← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 143

Sashe 61

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meema ne? #Babiyo #Mamiyo #Baffa Gi #Baffa Jibrila #Amarya Mardiyya #Hafizu driver/informer #Abdul-Hameed #Habib #Jawaad #Laushi #Meema #My Destiny #Matar Sayyadee #Barka da Sallah 08128755583 [7/8, 8:43 PM] Matar Sayyadee: *_MY DESTINY_* ( ~ addarata~) *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION* ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*) ```Takenmu shine unkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.` Page 35 *For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* *_Don girman Allah zan sake fa i, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin addarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* Zuciya sosai ta ciyo Babiyo ganin ya aje ayar magana amma kuma Samira babu alamu na yin magana a tattare da ita, jikinta ne kawai ke tsuma kamar an taurin da ake bugawa kirari da ki an gangi. wafa mai sauti Babiyo ya saki tare da furta, "Tunda haka kika za a na tada min hankali a cikin zuri'a, to na baki daga yau zuwa gobe, ki tattara kayanki ki wuce Yola, ko kuma ki bi Tukur ku wuce tare da Zubaida ( iyar Baffa Modibbo kuma anwar Marwanatu) tunda ita ma ta i zaman aure kuma ta hana wasu su zauna a nasu gidajen." Bakin Aunty Samira rawa yake yi kamar wacce ke rayuwa a dusar ara, so take ta bu e baki ta nemi yafiya, amma ta san muddin ta yi hakan ta kuma jawowa kanta bala'i da masifa wanda zai shafi har da mahaifinta wanda ani yake a wajan Babiyo in, uba aya amma uwa kowa da tasa. Aunty Zubaida kuka take sosai raku e da jikin kakarta, mahaifiyar Baffa Modibbo kuma matar Babiyo. Sai dai duk da kasancewarta matarsa, tamkar sakakka haka take cikin gidan ita da ayar matan, don gwara ma ita akan ayar kasancewar ita ko maganarta ma ba a ji kuma ba kowa ke zuwa inda take ba, hakan kuma umarni ne daga Mamiyo wacce ta yiwa Babiyo fanfo akan haka, shi kuma ya amince sakamakon haushin anta aya tilo da yake ji, wato alerin da ya kora a gidan shekaru sha da suka wuce. Kallon da Babiyo ya watsowa Baffa Gi o ne ya saka hantar cikinsa adawa ya sunkuyar da kai gabansa na fa uwa yana fatan Allah yasa indai tambaya ce game da budurcin Mardiya, ayi sa a ke ance ba a gaban wannan unbin jama'ar ba. Sai dai kash! Addu'arsa bata kar u ba sakamakon jeho masa tambaya da Babiyon ya yi wanda ya ji saukar sautin har cikin wan kansa tamkar aradu ce ta fa o masa. "Menene gaskiya game da zancen kwaryar da ka fasa? Shin Mardiya ba ta je da budurcinta akinka bane?" Ba shi ka ai da akai wa tambayar ba, mama Halima, Habib, Jawaad, surukansa, hatta ansa mata da kuma wasu daga cikin jikokin wani irin duum suka ji tare da wani irin kunya da takaici da ya lullu e su, musamman ma Habibu da yake jin kamar ya ruga da gudu ya fice daga akin taron. Mardiya kuwa kuka mai narka zuciya ta saki tana jin ina ma asa ta bu e ta shige ciki ta huta da wannan tereran ban adar da za ayi mata da wanda take masa kallon uba ba miji ba. Mamiyo kuwa wani gyaran zaman asaita ta yi don ta riga ta san Baffa Gi o ba zai musa akan Mardiya bata zo da budurcinta ba kasancewar tana da tabbacin ya sha i tutaren da ta goga a jikin Mardiyan lungu da sa o a jikinta. Babiyo kallon gefen da ya jiyo sautin muryan kukan Mardiyan ya yi yana jin wani takaicin na turni esa tare da fatan Allah ya sa ba dagaske bane abunda ake zarginta da shi, don idan ya tabbata gaskiya ne, shi ka ai ya san irin hukuncin da zai yi. Mayar da kallonsa wajen Baffa Gi o ya yi yana jiran arin bayani daga gare sa. Girgiza kai Baffa Gi o ya yi tare da fa in, "Ba gaskiya bane abunda ake yawo dashi a cikin Estate in nan. Ni ko hannun Mardiya ban ta a ba a jiyan balle har in san budurwar ce ko akasin haka." Wani irin zillo Mamiyo ta yi tare da sakin wani bahagon tarin da ya zo mata a bazata sakamakon jin zancen da ba tai tsammanin jinsa ba a cikin masarrafar jinta. Dakyar tarin ya tsaya don sai da aya daga cikin jikokin da ke akin ta yi saurin isa ga dispenser ta tsiyayo mata ruwa a glass cup tare da mi a mata. Tass ta sanye ruwan tana rarraba idanu. Sai da ta saisaita kanta tukun ta soma magana kasancewar gaba aya wajen zubo mata idanu a kai har da anta, "Wannan wani irin zancen banza ne? Wa ka ke son mayarwa abokan wasanka a nan? Ya za ka fasa kwarya da hannunka, sannan ka