← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 143

Sashe 109

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gadon da yake kai, jikinsa ya auki wani mahaukacin zafi tamkar garwashi. Cikin abunda bai wuce mintuna uku ba Allah ya auki rayuwarsa yana ihun da ya cika asibitin domin hatta Laushi da ke nata akin tana bori sai fa ta firgita ta an natsu na wucin gadi. Gawarsa aka auka aka nufi gida da shi domin masa wanka da jana'iza sannan a kai shi ma wancinsa. 'Ya'yansa da matarsa sai kuka suke yi tamkar rayuwarsa za ta bar jikinsu. Wai a hakan ma banda iyaye maza babu wanda ya san abunda suka aikata. Baffa aleri cewa ya yi babu inda za shi, zai zauna da mahaifinsa ya yi jinyarsa a asibiti kasancewar ba a fa awa Babiyon mutuwar an nasa ba. Sai dai lokacin da aka isa gida da shi, baffa Ahmadu ya ba da shawarar a fa awa Babiyon ko Allah zai saka ya yafe masa kura-kuran da ya masa. Duk akai na'am da hakan. Baffa Ciroma da Baffa Ahmadu sune suka tafi asibitin suka shaidawa an uwan nasu bayan kwantar masa hankali da kuma bashi baki akan ya yafe masa ko ya an samu rahamar ubangiji. Hawaye kawai Babiyo ya ke ta yi yana son yin magana amma maganar ba ta fita sosai. A wheelchair aka aura Babiyo sannan aka tura shi har mota sannan Abdul-Hameed ya cicci asa a ciki suka nufi gida. Kan kace kwabo Ar o Barkin o ya cika ma il da jama'a ta ko ina kasancewar Babiyo da iyalansa sanannu ne ko don sunan kamfaninsu. Duk mutanan arzikin Babiyo mamaki suke da ganinsa a kan wheelchair don wasu ma sun yi waya da shi da daddare. Mamiyo kuwa kulleta a ka yi a cikin aki saboda ihu da koke-koke da ta yi ta yi tana tsinewa Babiyo da 'ya'yansa wanda hakan ya jefa mutanan gidan da basu san komai ba mamaki. Bayan yi masa wanka akaa shiryasa cikin likkafinsa aka shimfidar da shi a asa, sai Baffa Modibbo ya turo keken babiyo zuwa gaban gawa. Babu abunda Babiyo ke yi sai hawaye. Cikin zuciyarsa kuwa cewa ya ke, "Ka ga duniya ko Jibrila! A jiya ku ka gama ha in kashe ni domin dukiyar da ni na tara da gumi na, ashe haukar banza kake yi ba za ka wuve yau ba kana numfashi ko da ace kun yi nasarar kashe nin jiya. Da su ka ai za su yi wada a kai kuma kana rami kana girbe abunda ka shuka. Kaicona! Kaicona da ban za ar maku uwa ta,gari ba dul kaffa-kaffa na. Kaico, da tsauri da zafina tunda gashi bai saka 'ya'yana sun zamo nagari ba, kaico da rashin jan 'ya'ya a jiki don gudun raini da gudun sa awa umarnin. Da na ja ku a jikina sosai ta yanda muka zama tamkar abokan juna da hakan bata kasance ba, da duk wata matsalarku kun sanar min. Kaico da girman kai da ji ima! Kaicona ni an Iliyas. Da na san wannan ranar za ta zo da ban bar baya da ura ba, da ban ri a tauye ku 'ya'yana ba. Don na san da yawanku na shiga ha insu matu a amma tsorona da irin anyen hukuncin da na ke yankewa a kanku ya saka bakwa iya min musu da sa a umarnina! Anya na cancanci a kira Ar o kuma uba kuwa? Tir! Da halina tabbas. Na yafe maka nawa ha in, Allah ya maka gafara Jibril!" Kuka yake yi sosai, hawaye ya gama ji a gaban rigarsa don har idanunsa ba sa oya bu ewa da kyau da ma kuma ga tsufa don shekarun ba na yau bane. Ganin jikinsa na rawa kamar zai kifo da sauri Baffa Ciroma da baffa Bel o su kai kansa tare da jan wheelchair in baya suna bashi baki. Baffa aleri in shigowa akin ya yi sabida taurin kai, kafiya, zafin zuciya da rashin yafiyar da ke cunkushe a ransa. Tsanar da ya yi wa Mamiyo da 'ya'yanta ya munana matu a ta yadda gaba aya zuri'arta suka fice masa a rai daga ciki kuma harda 'ya'yan baffa Jibrila in da ba su ji ba kuma basu gani ba. yar da lallashi baffa Ahmadu ya tasa baffa aleri a gaba suka tafi su ka kai gawan baffa Jibrila. Suna dawowa jikin Babiyo ya kuma rikicewa wanda ya saka dole aka mayar da shi asibiti tare da arin fitar da shi zuwa India. angaren Khairat kuma, amaryar Baffan Gi o ne ke zaune da it wacce ita ma ke auke da nata an tayin na sati biyu, sai dai ba mai tona asiri bane don ko ita bata san dashi ba. Amma kuwa shi uban cikin yana sane ko kuma muce yana zargi. Don yanaa dagaa cikin mazan da Allah ya masu baiwar fahimtar ciki a jikin matansu kamun su su gane hakan. Zeenah kuma, tun kamun rasuwar Jibrila Habib ya zagaya ya koma wajenta. in sauraransa ta yi sai bori ta ke akan a kai ta wajen 'yarta kawai. Da yar da su in goshi ya an