Sashe 80
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lami o ya ce wani abu, sai ga su sun shigo da gajerun wandunan da shirt na makaranta. afarsu da sanye da takalmi masu igiya. Wani irin waro idanun tsoro da tashin hankali mahaifin Lami o ya yi jin jikokinsa na turanci (kun san dai idan bafulatani ya ji turanci yadda yake karya harshe musamman ma ace turawan da kansu suka koyar dasu). Jiki na rawa ya mi e tare da nuna Lami o da hannu ya shiga fa in, "Ni za ka ciwa amana Lami o? Jikokina za ka tura wajen yahudawa suna koya masu yaren kafurci da kafurci! Ka cuce ni ka cuci rayuwarka da na anka Lami o. Allah ya isa tsakanina da kai Lami o! Allah ya isa!!" ya kuma fa i yana sharce hawaye. Hankali tashe Lami o ya ri o hannun mahaifinsa yana son ya masa bayani amma sai ya wancakalar da hannun tare da fa in, "Idan har kana so ni da kai mu daidaita, ka cire annan a makarantar Arna ka tattara inaka-inaka mu koma Mayo-Belwa a yau innan kuma a yanzu, idan kuma ba haka ba, babu ni babu kai, ban yafe maka ba ka ara zuwa Mayo-Belwa kuma ka kira ni mahaifinka, dukiyarka kuma zan saka annanka su tattaro su dawo maka da ita!" Wani irin fitinanniyar zuciya ta soma yun urowa Lami o wanda gada ya yi a wajen mahaifin nasa sai kuma ya zarta shi. Ko tari ya i yi balle kuma ya furta wani magana akam abunda mahaifin nasa ya furta. "Zan au shurunka matsayin bijirewa umarnina, idan kuma na saka afata na bar gidan nan a yau kuma a yanzu, ni Isiyaka na cire ka daga cikin sahun ana!" Duk da jin wannan furuci ko gizau Lami o bai yi ba har mahaifin nasa ya juya fuuu hannunsa ri e da na Musa da ke tsiyayar hawaye suka fice. Tafiyar da Lami o bai kuma saka mahaifinsa a idanu ba, domin kuwa kwana bakwai da tafiyarsu an fashi suka shiga auyen suka kora duk dabbobin jama'a tare da kashe mutane takwas, daga ciki akwai mahaifin Lami aninsa Jafaru, mijin anwarsa Lawisa da kuma wasu daga cikin mutanan auyen. aramin tashin hankali da kukan fitar hayyaci Lami o ya yi ba lokacin da ya yi arba da gawan mahaifinsa da aninsa har ma da mijin anwarsa ya yi ba har sai da ya zama abun tausayi. Bayan bakwai, Lami o ya tattara wasu daga cikin dangi da suka amince za su biyo sho tare da aninsa Musa da anwarsa zuwa cikin garin Yola inda ya ke a zaune. Sai dai wasu in biyo shi su kai a cewarsu ba za su bar mahaifarsu ba duk da kuwa ba su da wata sauran dukiya a garin. Shi kuma Lami o dukiyar da ya tafi da ita Yola, sai Allah ya saka masa albarka suka ru anya wa an fashi suka tafi dashi har da na mahaifinsu (gadonsu) wanda shi ma yana da dukiya sosai. Bayan dawowarsu Yola, Lami o ya ha a kan duk wasu yara an uwa tare da anwarsa ya saka su makaranta duk da wasu da yawa a ciki ba su so ba, amma babu yadda za su iya don ba aramin shakkarsa su ke ba har da wasu daga cikin annan mahaifinsa. Haka rayuwa ta cigaba a gidan Lami o, bai ta a gajiyawa ba wajen ciyar da dangin nasa ba, kuma dukiyarsa ba ta ragewa sai ma bun asa take. Eka hu u gare shi a nan cikin unguwar da ya ke noma da kuma aje dabbobinsa. Gidansa kuma da yake ciki, gine-gine ake ta yi a cikinsa saboda mutanan da suka cika gidan. Kowani magidanci da sasansa shi da iyalansa. Kuma bayan a uku da Hure ta haifa, Sakina ta, haifi aya ba a kuma sake haihuwa a gidan ba sai bayan shekaru goma Sakina ta sake haihuwar a namiji mai suna, lokacin shekarun Ar o sha takwas a duniya. Bai ma gida lokacin da aka haifi Safiyanu aninsa, yana Makaranta a Abuja da mahaifinsa ya kaisa yana karanta kasuwanci. Duk da, Lami o shi bai ta a yin boko ba, yana matu aunar boko don babu wanda bai boko a cikin gidansa. Ga aya gidansa ya zama na an boko daga matan har maza. Kuma ya cusa masu wannan ra'ayin a cikin zuciyarsu amma kuma duk da hakan, hakan bai sa ya ta a tarbiyarasu ba. Don doka ne a gidan duk wanda aka sama da laifin fasi anci (zina), sata ko kuma ha'inci da zanbo cikin amana, hukuncinsa korar mutun ne daga zuri'ar har abada. Kuma kowa taka tsan-tsan yake da wannan doka. Don kamar yanda suke karatun boka hake suke na addini ko ince fiye ma da haka. Watan Safiyanu biyar a duniya, Allah ya auki rayuwar mahaifiyarsa sakamakon zazza in kwana aya. Sosai mutuwar ta bigi kowa don Sakina mata ce mai sau in kai da biyayya. Ri on Safiyanu sai ya koma hannu Hure mahaifiyar Ar o. Dama kuma tun can Firdausi akin Hure ce, sai ta rungumesu duka ta ha a da nata an ta cigaba da ri o Barkin o da ya tashi yin nasa gadon, sai