zo kana fa a mana ko hannun Mardiya baka ta a ba! To uban wa ya fasa kenan? Kuma menene amfanin abunda ka aikata?" Da huci ta arisa maganar. Babiyo da ya auke idanunsa a kan Mamiyo tun san da ta soma maganar, wani irin murmushin ne ya su uce masa har sai da hakan ya bayyana wanda ya saka gaba aya akin suka wani irin auke numfashin mamaki don babu wanda bai ga hakan ba shimfide a saman fuskansa wanda abu ne mai matu ar wuya hakan. Kan Baffa Gi o a asa ya kuma maimaita abunda ya fa i cike da tabbaci. Mamiyo ta bu e baki za ta kuma yin magana, Babiyo ya aga mata hannu alamar bai son jin komai daga gare ta. Wani irin tsaam ta yi, domin hakan wani abu da bai ta a faruwa ba a kaf tarihin zaman fadar Babiyon. "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Na ji da i kwarai dagaske jin wacce na ke da tabbaci a kan tarbiyarta ari bisa ari, hakan ya ke. Wannan abu ya sanyaya min zuciya har ya saka na janye hukuncin da na zartar a karo na biyu a rayuwata; na farko dawowar Bel o cikin gidan nan, na biyu kuma yafewa Samira akan abunda ta aikatawa Halima na rashin kunya. Na yafe miki Samira, amma ki je har gida ki nai mi yafiyar Halima akan rashin kunyar da kika mata idan an tashi daga zaman nan." Aunty Samira ji ta yi kamar an tsoma ta a aljanna, nan da nan ta shiga kwararowa Babiyo godiya da kuma addu'ar tsawon rai. Mamiyo kuwa ji ta yi walwarta na neman fashewa, hankalinta ya mugun tashi sosai ganin cikin anin lokaci komai yana neman rinca e mata. "Daga yau, a yanzu kuma, ban so na ara jin wata magana dangane da fashewar kwarya har abada. Duk wanda ya taso da ita kuwa..........Hmm! Ba zan ce komai ba, na san dai kowa ya san irin hukuncin da zan iya yankewa. Ayi dogon addu'a ga Abdul-Hameed da ke kwance a kan gadon asibiti," fa in Babiyo murmushi auke a fuskansa. Cikin sakonni akin ya auki sauntin Jawaad yana koro addu'a kamar yanda Babiyo ya fa i. A cikin addu'ar kuwa, ya ha o har da wanda ke neman rayuwar Abdul-Hameed in da kuma duk wanda ke son ya ga ya tarwatsa Ar o Barkin o na jiki da na nesa. Sosai Mamiyo ta sha jinin jikinta, lokaci guda iyayyar Jawaad in ya kuma sukar zuciyarsa ita da anta. Bayan kammala addu'a, duka an Babiyo suka nufo sa yana shafa kawunansu tare da saka masu albarka suna ficewa daga akin. Jawaad da Habibu kuwa, kai tsaye suka wuce asibiti don basu samu labarin abunda ya faru ba sai da asuba da suka fito masallaci sallah. Bayan an idar da sallah ne Babiyo ya sanar. Hankulansu ba aramin tashi ya yi ba da jin hakan. Ko da suka isa asibitin, kwance suka taras dashi yana kallon sama an saka masa na'urar numfashi, eyarsa kuma wani tafkeken inki ne an rufe da bandage. Habib da yafi Jawaad nuna rauninsa a zahiri, tuni ya soma zubda hawaye yana la'antar duk wanda ya yiwa aminin nasa haka. Jawaad kuwa idanunsa ne sukai jajir la ansa na motsawa ganin halin da an uwansa ya ke ciki. Su an jima a asibitin kamun kowannen su ya nufi gidan amaryarsa cikin motocinsu. ilin! arar shigowar sa o ya shigo wayar Jawaad. Hannu ya mi a ya auki wayar dake cikin bonet tare da shigo inbox _Assalamu alaikum Oga, ga ta nan yanzu muka ga ta fito cikin wata makaranta ita ka ai. Yanzu haka ina bibiyarta a baya. Sai dai kuma tun fitowarta na lura da wasu suna bibiyarta ita ma, kuma sam ban yarda da su ba. Umarninka kawai nake jira._ Wani irin taka burki Jawaad ya yi tare da silalewa gefen titi ya faka sannan ya dannawa wanda ya turo maka da sa on kira. Bugu biyu ya aga kiran. "Har yanzu ana bin ta in ne? Ka yi duk yanda za ka yi ka saka ta shiga motarka, kar ka kuskura wani abu ya same ta!" Ya arisa maganar da an tsawa. "Yanzun nan kuwa, dama umarninka na ke jira," yana gama fa in haka ya katse kiran tare da age tinted glass window sama ya shiga bin bayan Laushi. Motar da take bin bayan Laushin na gab da shan gabanta, shi kuma ya taka motarsa da arfi ya riga su shan gabanta tare da bu e murfin gaba ya furta cikin sauri, "Shiga da sauri ki rufo ofar!" A razane ta an ja baya, amma ganin yanda motar bayansu ta ja wani mahaukacin burki, sannan kuma ta yi arba da fuskan Yasaar bata san lokacin da ta afka cikin motar da sauri ba ta rufe murfin motar shi kuma ya ja motar a ari da hamsin. Ganin haka Yasaar ma ya taka tashi motar da uban gudu yana bin bayansu. So ya ke ya fito da bindiga ya yi harbi amma babu dama don hakan zai iya
Chapter 61 · 0% Book details