← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 143

Sashe 24

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ta yi ta soma zagaye akin tare da dun ule hannunta tana naushin ayan hannun. Dogon tunani ta shiga yi ta yanda _Sabo da kaza_ ya yi mata farin sani haka. Sam ta mance da ciwon da ke goshi da kuma damtsenta duk da jinin ya bushe a jikinta har zuwa rigar da ke jikinta. "Duk da ni ban ta a yarda da mutum, amma ina ji a jikina sam ba Ladi Katifa bace za ta yi leading Sabo da kaza zuwa garinmu. To amma idan ba ita ba a nan garin Lagos wanene ya san ni haka? To kuma ai Ladi bata san na kashe Abbanmu ba," Laushi ke wannan maganar a bayyana tana zaga akin. "Zai iya yiwuwa da ya samu brief labarinki a wajenta sai ya tafi can domin bincike. Maybe a nan ya samu cikakken labarin tunda doge washa garin ranar da na cakawa Abbanmu wu a a ciki magana ta bayyana tunda a gaban yayata Maryamu komai ya faru," wannan karan a cikin zuciya ta yi maganar. Ta jima tana sa a da warwara. Sai dai duk inda ta kawo zargin Ladi Katifa sai ta ji wata zuciyarta tana arin aryata ta saboda It's been 14years kenan da ha uwar su kuma bata ta a kama Ladi Katifa da arin cin amanarta ko munafuntarta ba. "Anya ban ebo ruwan dafa kaina ba kuwa ni Zeenah? Wannan shi ake kira reshe ya juye da mujiya. Amma duk da hakan ba zan yi giveup ba. Zan bisa a yanda ya so. Sai dai idan ya san wata to bai san wata ba. Makircin mace ya fi na shai an don ko shi tsoranmu ya ke," ta fa i cike da bawa kanta kwarin guiwa tare da shiga bayi.. Tana fitowa wayar da Sabo da kaza ya bata ya hau ringing. Towel ta kai ta share ruwan da ya gangaro daga goshinta sannan ta nufi kan gadon ta auki wayar tare da picking ta kara a kunne, "Hello, ina ji!" Ta fa i a dake duk da ta san mai kiran. "I like your confidence! Sai dai ki sani, duk motsinki a tafin hannuna yake. Zan dawo anjima saboda wani aiki da ya tsayar dani. Ki gyara min kanki da kyau sai na dawo Hajiya Laushi," it ya kashe wayar ya barta da sakakken baki tana kallon wayar. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Na shiga uku ni Zeenah. Bi diddigi ya saka min kenan?" Ta fa i maganar tana bin akin hotel in da kallo daidai lokacin da aka yi knocking ofar akin. arisawa wajen ofar ta yi tare da mur awa ka an. Ganin saurayin azu ne hannunsa ri e da hannun Meema, sai Ladi Katifa da kuma Salma nice da ke bayansa ri e da aruwar akwatin kayanta da na Meema. ofar ta yi da sauri ta basu hanya domin shigowa. Kallo aya saurayin nan ya mata ya kawar da kai domin aramin towel ta auro a jikinta, santala-santalan cinyoyinta duk a waje, don tana du awa mazaunanta za su bayyana. Shi kuma saurayin zunubi ne a gare sa ya kalli abun hutawar mai gidansa. Da gudu Meema ta isa wajan uwarta ta rungume tare da soma hawaye ganin yanka a can saman goshinta. "Mai ke faruwa Laushi? Mai yasa kika turo a auki Meema?" Fa in Ladi Katifa kuma kusan a tare suka yi maganar da Salma nice. "Uhm! Allah ya ta aita min wahala ne da yanzu ina kan gadon asibiti ko kuma ana shirye-shiryen kai ni kabarina. Don wallahi ba aramin duka na sha ba a hannun matar Alhaji Nura da yayarta ba. Na ci wuya Katifa," fa in Laushi tana mai kai hannu kan goshinta. "To duk garin yaya a kai haka? Kuma ke kika tsaya? Gaskiya kin ban kunya. Sai ka ce ba ar bariki ba!" Ladi katifa ta fa i cike da takaici. "Bari! Bari Ladi!! Sarkin yawa ya fi sarkin arfi. Su biyu fa! Ai wallahi na ma yi namijin ari," ta fa i tare da bu e akwatin da Salma Nice ya ajiye a tsakar akin ta fiddo pant da bra da kuma wata doguwar riga mai hula sannan ta rufe akwatin. "Ni ba kiga na kasa magana saboda takaici ba? Ai wallahi zuciyata tafarfasa take akan wannan cin mutuncin da a kai wa uwar akina.. Mtsw (Tsaki) wallahi takaici nake saboda azu ba muyi mata dukan sakwara tare da karya afar shegiyar sannan munyi mata tsirara ba. Kuma yanzu shikenan ta ci banza?" Fadin Salmanu an daudu. "Salma, to ai bala'in da take ciki yanzu ya wuce na karya afa da tsirara don kuwa dai yanzu na san tana can an sanda sun tasa eyar ar banza. Wu a fa ta taho caka min, sai Allah ya tsare ni ta caka a cikin mijinta," Laushi ta fa i tana mai arisa saka bireziya inta sannan ta saka doguwar rigar. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!" A tare Salmanu an daudu da Ladi Katifa suka fa "Wallahi kuwa. Yana can cikin jini a kwance sai tsartuwa yake. Wai kuwa kunga uban gudun da na sha? Hmm! To ai wannan dalilin ne ya saka a ka turo ku da Meema da kayanmu don zaman gidan Hajja Lanti ya fi arfinmu kuma. Don na san an sanda sai sun bi diddigina." Wani kallo Ladi Katifa tabi Laushi da shi tare da fa in, "Ban gane zaman gidan Hajja Lanti ya fi arfin ki ba? Kina da wani wajen ne da yafi can in? Kuma ai naga ba kece kika yi kisan ba." "To shine nima na gani, Katifa!" Fa in Salmanu an daudu. Kallon su Laushi ta yi tare da fa in, "Wallahi ba ni ce na kashe Alhaji Nura ba. To don mai yasa zan kashe shi? Kun manta a gaban kowa da kuma matarsa ta sunna ya za e ni sama da uwar ansa? Kishi ne ya kai ta ga hakalaka mijinta, babu hannuna a cikin mutuwar Nura." "To dama can kin yi niyyar barin gida Hajja Lantin kenan? Don idan ba haka ba ban ga ta yanda kisan Alhaji Nura ya ke da ala a da ke ba. Muma fa mun san manyan nan da hukumomin. Wallahi ko da ace ke kika yi kisan nan babu abunda zai faru da ke a cikin Lagos in nan. Nawa suka yi kuma suka sha!" Salma Nice ya fa "Lallai ba ku da hankali da kuke cewa ban da ala a da kisan da a kai wa Nura! To wacece sanadi idan ba ni ba? Zan cen gaskiya ba zan koma gidan Hajja Lanti ba, daga nan gidana na yi," Laushi ta fa i tana mai zubawa Meema harara kasancewar tsuru ta yi tana sauraran hirarsu. "Don ubanki wannan zubo mana idanun na minene? Wato kin baza kunnuwa kina rekodin ko? To maza juya ki kalli can, kar ki kuskura in juyo mu ha a idanu da ke!" Da sauri Meema ta kau da idanunta ta kwanta flat a kan wani resting chair da ke akin hawaye na zubo mata a idanunta. "Don Allah ki daina tsangwaman yarinyar nan haka," fadin Ladi Katifa. "Ta ma kashe ta kawai, Mtsw (tsaki) aikin banza da wofi!" Fa in Salma Nice. Murmushi Laushi ta yi sai da kumatunta ya lo a tare da fa in, "To kuyi ha uri. Gani na yi ta zubo mana idanu kamar ta samu talabijin." Babu wanda ya ce mata uffan, sai ma hararan da suka bita da shi. "Dama ai kai na fara yasa maka zancen barin gidan Hajja da zan yi, to yanzu lokacin ne ya yi. Salma don Allah zauna a nan kai da Meema bari na an yi magana da Katifa a waje," Laushi ta fa Mera baki ya yi tare da fa in, "Ba matsala ku je." Ba tare da sanya mayafi ba Laushi ta fita daga akin mazaunanta na motsawa duk yanda ta yi taku. Da idanu Salma ya bi Laushi da shi ciki zuciyarsa yana fa in, "Mace har mace amma ta banza!" Sai da suka nufi farfajiyar hotel in ta baya sannan Laushi ta zauna a wani an dandamali tare da nunawa Ladi wajen zama itama ta zauna. "Ladi, wata magana na ke so muyi amma na ro e ki da girman Allah ki fa a min gaskiya. Kin fi kowa sanin ban da yarda sam, amma ke kina daga cikin wa anda na amince da su ko da kuwa ban furta miki ba," Laushi ta fa i tana kallon Ladi cikin idanu. "Laushi, ki je kan maganarki kai tsaye. Ke ma kin san ba awa ko abokiyar sana'a kawai na auke ki ba, ke in tamkar ar uwa kike a wajena," Ladi ta bata amsa itama tana kallon Laushin. "Ladi, a ina kika san Sabo da kaza?" Ta jefa mata tambayar tana kallonta sosai domin ta ga reaction inta. "Sabo da kaza? Wanene haka in? Wallahi ban ta a jin wannan sunan ba idan ba yanzu a bakinki ba. Wanene shi?" Wani ajiyar zuciya Laushi ta saki domin yanzu ta gama gamsuwa babu hannun Ladin a farin sanin da Sabo da kaza ya yi mata. Don ko iyayen Ladi ba zasu nuna mata sanin halinta ba. "Wanda ya saya min gidan da zamu koma can," Laushi ta fa "To menene ha ina da shi kuma? Ta yaya zan yi ala a da shi bayan ban ta a ganinsa ba, kuma ke ma baki ta a nuna min shi ba? Laushi babu wanda zai fa a min wacece ke a nan garin. Na san sam baki da yarda da aminci shiyasa ban ta a damuwa da shiga shiga al'amuranki ba akan sai na san komai na ki. Kina zargina ne da wani abu?" "Ladi, na auko ruwan dafa kaina da alama. Kin san cewar kuwa Sabo da kaza ya san wani sirrina wanda ko ke in nan baki san shi ba! Babu tarihina da bai sani ba. Ina tsoron kar ya yi amfani da hakan wajen azabtar dani nan gaba. Jikina ya yi mugun sanyi!" Da idanu Ladi ke bin Laushi ka mun ta ce, "Wani sirri ne wannan wanda Sabo da kaza ya sani na ki?" Ta jefa mata tamabaya. Shuru ta yi na wasu da u kamun ta kama
Chapter 24 · 0% Book details