← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 143

Sashe 4

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

zuciyar salama Laushi ta yi. Don ji ta yi kamar an zare mata aya. "Ca ! Tun da nake kar an haihuwa lokacin ina amsa sunan unguwar zoma, ban ta a cin karo da ba ar jaririya kamar wannan a ba. Wai! Duna. Sunan wani ba in kare." Fa in Hajja Lanti bayan ta yanke cibiya da sabuwar rezar da ta shigo da shi lokacin da ta je auko handgloves. "Kin ga uwar ma ta biyo baya. Gaskiya awar nan ta ki ta taki Sa'a. An tsallake rijiya da baya." Ta sake fa i tana mai kwaso jini a jikin Laushi wanda ke fitowa guda-guda. Ladi katifa kuwa urawa jinjirar idanu tayi tana so ta hango kamanni Laushi ko aya a jikin jinjirar. Sai dai babu ko aya. Don ko dogon hancin jinjirar ba irin na Laushi bane. Jinjirar ta fita hanci sosai.. Hajja Lanti ta gama taimaka mata ta mi e tare da cire handgloves ta jefar a nan tsakar gidan tare da kallon Ladi katifa ta ce, "Ki same ni a aki idan kin gama kimtsata uwar. Ita kuma ar zan turo Salma yanzu ta zo ta kar e ta ta yi mata wanka." "Mun gode sosai Hajja Lanti. Allah ya ara miki tsawon rai kici karenki babu babbaka." Fa in Ladi Katifa. Ba tare da Hajja Lanti ta kuma furta wani abu ba ta fice daga akin tana mai tsirtar da yawu a bakin ofa, a cewar ta jinin Laushi matukar arni ne da shi. Babu kayan jarirai da Laushi ta tanada ko aya. Hakan ya sa Ladi Katifa auko sabuwar zaninta ta lullu e jinjirar tare da kwantar da ita. "Ah! Kice haihuwa akai mana cikin gidan nan. Gaskiya kam akwai buduri. Gaskiya wannan karuwa ta shigo da afar dama. Eh mana! Ai dole na fa i haka tunda har kece da kanki kika kar i haihuwar. Bari kiga in gyara jikina in canza auduga don abun namu na mata nake yi." Fa in Salmanu an daudu da yayi saurin tarar Hajja Lanti yana rausaya tare da kwance zani yana ara aurawa a irji bisa dogowar farar jallabiyar dake jikinsa. Dafa shi Hajja Lanti ta yi tare da fa in "Ki saurareni da kyau Salma Nice. Wannan ba in ne da suka so jiya ce aya daga ci ta haifu. To so nake ki amshi jaririyar ki wanke ta tas. Za ki samu kaso mai tsoka." Wani irin uwar guda Salmanu an daudu ya saki tare da kwance zani ya kuma aurawa sannan ya ce, "Ke duniya! Ni wallahi ma duk sai naji kunya ta rufe ni. Ni da ko haihuwar fari ban yi ba, amma nice yau da wanke jinjira. Ko da yake, ai aikina ne. Don billahil lazi ba zan iya irga maki cibiyoyin jariran da na yanke ba. Kuma masu jegon ma ni ke wanke su sumul da ganyen dalbejiya sannan kuma nayi masu gashi. Ke wani lokacin ma haka zaki ga an buga uban layi ana jiran Salma nice ta amshi haihuwar mata. Unguwar zoma ce da kike gani na nan. To menene a ciki? Duk jinsi aya muke ai." "Kiyi maza kizo ki amshi sabulun salo ki wanke iyar tass. Za dai kiga jaririya." Hajja Lanti ta arisa maganar tana mai fashewa da dariya sannan ta nufi akinta. Salmanu an daudu kuwa; kai tsaye ya nufi akin da su Laushi ke ciki tare da kama ugu da hannu aya, aya hannun kuma ya dafe jikin ofar akin tare da fa in, "Gafarar ku dai. Zan iya shigowa? To menene ma abun tambayar izinin shigowa tun da dai duk jinsi aya muke. Salma nice ce!" Ya arisa maganar yana fari da idanu. _MATAR SAYYADEE_ 08128755583 *SHARE FISABILILLAH!* [1/28, 8:52 PM] Rahamanatu: *_MY DESTINY_* ( ~ addarata~) *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee Page 3
Chapter 4 · 0% Book details