← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 143

Sashe 63

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

PM] Matar Sayyadee: *_MY DESTINY_* ( ~ addarata~) *Zulfa'uerr Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee *ZAFAFA WRITER'S ASSOCIATION* ( *Forum of intelligent and non-vulgar writer's of the nation*) ```Takenmu shine unkasa cigaban adabi!``` `We aren't only writing for entertainment but rather we use our pen to highlight some of the challenges faced by women with a view to finding solutions to them.` Page 36 *For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisa gaskiya* *_Don girman Allah zan sake fa i, masu tambayata ta private akan in ba su daga farko, ku yi joining domin samun labarin addarata daga farko. Na yi nisan da ba zan iya turowa daga farko ba. Thank you!_* *For those asking from the beginning, follow this link to join the group don na yi nisan da ba zan iya turowa ba.* "Madam mai ke faruwa? Ki min bayani. Ina yarinyar mutane?" Informer ya fad'i hankalinsa na tashi ganin ganin yanda shugabar makarantar gaba daya ta rud'e. Kasancewar akwai CCTV camera a lungu da sak'on makaranta saboda tsaron yara, sai kawai ta hannunsa suka nufi wani d'akin computer. Maza shida ne a cikin d'akin ko wannen gaban computer ya ke. Ku tariyo min abunda ya faru a office dina da kuma school premisses mintuna talatin da suka wuce" shugabar makarantar ta fad'i cikin harshen turanci. Cikin k'ank'anin lokaci suka yi abunda ta umarta, sai ga hoton Yasaar zaune gaban shugabar makarantar yana koro zancen k'anzon kurege tare da nuna katin shaida ta k'arya. Umarta ta kuma yi da su zuk'o mata katin pass d'in da ya ke nuna mata, ko da aka zuk'o babu wani bambamci tsakanin wanda ya nuna da wanda ke hannun informer. Har hoton harabar makarantar sai da aka hasko lokacin suna yiwa Meema rakiya ita da classroom teacher d'in su Meemar. "Damm it!" fad'in informer yana mai buga teburin da k'arfi sai da shugabar makarantar ta razana. A fusace ya fice daga computer room d'in ya bar makarantar gaba d'aya yana tunanin yana tunanin ta yaya zai fad'i wannan mummunar zancen ga ubangidansa, uwa-uba kuma ita uwar yarinyar. _YASAAR_ Yana barin makarantar ya d'auki hanyar wani unguwa mai nisa wanda babu wanda ya san wajen sai shi d'aya sai kuma yanzu da zai kai Meema tare da abokin cin mushensa. Babu abunda ke kwance a fuskansa sai murmushi. Tafiya ce Mai d'an tsayi suka yi sannan suka iso gidan. Sauka ya yi a motar tare da isa k'ofar gidan. Mukulli ya saka ya bud'e gate d'in sannan ya koma cikin motar ya tada ya shiga cikin gidan ya yi parking. "Kulle mana gidan, bari na shiga da yarinyar nan ciki. Gobe-goben nan za ta bar k'asar nan don ba ni so a zo a samu wata matsala" Yasaar ya fad'i yana mai mik'a masa key d'in gidan shi kuma ya zagaya ya ciccib'i Meema da tun barin su harabar makarantar ya fesa mata wani abu a fuska ta b'ingire da bacci. Karb'an key d'in abokin nashi ya yi, shi kuma ya nufi cikin gidan Meema sab'e a kafad'arsa. Bayan mintuna kad'an abokin nashi ya shigo d'akin tare da fad'in, "Ya turo maka kud'in