ya dame kakansa da mahaifinsa a zafin zuciya da halin ri au duk da kasancewarsa cikakken an boko. Shi dariya ma ba al'adarsa bace sam, hakaa duk wani kani nasa wanda suke uba aya da ma cousins insa ba aramin tsoro da shakkarsa suke ba. Bayan shekaru biyu da mutuwar Sakina, Hure ma Allah ya amshi abinsa bayan jinyar da ta yi na tsawon wata bakwai sakamakon daji da ya fito mata a mamanta. Kusan fita hayyaci Lami o ya yi, don shi zai iya cewa Allah ya azurta shi da mata masu biyayya. Haka Ardo ya yi kuka sosai da mutuwar mahaifiyarsa. Kuma lokacin bai wani jima da kammala degree insa ba, don ko wata biyu bai yi ba. Shi ya cigaba da kuwa da Safiyanu, wankansa da komai nasa, don sosai ya ke son yaron. Komawarsa Abuja ne rainon Safiyanu ya koma hannun Inna biyu, matar anin babansa (Musa). Don shima ya yi aure har da a uku. Ita ma Lawisa autar su Lami on ta sake aure a nan cikin Yola, sai dai an tsohon mijinta suna nan a gidan Lami Dalilin dawowar Ar o Abuja kuwa, aikin gamnatin da ya samu ne a wata aramar ma'aikata. Sai dai bai tsaya a haka ba, fa awa kasuwanci ya yi ka'in da na'in sakamakon jari da mahaifinsa ya bashi. Kamar wasa ya bu aramar ma'aika da ke yin madarar yoghurt ta gora mai suna Barkindo fresh yoghurt. Ai kuwa yoghurt in ba aramin kar uwa ya yi ba, don a wannan lokaci kaf Abuja babu yoghurt kamarsa. Ganin yogurt in ya karbu sai suka sake inganta shi. Da na aramar gora kawai suke yi, sai suka soma yin na babban gora litre-litre, Ice-cream da ruwan ruwan gora. A wannan lokacin kuma ya ha u da first love insa Maimunatu wacce itama bafulatana ce ta Yola a aramar hukumar (Girei). Soyayya suka kai mai tsafta da tsananin sha uwa wanda ta kai su ga aure. A nan cikin abujan su ke da zama in da ya sayi wani gida four bedroom. Shekara bata cika ba Maimunatu ta haifi anta kyakkyawa mai kama da mahaifinsa. aramin biki aka yi ba domin mutanan Yola sun zo har da Lami o mahaifinsa kasancewar bikin sunann an ha a ne da bikin bu e katafaren kamfaninsa mai suna `Ar o Barkin o Global Company Limited`. Ranar suna yaro ya ci sunan kakansa babansa wato Abubakar amma suna kiransa da aleri. Sosai Allah ya sawa company in albarka, domin kuwa a shekaru uku kawai sun cimma nasara, don company in har suger, spaghetti, maccoroni, magi, gishiri, spices, flour suke yi. Abun mafi farin ciki kuwa, wani shahararren mai ji da ku i Abdurraza Usman Chawai ya zuba hannun jari a company wanda shike da rinjaye na shares Wani tan ameman Estate Ar o ya shiga ginawa domin shi da duk iyalansa. Don ba karamin estate bane. Babu abunda babu a ciki, makaranta, asibiti, kasuwa, masallacin juma'a da sauransu. Maimuna ta kuma haihuwar a namiji mai suna Abdul-Azeez (Bel o). shima bai cika shekaru biyu cif ba, ta kuma haifan Huzaifa (Gi o) kuma a wannan lokacin ne Ar o ya kuma ha uwa da matarsa ta biyu, wacce ita ma dai bafulatanar ce amma ta Yobe mai suna Lauratu, ta fito ne a gidan masu matsakaicin arfi. Ta kasance mace mai izza, mugun hali, makirici da son kasancewa ontop tare da burin komai ya zamo nata. Tun shigowarta gidan Maimunatu ta fuskanci ba abokiyar zama bace sam. Don sau hu u tana ha a su, gagarumar fa a ita da Babiyo. Haihuwar da take a kai a kai ya kuma fasa mata kai, domin cikin shekaru biyar ta ajiye a har hu u; Tukur, lawal, Mahmud da Jibrila. Hakan ya sa take ganin ai ko yau Ar o ya fa i ita ce da rabi da kwatar dukiyar gidan. Sai dai ita ma shekarunta biyar aka dan aro mata kishiya, ita ma dai ar Girei ce, iyayanta sun san juna da iyayan Maimunatu. Sunanta Latifa (Inna Jume) a biyu ta haifa Maryuda da Huzaifa (Huzaifa biyu babiyo ke da shi. Da mahaifin Habib da mahaifin Jawaad, amma suna da bambamcin sunan gida. Baban Jawaad bobbo ake ce masa, shi kuma baban Habib Gi Sai matarsa ta hu u, Karima (Inna arama) aya ta haifa Yunusa (Baffa Modibbo na Lagos mahaifin Marwanatu). aramin mulki Lauratu (Mamiyo) ta ke zubawa a gidan ba. Dom ma Ar o na taka mata birki, don har shika aya ya ta a shiga tsakaminsu, dakyar da su in goshi ya dawo da ita. Tun daga nan ta shiga hankalinta, sai dai wani mummunar iyayyar matan Ar o da ansa ya huda zuciyarta har ta yi nasarar cusawa anta. Sai aya bai isa ya nunawa aya ba saboda sanin halin mahaifinsu. Akwai biyayya da mutunta juna sosai a tsakaninsu ko da kuwa kwana aya ne a tsakaninsu. Tashin hankaline ya samu zuri'ar Ar o Barkin o sakamakon rasuwar da Baban Ar o (Lami o) ya yi. Gaba aya suka