye ga iyayensa to ni ma zan lamunce masa dukiya mai yawa da tsawon rayuwa, da soyayya da kuma daukaka tsakanin iyalai da danginsa . Haka nan a wata ruwayar ya zo cewa; "Ku bi iyayenku sai 'ya'yanku su bi ku" . Saukin Mutuwa Imam Sadik (a.s) ya ba wa 'ya'yan da suke aikin alheri da kyautata wa iyaye ladan cewa: "Duk wanda yake son ya samu sauki a wajen Ubangijinsa yayin mutuwa to ya sadar da zumuncinsa, kuma ya kyauta wa iyayensa, idan ya yi haka to zai samu sauki yayin fitar ransa kuma ba zai samu talauci da miskinanci a rayuwarsa ta duniya ba. Wani saurayi daga sahabban manzon Allah (s.a.w) da ya yi rashin lafiya aka kwantar da shi. Sai manzon Allah (s.a.w) ya tafi domin ya gai da shi. Ga halinsa ya yi tsanani kuma ga shi karshen rayuwarsa ne. sai manzon rahama ya umarce shi da ya fadi kalmar shahada, amma sai harshensa ya kasa kawo wannan kalma. Sai manon Allah (s.a.w) ya tambayi wata mata da take wurin cewa: Shin wannan saurayi yana da uwa kuwa? Sai ya ta ce: E, ni ce babarsa. Sai ya ce: Shin kina fushi da shi ne? Sai ya ta ce: E, ya ma'aikin Allah. Sai manzon rahama (s.a.w) ya nemi ta yafe masa kurakuransa, sai ta ce: Ya ma'aikin Allah na yafe masa saboda kai. A wannan lokacin sai manzon Allah ya sanar da wannan saurayi wannan addu'a: Ya man yakabalul yasira wa ya'afu anil kasir, ikbil minni alyasir wa'afu annil kasir, innaka antal afuwwul gafur. Sannan sai ya lakkana masa kalmar shahada, a wannan lokacin ne saurayi ya bude bakinsa cikin sauki ya fadi wannan kalma ta shahada" . Ladan Hajji Manzon Allah (s.a.w) ya ce: babu wani da da zai kalli fuskar iyayensa da tausayawa da rahama sai Ubangiji ya rubuta masa ladan hajji kan kowane kallo da ya yi. Sai sahabban manzon Allah (s.a.w) suka ce: Ya ma'aikin Allah! Idan mutum ya kalli fuskar baban da babarsa a sau dari fa za a ba shi wannan ladan? Sai ya ce: Haka ne, koda kuwa ya kalla sau dari ne to za a ba shi ladan hajji sau dari. Ubangiji madaukaki mai iko ne ya ba shi lada sama da haka . Shafe Zunubai Samun gafarar zunubai yana daya daga cikin abubuwan da ake samu saboda kyautata wa iyaye. Imami na shida yana cewa; wata rana wani mutum ya zo wajen Annabi (s.a.w) sai ya ce: Ya ma'aikin Allah! Lokacin da na sami