shawo kanta a kan ta yi hakuri rasuwa akai a gidan amma ya mata al awarin tafiya Lagos ya dubo mata ita a duk inda take ko da kuwa zai bada rayuwarsa ne, zai yi hakan domin ita. Sai ta ji ta an gamsu duk da dai hankalinta ba akwance ya ke ba. *_Bari mu le a Queen Elizabeth Amarya_* Tun bayan da aka kawo ango gidan bata samu lokacinsa na mintuna biyar ba. Don ko da aka kawo sa bai shigo akin ba sai after ten. Shima kazan amarci ya kawo mata ya yi excusing ansa ya fita domin bata dama ta shirya shi ma ka ya yi waya da wanda ya bawa kongilar nemo masa Yasaar a can Lagos. Sai dai ko kamun ya koma akin amarya a kai kiransa a waya aka shaida masa Babiyo na can rai a hannun Allah wanfa hakan ya saka ya fice ba tare da yafadawa amaryar tasa fitar ba don a gigice ya fita. Kuma ba shi ya dawo ba sai to three AM da dare lokacin Asma'u bata san inda kanta yake ba. Sai da asuba da ya tashe ta bacci ta gansa, sai ta hau kumbure-kumbure tana fushi. Murmushi ya yi ya hau lallashinta da fa a mata abunda ya faru (kun san fa ance amarya ko ta buzuzu ce akwai farin jini. Idan baku amince ba ku je ku tambayi Baffa Gi Sai dai yadda ba ta auki abun serious ba ya ona masa rai. Don ko ya mai jikin bata ce ba sai wani turanci banza da wofi da ta ishe sa da shi. Gaba aya shi bai ma cikin hankalinsa da tunaninsa gashi ya samu kira daga senate akan screening in da za ai masu domin tantance ministers in da kowacce jaha ta kawo za a za a. Babiyo ya riga ya shaida nasa kujeran da za a bashi kasancewar sune manyan asa, amma shi sam hakan bai a shi da asa ba. Ga kuma rasuwar da a ka yi a yau in da rashin lafiyar shi kasan Babiyon. Da taimakon Asma'u ya shirya domin mutanan Babiyon sai zabga masa kira suke a waya a kan he is delaying. Maza-maza ya kammala sannan ya fito ya shiga mota tare escourt suka nufi senate House. Asma'u da i tamkar zai kasheta, tuni har ta kira awayenta ta gama fesa musu abunda ke faruwa duk da garga in da Abdul-Hameed in ya mata. Sai da ya kwashi awanni shida a Senate House bayan amsa tambayoyin da bakinsa sai ya nemi ya matsa tsami sannan suka bashi damar tafiya. Ko da motarsu ta shigo Ar o Barkin o kai tsaye ya ce su wuce asibiti domin ganin jikin Babiyo. Asibitin babu mutane sosai sabida tsaron da aka saka da kuma samun nutsuwa da rashin hayaniya. Baffa Ahmadu, Baffa Bel o, Baffa aleri da Baffa Gi o ne kawai ke asibitin don an kora kowa. Sauran iyayan irin su baffa Bobbo, baffa Modibbo, da baffa Macci o suna can wajen zaman makoki. A yara kuma Hamma Jawaad da Hamma Habib sai babban an Baffa Modibbo wato wan Marwantu ne ke asibitin. Iyaye mata kuma Mahaifiyar Modibbo ce kawai wato Inna arama, Inna Jume tana can wajen zaman makoki. Dukkansu a waje suke don suma an ce su fito su bar Babiyon shi ka ai domin ya huta don jininsa ara sama ya yi kuma hakan zai iya jawo bugawar zuciyarsa ya mutu. Shigowar Abdul-Hameed in ne duk ya saka suka juya suna kallonsa don sun san inda ya je. awa ya yi ya gaishe su tare da tamayan jikin Babiyo. Duk suka amsa masa da sau i sannan suma suka tambayesa abunda ya wakana a can. Fa a musu duk abunda aka tambaye sa a can ya yi su kuma suka amsa da fatan alheri. Komawa kusa abokan nasa da su kai kicin-kicin ya yi tare da zama yana fuskantar wards da ke cikin wani korido. Ba tare da ya ce masu uffan ba don duk a tunaninsa abubuwan da suka faru a gidan ne ya canza mood in nasu. "Ki ban hanya na ce miki!" Laushi ta fa i da arfi cus she's tired of sitting while her daughter is missing. Da sauri Jawaad da Habib suka mi e jin muryan Zeenah. Shi kuwa Abdul-Hameed wani irin bugawa zuciyarsa ya yi jin muryan da ko cikin mafarki ba zai ta a mancewa da ita ba. angaren Baffa aleri kuwa, ji ya yi kunnuwansa na masa gizo da muryan da kwata-kwata bai aunar sake sauraransa a duniya. Amma yadda yaga 'ya'yan nasa sun mi e su ukun lokaci guda ya saka shi mayar da idanunsa inda suke zuciyarsa na harbawa ba kuma tare ya yi ko yun urin mi ewa ba. "Zeenah! Ina kuma za ki je? Ba mun riga mun gama magana ba." Habib ya fa i wanda shine ya fara isa kusa da ita tare da tsayawa a gabanta ya yi bake-bake don kada Jawaad ya samu damar ha a idanu da ita balle ya yi mata magana. Ji ya yi an janyesa iiiii tare da matsar da shi gefe, a zuciye ya juyo domin duk a tunaninsa Jawaad ne ya masa
Chapter 109 · 0% Book details