ne? ka ce min in pound zai turo ko? Akwai shagali fa abokina! Ya k'arisa maganar yana mai mik'a masa hannu suka tafa suna dariya. "In dollar ne. Ya turo min kafin alk'alami dala miliyan d'aya, sauran dala miliyan d'ayan kuma sai Meema ta isa Colombia. Ka San mai nake so da kai abokina? Wani aiki zan baka don Allah, so Ladi katifa na ke so ka san duk yanda za ka yi ka d'auko min ita kamun hukumar NDLEA su isa can gidan Laushi, don na tabbata idan muka kwamusheta za ta iya bamu bayanin inda Laushi ta gudu ita tsinannan da ya taimaka mata suka gudu. Wannan shine hotonta" ya k'arisa maganar tare da mik'a masa hoton Ladi katifa. Karb'a ya yi tare da k'arewa hoton kallo sannan ya ce, "Shegu! wallahi zafafa ne matan nan amma kuma karuwan banza. Yanzu ko za ka ga aikin da cikawa, don na San tabbas ko wani irin lokaci hukuma za ta iya isa gidan tun da ka riga ka gama shirinka" ya k'arisa maganar yana mai kashe masa ido d'aya tare da mik'ewa ya wuce. _SABO DA KAZA_ Kwance ya ke a guest house d'insa shi da sabuwar karuwarsa da ya yi suna bacci bayan gama masha'arsu, ko kaya babu a jikkunansu sai bargo da suka lullub'e. Burum! suka ji an bugo k'ofar da k'arfi an Kuma shigo. A firgice suka farka dukkansu. Gaba d'aya sai su Kai arba da hukuma zagaye da gadon kuma sun nuna su da bindigu. Mamaki ne ya kusan sumar da Sabo da kaza, don a iya saninsa mutane biyu ne kawai suka San da zaman wannan guest house d'in daga Laushi sai Sabo da kaza. Wani mummunar b'acin rai ne ya shiga turnik'esa yana fatan ba abunda zuciyarsa ke raya masa bane, dan kuwa hakane; to babu abunda zai hana shi kashe Laushi har lahira bayan gana mata mummunar azaba, wannan ita ce alk'awarinsa. Cike da isa da tak'ama ya hau magana a zafafe "Wani d'an iskan ne ya ba ku damar shigomin har nan Kuna nuna ni da wasu matsiyatan bindugunku da basu wuce mashin katako ba a wajena? Kun San ko ni wanene?" ya k'arisa maganar a hassale. "An ba mu izinin kama ka sakamakon miyagun kwayoyi da muka kama dumu-dumu a cikin gidan nan, Sannan za mu tafi da Kai har can gidan da ka sayawa karuwarka domin ka rik'a safarar makamai da hodar iblis, wannan shine IDcard d'ina, wannan Kuma takardar izinin kama ka. Don haka salin alin ka bamu had'in kai asirinka a rufe mu bar gidan nan da kai ko Kuma mu wulak'antaka," d'aya daga cikin su ya fad'i hakan rai b'ace. Wani mugun miyau mak'ot! Sabo da Kaza ya had'iye zufan tashin hankali na tsattsafowa tun daga tsakiyar kansa har wuyarsa. Cike da dakewa ya furta, "Ina buk'atar privacy domin tsaftace jikina!" Taku biyu jami'in ya yi tare da tattare duka wayoyinsa da ke kan mirror ya rik'e a hannunsa sannan ya umarta jami'an da duk su fice su bashi damar suturta jikin nasa kamar yanda ya buk'atar. Suna fita, a gaggauce ya sauko daga kan gadon tare da saka kayansa Sannan ya nufi wata drawer ya d'auko biro da takarda ya rubuta wasu numbers guda uku ya mik'awa karuwarsa tare da fad'in, "Kina fita ki kira wad'annan numbers guda biyu ki fad'a masu Sabo da Kaza ya ce su san takunsu zance ya b'aci. Wannan d'ayan kuma number d'in yaron aikina ne, Yasaar. Ki kira sa