← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 143

Sashe 60

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kowa da kowa, iyaye da yara su ha u a fada!" Yana gama fa in haka ya katse kiran. _Lagos_ Kallo aya kawai za kai wa Laushi gabanka ya fa i in har ka mata farin sani a baya, don yanzu ta yi wani irin zabgewa ta lalace saboda cutar da ke neman haukata walwarta. Wani lokacin haka za ta yi abu kamar na mai hankali, wani lokacin kuma kamar haka-haka. So da dama tafi zama shuru ta urawa wani waje idanu ko kuma ta kafe Meema ko Ladi Katifa da idanu tana hawaye. Idan kuma abun ya lafa, baza ka ta a tunanin tana da wani cuta a walwarta ba sai dai uban rama da tayi don dogon hanci da manyan idanunta kawai kake hangowa a waje. angaren Yasaar kuwa, ya gama ha a plan insa wanda abokinsa Layos ke ba shi gudunmawa domin ganin bayan Sabo da Kaza. Don Yasaar ya lashi takobin sai ya nunawa Sabo da Kaza ya fishi sanin kan tsiya... Yau da Laushi ta tashi da arfin jiki domin cutar ta an lafa mata. Sai dai gaba aya jikinta a sanyaye yake. Sauka daga kan gado ta yi tare da yaye duvet in da ta lullu a da shi tare da kallon gefenta da Meema ke kwance tana bacci. Gashin da ya rufe idanun Meeman ta mayar dashi baya tare da kallon fuskanta na kusan tsayin mintuna biyar. Kanta ne ta ji ya mata wani duum har sai da ta kai hannu ta ri e kan na wasu mintuna kamun ta kuma mayar da kanta kan Meema da girma ya fara zuwan mata. Don shekarunta goma sha aya, watannin ka an ne babu. Tana da tsayi don ko a yanzu ka an ya rage ta kamo uwar, kyawunta sai da a fitowa ya ke. Komai na Meema mai matukar kyau ne. Da kallo ta bi tun daga kan Meema har afafunta, gabanta ne ya fa i sosai ganin irin dirin da Allah ya yi mata, don duk yanda ake ko a kyawun dirin jikinta ta san idan Meema ta ara wasu shekaru biyu zuwa uku nan gaba, komai na halittar jikinta fitowa zai yi wanda kuma hakan fa ar mata da gaba ya ke. Idanun Meeman ta kalla ganin yanda zararan gashin giranta suka kwanto saboda tsayin su kamar artificial. "Wanene kai? Kana ina don girman Allah??" Laushi ta fa i a kan la anta tana kallon fuskan Meeman sosai. A hankali Meema ta bu e idanunta tare da fa in, "Mummy, da wa kike magana??" Hannu Laushi ta kai tare da shafa kanta sannan ta ce, "Ina kallon fuskanki ne ko Allah zai saka in ga kamannin mahaifinki a fuskanki har Allah yasa in gano shi." Wani murmushin Meema da baccin ya aurace a idanunta ta yi tare da fa in, "Mum, ki kwantar da hankalinki. Ke ka ai ma kin ishe ni, yanzu ban ma so in san wanene babana. Ko da can da nake damun ki saboda abunda kike yi ne da maza, wallahi mummy ji na ke kamar in cakawa duk namijin da ya ta a jikinki wu a a nan," ta arisa maganar tare da nuna ramin ma oshinta. Kallonta kawai Laushi ke yi without blinking. Tun Meema na da rai years, Laushi ta fahimci ita yarinya ce mai matu ar wayo kuma bata mance duk wani abu da ta saka a walwarta. A yanzu haka idan Meema na tuno mata wasu abubuwan da suka faru tun tana da five years a duniya, abun matu ar mamaki yake bata. Shafa fuskarsa ta yi tare da fa in, "Za ki yi lattin zuwa school, ki tashi ki wanka don yau ba aunty Ladi ko Uncle Salma bane za su kai ki, ni da kaina zan kai ki." a kai Meema ta yi tare da sauka a kan gadon ta nufi bayin da ke cikin akin. Da idanu Laushi ta bita har ta shige ta rufo ofa. _Abuja_ Gaba aya akin a cike yake babu masaka tsinke kasancewar rabi da kwatan Ar o Barkin o ne a cikin akin don ma wasu ba garin suke ba sannan ananun yara daga masu shekaru sha biyu zuwa asa ban da su a wannan taron. Amma tun daga kan baffanni, iyaye mata, annai, yayyai da wasu daga cikin manyan jikoki duk suna wajen. Tsit akin ya auka sakamakon isowar Babiyo hannunsa ri e da golden stick insa kuma fuskansa a murtuke kuma a ace, wanda karyar duk wani mai shekaru hamsin zuwa asa ya ce ya ta a ganin bayyanar acin ran Babiyo har ya nuna a fuska haka. Don shi ka'ida a yanayin zamansa ko gyaran muryansa ake fahimtar acin ransa. A bayansa Mamiyo ce, sai dai ita tata fuskan babu yabo babu fallasa, domin shi ba a aure yake ba, kuma shi ba murmushi bane a samansa. Babiyon ne ya soma zama akan kujerarsa ta sarautar Ar o Barkin o ya wani karkace ka an tare da watsa hannayansa a saman hannun kujeran yana kallon kowa ai da tsananin acin ran da ya haddasa cikkunan mutane da