← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 143

Sashe 134

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yi ya kasa furta ko kalma aya sai zuciyarsa da ke wani fat-fat-fat. Daga can angaren kuwa, alhaji Haruna ya fahimci halin da Mr President in ya ke ciki sai ya cigaba da magana, "Abunda ka jima kai da matarka kuna mararin gani na tare dani a yanzu haka. 'Yarka Meemah tanaa gidana tare da iyayanka. Ka same mu a family House inku yanzu haka can za mu tafi wajen Babiyo." Wani irin mi ewa tsaye ya yi jikonsa na wani irin karkarwar da ya baiwa PA mahaukacin mamaki don ya san mawuyacin abu ne wani abu ya gigita Mr President haka saboda tsananin juriya da danne kansa, amma yau aya ya ga walla a idanunsa da kuma wani irin shau i. Don ajiye wayar ya yi akan tabur tare da fitowa sarari ya kalli gabas sannan ya yi sujada. Ya jima kansa a asa yana hawayen farinciki kamun ya ago. Yana agowa ya aga hannu samaa tare da fa in, P.A sai murmushi ya ke yi don yasan ba aramin abun farinciki Mr. President in ya ji ba. "Ka je ka fa awa securities su shirya mota zan tafi Ar o Barkin o yanzun nan." HiscExcellency ya fa i bayan ya mi e tsaye daga sujudul shukur in da ya yi. Da sauri P.A ya fice daga office in bayan ya furta, "Yes sir!" Abdul-Hameed jikinsa har wani tsuma ya ke yi wajen lalubo number in da ya yi saving da Queen of my heart ya danna kira. Ringing biyu Zeenah ta amsa kirar tare da karawa a kunne ta yi sallama cikin sanyayyiyar muryan da ta koya tun lokacin da ta tuba da bariki. "Ameen wa'alaikissalam sarauniyar zuciyata. A kullum muryanki ta daki kunnena ji nake kamar ana mun busar sarewa. Muryanki kawai idan ta daki kunnuwata imautani ta ke yi." Murmushi mai sanyi Zeenah ta yi tare da fa in, "Shiyasa sam ban nesa da wayata don na san a rana idan baka min kira goma ba to za ka yi ashirin. Ko mintuna talatin ba mu yi da gama waya da kai ba ka sake kira. Ni ma kuma ban ta a gajiya da jin dadda ar muryanka da ta fi na kanari za i. Duk lokacin da raina ya aci ko na shiga tashin hankali, da na tuna ina da kai sai inji zuciya ta wanke tare da jin warin gwiwar cigaba da numfashi. Duk da aya na bugun numfashina da sunanka ya ke bugawa!" "Ina da gaggarumar tukuici game da wannan dadda ar kalaman naki. Tukuicin da zai saka ki faricikin da sai kin zubar da hawaye. Shin kin shirya amsar wannan tukuicin?" Abdul-Hameed ya fa i fuskansa bayyane da zallar farinciki da annashuwa. Zeenah a kwance take akan makeken gadonta, bata san lokacin da ta mi e zaune ba gabanta na bugawa duk da kuwa bata san wani tukuici mijin nata zai mata ba. Sai cewa ta yi, "A shirye nake domin na tabbata tukuici indai daga wajenka zai fito to abu ne mai tsayawa a rai tare da sanya shau i da annashuwa." Murmushi ya kuma yi mai sanyi sannan ya ce, "Tukuicina na daban ne, idan na bada ni ma sai an ba ni wani abu in return." Cikin ta a Zeenah ta furta, "Zan dage a daren yau na yi wa su Muhaysim anwa, shin hakan ya yi?" ta arisa maganar tana kashe idanu tamkar dai Laushin da can. ( ba ruwana kada Mr president ya saka a nemo ni a gar ame ni) His Excellency wani siririn dariya ya yi tare da shafo eyarsa sannan ya ce, "Na gamsu da wannan tukuicin. Allah dai ya miki albarka! Ki shirya gani nan zuwa zamu fita zuwa wani waje yanzu." "In sha Allah!" Zeenah ta fa i tana arin sauka daga kan gadon. "I love you, sai na ariso." ya fa i tare da hura mata kiss. "I love you too!" ita ma ta mayar masa tare da hura masa kiss in sannan ta yanke kiran. Can gidan alhaji Haruna kuwa, gaba aya su Baffa suka shiga motocinsu domin zuwa family house. Father, Momcy, Meemah a mota aya suka zauna