idan ya d'auka ki ce na ce ya nemi ajiyarsa a duk inda take ya cika muradinsa fiye da yanda ya ke kissimawa a zuciyarsa. Ki bud'e waccen drawer d'in ki d'ibi adadin kud'in da kike so ki wuce. Ki tabbatar dai kin yi duk abunda na umarce ki da ki yi!" Ki fita babu abunda za su miki, ni kawai suke da buk'ata." Gyada Kai kawai ta rik'a yi don a mugun tsorace ta ke. A gaggauce ta saka kaya a jikinta tare da d'aukar jakarta ta nufi drawer ta kwashi kud'i ta saka a jaka sannan ta nufi k'ofa ta fita. Tana bud'e k'ofar gaba d'aya jami'an su Kai saurin pointing d'inta da bindigu. Ba su ba ta damar tafiya ba sai da suka caje jakarta tsaf, ganin babu wani abun zargi sai suka jefa mata jakarta tare da nuna mata hanyar ficewa daga d'akin. Kamar iska haka ta fice gabanta na fad'uwa. Tasa k'eyar sabo da Kaza su Kai bayan sun buga masa ankwa a hannu da k'afa. Da idanu ya rik'a bin hodar iblis d'in da ke tule a parlour sai d'aukar su hoto jami'ai suke da camera. Wani uban kwafa ya buga cikin zuciyarsa da ke masa tuk'uk'in bak'in cikin da ya ke tunanin Laushi ce silar tonuwar asirinsa. Can gidan da ya sayawa Laushi suka nufa inda nan ma d'in Jami'an tsaro ne zagaye da gidan basu samu kowa a gidan ba, b'alle gate d'in suka yi bayan isowar sauran jami'an tsaron tare da Sabo da kaza. Kaf d'akunan sai da suka hargita, kitchen da toilet ma duk ba su bari ba sai dai basu samu komai a ciki ba sai a d'akin sirri Wanda suka b'alle da kyar. Numfashinsu kusan tsayawa ya yi ganin manya-manyan makamai masu hatsari har da bomb. Nan da nan suka shiga d'auka a hoto tare da video Sannan suka kira y'an jarida. Ladi kuwa, fita su kayi ita da Salma nice domin sayo kayan abinci a kasuwa kasancewar na gidan ya yi k'asa sosai. Tun daga farkon layin suka fahimci akwai matsala, ganin matsalar a k'ofar gidansu ce, sai suka umarci taxi driver d'in da ya d'auko su da ya mik'e k'asan layin Sannan ya b'ullo layi na gaba da zai mayar da su asalin bakin hanya. Waya Laadi katifa ta lalubo da sauri ta shiga neman layin Laushi. Sai da ya yi ringing har ya kusa katsewa Sannan Laushi ta d'aga kiran tare da fad'in, "Na shiga uku Laadi!" Yanda Laushi ta kira sunan Laadi sai da hakan ya saka gabanta ya wani irin harbawar ninkuwar tashin hankali. "Zinatu kina Ina? Don girman Allah kar ki ce min kina cikin mugun hannu. Wayyo Allah ni Rakiya! Ta k'arisa maganar tare da d'aura hannunta d'aya a ka ta fashe da kuka. Nan da nan Salmanu d'an daudu da ke gaban mota shima hankalinsa ya yi mugun tashi. "A'a ban mugun hannu amma kuma tashin hankali da damuwata, Meema! Ban san ko a wani hali take ciki ba. Yasaar ne ya kawo min farmaki lokacin na fito daga makarantar su Meema, kuma ga dukkanin alamu wannan karon dani ya ke son yi garkuwa. Wani wanda ban sani ba ya kawo min d'auki ya cece ni daga gare sa.Yanzu haka ya kawo ni wani k'aramin masaukin bak'i wanda ban san ko a ina yake ba. Amma mun yi nisa sosai daga cikin garin Lagos. Shi kuma Wanda ya cece ni ya tafi makarantar su Meema domin d'auko min ita, mun yi waya da shugabar makarantar ma yanzu. Ta kira domin
Chapter 63 · 0% Book details