← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 143

Sashe 100

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jikin Hafizu saboda tsabar ki imewa. Ya kasa ko warar motsi tsabar shiga tension. "Ka tashi ka fitar min a aki. Jibi iwar haka ina son jin labarin mutuwar aleri tare da takardun kamfanina da daddare kuma na Young Minister ya biyo baya. Saura aikin kuma, 'ya'yana za su gama da shi. Ku fitar min da shi!" iii! Suka ja Hafiz har ofar aki sannan suka watsar. Jibrila ya kalli Mamiyo tare da fa in, "Amma kina ganin ba zai fa awa aleri ba, don alamu ya nuna bakinsu aya." Murmushi Mamiyo ta yi tare da fad'in, "Ba zai kwatanta wannan shirmen ba don iyalansa suna a hannunmu." Jinjina kai Jibrila ya yi yana jin gamsuwa a ransa. Baffa Mahmuda ya kuma kallan Mamiyo tare da fa in, "To shi kuma boss in ya za muyi da shi." Hannu Mamiyo ta kai saitin wuyarta tare da ja alamar kisa sannan suka bushe da dariya duka. A wannan daren Habib, Jawaad, Laushi da Khairat suka duro Nigeria. Sai dai shi Habib ya riga su Jawaad isowa tun shekaran jiya. Tsayawa ya yi a Lagos domin neman Laushi don a tunaninsa Jawaad in bai same ta ba don tare suka bar Nigeria kuma a rana aya. Ganin bai same ta ba kuma ga biki jibi, sai kawai ya kuma hawowa jirgi shi da Amatunsa suka diro Abuja. Jawaad ya riga Habib shigowa Estate in, sai ya yi maza ya nufi gidansa ya aje Khairat da Zeenah sannan ya fito ya nufo gidan Babiyo kuma a wannan lokaci bold in su Habib ya shigo estate in daga airport. Babiyo zaune a kan kujeransa ta gado yana amsa waya Jawaad ya shigo. Waje ya samu a asa ya zauna yana jiran Babiyon ya kammala waya. Ya au tsayin mintuna yana wayar kamun ya kammala. Yana aje wayar ya kalli inda Jawaad in ya ke tare da bu e masa hannu alamar ya taho ya rungumesa. aramin mamaki Jawaad ya yi ba, amma sai ya mi e tsam ya nufe sa tare da rungumesan. "Allah ya yi maka albarka da zuri'arka gaba aya!" Babiyo ya fa i wanda ya saka Jawaad lumshe idanun farinciki don har walla sun taru a kwarmin idanunsa. "Ameen, na yi kewarka sosai Babiyona!" Jawaad ya fa Jan hancinsa ya yi yana murmushi sannan ya shiga tambayar sa iyalansa, "To ya alkhairin da na ha a, shin kana jin alfahari da haka?" Babiyo ya fa i da sigar zaulaya abunda bai ta a yi ba. "Har arshen rayuwata ba zan daina godiya ga ubangiji da kuma kai da kai silar wannan ulluwan auren ba. Ha a ne maganar da hausa suke yi na cewar duk abunda babba ya hango yaro ko ya hau rimi ba zai ta a hangowa ba. Nagode warai kakana." Wani irin murmushin ne ya su ucewa Babiyo har sai da ha waransa ya bayyana sannan ya furta, "Je gida jikana ka huta ka yi wanka sannan ka auki matarka ku tafi ku gaida iyayanku." "Godiya na ke yi," fa in Jawaad yana mamakin abunda ya hana Babiyo ce masa ya tafi ciki ga gaido da Mamiyo. Fitarsa bai fi da mintuna talatin ba Habib shima ya shigo. Kamar yadda ya yiwa Jawaad haka shima ya yi masa. Kuma dukkansu ya ji da in amsar da suka ba shi. Shima dai umartarsa ya yi da ya je ya huta sannan ya auki matarsa su gaida iyayansu. Da daddare Babiyo ya yi kiran Meeting tare da umarta kowa ya kasance don duka anan za a ha u aci abincin dare. Kowa da kowa, yara da jikokin babu wanda bai ji da in wannan walima ba. Don hatta Baffa Bel o da iyalansa suka wajen. Baffa aleri ne da iyalansa kawai ba sa wajen. Inna Karima da Inna arama suna gefen hagun Babiyo, yayin da Mamiyo da babu fara'a akan fuskanta ko ka an ke a gefen damansa. Don yanda Babiyon ke raha da jikokin nasa abunda bai ta a faruwa ba ko cikin mafarki ba aramin ona zuciyarta ya yi ba. Musamman ma da Babiyon ke jeho Baffa Bel o cikin hirarsa. "Babu komai kai rahar arshe, gata iwar haka matacce ne kai!" Mamiyo ta fa i a zuciya. "Ina ro on alfarma kowa, mada da mata, yara da manya akan mu duka mu azumci alhamis in gobe wato jajibarin aurin auren Abdul-Hameed, kuma a sati mai zuwa ne muke saka ran jin sunansa a matsayin ministern wannan birnin tarayyar. Amma fa ban tilastawa kowa ba, duk wanda ke da ya ga zai takura ba sai ya yi ba. Wa anda za su au niyya kuma, sai suka saka a ransu za su yi azumin ne da niyyar nemawa an uwasu ko ansu za in Allah akan wannan mulkin, idan har ba zai iya sauke nauyin da ke kansa ba na talakawa, kada Allah ya aura shi akai, sannan kuma da niyyar samun zaman lafiya da ha in kan wannan family da