dama da ke zaune a wajan mur awar tsoro. Zama Mamiyo ta yi a nata kujeran tana an sakin murmushi a kan la anta don tabbas ta san yau a kwai tashin hankali ganin yanayin Babiyon da ko ita sau aya ta ta a ganin haka a iya zaman da suka yi, kuma ba aramin hukunci ya yi ba a wancan lokacin da ya girgiza uban kowa da ke cikin Ar o Barkin "A bu e taro da addu'a a ta aice!" Fa in Babiyo a kausashe wanda ya saka kusan su duka agowa suka kallesa don kowa ya san Babiyo dai ya fi son doguwar addu'a. Nan da nan akai addu'ar aka shafa kowa na jiran jin bayani daga bakin Babiyo da kuma irin hukuncin da zai aiwatar a yau. "A jiya, ashirin da aya ga watan Nuwamba, dubu biyu da takwas, an samu wani mara albarkan ya shigo har Ar o Barkin o kamar yanda wasu suke tunani, domin cutar da jikana wanda da badan Allah ya yi yana da tsawon rai da kuma sauran shan ruwansa a duniya ba, da yanzu haka wani zancen ake yi. To ina son kowa da ke cikin akin nan ya saurare ni da kyau! Wallahi, Tallahi, thumma Billahil azim ba zan kyale duk wanda ya yi wannan yun urin ba, walau a wajen Ar o Barkin o ya ke, ko kuma a cikin Ar o Barkin o kai ko a wata duniyar ya ke, sai na bincikosa kuma abunda zan yi......" Yana kawo nan ya wani cije le e tare da girgiza kai yana buga golden stick insa a asa rai ace. Baffa Jibrila gangan jiki da ruhinsa wani irin kakkarwa suka shiga yi don ji ya yi kamar kai tsaye Babiyo da shi ya ke magana. Duk da Acn da ke akin wani irin zufa ya ke yi. Mamiyo kuwa, duk arfin zuciya irin nata sai da ta girgiza tare da tsoron kalaman Babiyon, don tunda ya furta, sai ya binciko kamar yanda ya yi alwashi. Hankalinta ne ya yi wani irin mugun tashi, duk wani farin ciki da ganin ita ce da nasarar da ta shigo da shi nan take ya yi fitar bindiga.. Dogon numfashi Babiyo ya ja tare da cigaba da fa in, "Abdul-Hameed babu abunda zai same shi da izinin ubangiji, kuma ko ina da rai, ko ban da shi, in Sha Allah har shugaban asar Nigeria sai ya yi!" Dumm gaban Baffa Jibrila ya sake bugawa da arfi, zuciyarsa har wani tsalle take yi kamar za ta faso irjinsa ta fito ganin kamar shagu e Babiyon ke masa. Mamiyo kuwa tsabar yanda maganar Babiyo ya dake ta wani suman wucin gadi ta yi a nan zaune. Don ji ta yi kunnuwanta sun yi mata wani dummm, can kuma ta koma ji shuuuu a cikin masarrafin jinta kamar rediyon da aka daukewa wuta. Ta kusa mintuna uku tana jin haka kamun komai ya saisaitun mata har ta soma tsinkayan maganar Babiyo ta gaba. "Abu na biyu kuma, tambaya nake son yi shin yaushe Estate ina ya zama dandalin tashin hankali da ananun magana? Shin na mutu ne, ko kuwa ban da amfani ne da har ke, Samira yaushe har wuyanki ya yi kaurin da za ki wanke afafu ki tafin gidan Gi o kina ciwa matarsa mutunci?" Jikin Aunty Samira rawa kawai ya ke yi ta kasa ko agowa ta kalli Babiyon don sai yanzu dana sanin rashin mutuncin da ta yi wa mama Halima ya zo mata. Mama Halima da ke gefe kuwa, babu abunda take yi sai hawaye. Haka angaren amarya Mardiya ita ma da sai daga baya ta samu labarin sharrin rashin zuwanta gidan miji da duburci ya same ta. Shima aunty Aunty Samira ce ta saka ta a aki tana bincikarta domin ta ji gaskiya. Anan ita kuma ta yi mata rantsuwar ko fuskan mijin ma bata gani ba balle har ya kusance ta. Hakan ne kuma ya tunzura Aunty Samira take ganin kamar shirin Mama Halima ce saboda kishi. Jawaad kuwa kansa ya ri e sosai yana jin takaicin wannan banzar al'adar tonon asirin sirrin auren da har yanzu aka kasa daina yi a cikin familynsa, don ya san tabbas sai Babiyo ya magantu a kai kuma a gaban wa anan umbin jama'ar. Habibu kuwa tunda ya saukar da kansa asa bai ago ba sai hawayen da ya ke ta tsiyayarwa ganin abunda ake son yiwa mahaifinsa da mahaifiyarsa kuma duk ta silarsa. Baffa Gi o kuwa tagumi ya zabga yana kallon tiles in da ke shimfide a asa idanunsa sun tara hawaye yana jin zafin Habibu cikin ransa don gani ya ke duk shi ya jawo masa wannan abu gashi yau za a titsiyesa gaban yayyi, annai, a, surukai da kuma wasu daga cikin ansa (Jikoki) da suka tasa. Shi kansa cike ya ke da mamaki ta yanda a kai kwarya ta fashe bayan shi ya san ko yatsan Mardiya bai ta a ba, infact ma ko fuskanta bai gani ba a daren jiyan........... (Wohoho! Ku gyara zama tare da kimtsawa don yanzu gwaramar zai soma. Wani shiri Yasaar ya yi a kan Laushi da
Chapter 60 · 0% Book details