kuma kawar da fitintinu da rabuwar kai. Allah ya ba da ikon yi ya kuma sake ha amu kamar haka a cikin aljanna firdausi." Gaba aya akin da ameen aka amsa banda irin su Mamiyo da su Baffa Jibrila. Bayan rufe taro da addu'a kowa ya yi gidansa tare da matarsa. Jawaad kuwa Allah-Allah ya ke ya isa gida sabida Laushi da suka bari ita ka ai a gidan. "Ya kake gudu haka akan titi kamar za mu tashi sama?" Khairat ta fa a tana kallonsa. an tsaki ya yi tare da fa in, "Duba sha aya ta wuce fa! Mun bar baiwar Allah ita ka ai a gida." "Shiyasa hankalinka ya tashi hakaa? Ni fa na lura gaba aya yarinyar nan a zuciyarka ta ke. Bam tunanin ko shi mijin nata zai iya nuna damuwa haka a kanta kamar yadda kake yi." "A'uzu billahi! Haba Khairiyyah, kar kishi ya rufe miki idanu haka mana. Matar wani ce fa!" ya fa i yana an rage gudun motar. "Kuma ai na ga dai ba yarinya bace da za ka damu haka don mun barta ita ka ai a gida. Ina ga nan gama cikin aljihu za ka ri a saka ta kana yawo da ita." Shuru bai ce komai ba har suka iso gida. Don ya nuna mata shi ba zumu in ganin Zeenah in ya ke ba, sai kawai ya wuce bedroom insu ba tare da ko kallo aya ya yiwa akin da Zeena ta ke ciki ba. Kuma hakan ya mata da i sosai duk da ita sai da ta le a ta ganta kwance tana bacci. Washa gari mutane da dama sun tashi da azumi a Ar o Barkin o, irin su Mamiyo da 'ya'yanta ne kawai ba mai yi, sai dai kuma su ka ai suka san haka. Don a wajen sauran jama'a suna yi. Sai kuma wasu daga cikin mata masu lalurarmu ta haila. Wani aramar warya- waryan walima Babiyon ya saka aka ha a lokacin bu e baki. Anci ansha kuma anyi raha tare da addua wa Abdul-Hameed da kuma ahalin gaba aya har da su Jawaad da Habib akan Allah ya ba su zaman lafiya da zuri'a ayyiba. Kuma kamun a watse sai da Babiyo ya ro i yafiyar duk wanda ya ata wa rai bayan ya yi maganganu masu tsuma zuciya da ya saka mutane da yawa kokawa. Don hatta mutanan Yola duk sun hallara kasancewar gobe ne aurin aure. Washa gari kuwa da gagarumin biki aka tashi a estate in. Tun sha ayaa motoci su kai zuga suka tafi aurin aure Kaduna. A gidan Jawaad kuwa, Zeenah ce kawai cikin gidan a rufe a aki don Jawaad sosai ya bugawa Khairat warning akan kar ta kuskura kowa ya ga Zeenah kuma ko waye shi. arfe hu u su Babiyo suka dawo har da amarya da danginta. Kai tsaye Babiyo ya ce a wuce da ita gidan Baffa Bel o wanda hakan si da ya kusa tsayar da numfashin Mamiyo. Don a al'ada dai wajenta ya kamata a kai amarya. Dakyat ta iya danne hakan a zuciyarta. Washa gari ma da wani gaggarumin bikin aka tashi, dangin amarya Asma'u ma da su akai shagali, sai bayan la'asar Babiyo ya saka aka mayar da su gida bayan sun kai amarya akinta da ke Abdul-Hameed close. "Mama Halima, don Allah bari na an je gidan Hamma Habib na kwana can, kin ga nan anyi yawa har yanzu akwai ba in biki." Marwantu ta fa Kamar Mama Halima ta ce mata a'a, sai kuma ta ga kamar Marwanatun za ta ji ba da i, sai ta gya a mata kai. Da sauri ta juya ta bar akin duk da kuwa dare ya yi don goma saura mintuna biyar. Wanda zai kai ya ta shiga nema don akwai nisa baza ta iya tafiya a afa ba. Jawaad ganin Khairat baccin gajiya ya dauketa sosai don tum shigowarsu ta ke gyangya i a falo. Sai ya lalla a ya fito ya nufi akin da Laushi ke kwance. Tura ofar ya yi ya shiga, to his surprice idanunta biyu hannunta rike da kai tana hawaye. Bai san lokacin da ya arisa ya kusa da ita ba tare da zube guiwowinsa a asa ya kamo hannunta yana le en fuskanta tare da kama hannunta biyu da ke ri e da kanta ya furta, "Zee! Zee mai ke damunki? Why are you crying?" Ko kamun Zeenah ta yi magana suka soma jin wani irin tafi a bayansu wanda ya saka Jawaad ya juya a firgice, ita ma Laushi da sauri ta ago kai tana kallon ofar akin. Khairat ce tsaye sanye da doguwar rigar bacci fuskanta tamkar an aiko mata da sa on mutuwa. Da hannu ta nuna su sannan ta ce, "Cin amanar da za ku min kenan? Matar abokin naka kake zagayowa kana fasi anci da ita? Ni za kai wa haka Jawaad?" ta arisa maganar wasu irin wallar ba in ciki na kwaranyo mata daga idanu. "To wallahi tallahi a yau innan ba gobe sai ta bar min gidan mijina!" ta kuma fa i a matu ar fusace tare da cafko hannun Zeenah tare da soma janta iii tana fa in, "Sai kin fitar min daga gidan miji karuwar banza da hofi." Da sauri Jawaad
Chapter 100 · 0% Book details