yayin da Aizaad ke driving. Sai da suka soma zuwa Resturant suka sayawa Meemah Sancocho tukun sannan suka nufi Ar o Barkin o Estate. Sosai Estate in ya ara shan gyaran da sabon fentin da ake masa duk shekara. Wannan karan ma farin fenti da ratsin ash colour akai wa kafatanin Estate in. Masallaci da gidan Babiyo ne kawai ya kasance fari al babu ratsin ko wani kala a jiki tun daga wajen gidan har ciki. Furnitures ne kawai suka kasance Emerald green. A katafaren farfajiyar Babiyo su kai parking, motar da su Aizaad ke ciki ne arshen shigowa saboda sune a baya. Meemah ce ta soma alle murfin mota ta fito tana gyara zaman straight skirt in jikinta saboda karkacewar da ya an yi. Aizaad sai harararta ya ke yi yana addu'ar ta ago kai ta kallesa domin ya nuna mata abayarta da ke ajiye a kujeran gaban mota da ta tashi ko Allah zai saka ta gane ta saka, amma inaa Meemah bata ma san mai ya ke yi ba. Hannu ma ta kai wajen high neck bodyhug inta tana gyarawa. aga hannun da ta yi sama ba aramin ara bayyanar da bayyananniyar kyawun dirin jikinta da Allah ya yi mata ba. Kayan sosai ya fidda shape in jikinta. Domin hatta well curve bra inta ana ina, hangosa aro- aro, haka hip insa da ke cikin straight skirt tamkar ita tai kanta. "Wai kai baza ka fito bane? Mu fa suke jira gasu can tsattsaye!" Momcy ta fa i lokacin da ta an du a daidai window in da Aizaad ke gefen. alle murfin ya yi ya fito yana mai jin matsanaicin kunya idan ya kalli Meemah cikin wannan shiga. Jerawa su kai har inda su Baffa su ke sannan gaba aya suka nufi ainahin part in Babiyo. Baffa aleri sai satan kallon Meemah ya ke yi yana an tsoki a zuciyata tare da tsinewa rainon yahudawa. "Gaskiya yarinyar kin shigo da afar dama. Da ace a da kika shigo Ar o Barkin o lokacin Babiyo na, Babiyon cikin wannan shiga da tabbas sai an yi aramin ya i billahil lazi. Don irin guguwar tashin aljanu a filin saharar da zai faru a fadar Babiyo Allah ne ka ai zai iya tsagaita shi. Don ni na ga kaina matsayin korarre sau dubu billahi!" baffa aleri ya fa i ciki-ciki. "Ko kuma a aura maka aure da 'yar cikinka ba!" baffa Gi o ya fa i yana dariya asa- asa don sarai ya ji abunda Baffa alerin ya fa Dariya Baffa aleri ya yi tare da fa in, "Shiyasa naga kai da aka maka hakan matar ta yi haihuwa hu u ga cikin na biyar na ya kusa zuwa duniya. Tsabar zari har gwarne ka ke yi! Gaskiya Gi o a gaishe ka." Wannan karan sosai sautin dariyar Baffan Gi on ya fito don sai ya tuna cikin farko da Mardiyya ta yi ba aramin oye- oye suka ri a yi ba tamkar cikin shege. Gwara shi sau dubu ma a kan uwar gayyar wato Marwanatu. Don har sai da jininta ya hau tsabar fargaba da kunya. Yanzu kuma komai ya wuce kamar ba ai ba. Soyayya a gaban uban kowa gwada masa take yi don wani lokakin ma mugun mamaki yake ji idan ta yi wani abun tamkar ba wacce aka ri a kai ruwa rana da ita ba. Sai dai abunda ke saka shi farinciki da ita shine tsantsan biyayyarta a gare shi da kuma uwar ri onta wato matarsa Mama Halima. Sallama su kai sannan suka mur a handle ofar suka shiga. Zaune ya ke a kan Wheel chair saboda afarsa da bai iya takawa ya yi tafiya sam, ko a cikin falonsa bare kuma waje. Sallah ma yanzu ya daina ja a masallaci, amma kuma har yau bai daina zuwa masallaci yin salloli biyar innan ba. Hasken ibada ne ya saka har yanzu jikinsa da arfi. Idanunsa ras yake gani, haka ha oransa ko guda aya bai fita ba. Sai dai tsufansa sosai ya fito kuma jikinsa ya an tattare. Remote ne a hannunsa yana kallon labaran da ake nuna wa tashar NTA kuma duk akan cece-kucen da wasu jama'ar suke yi ne akan His Excellency Abdul-Hameed da matarsa da ake ta cewa karuwa ce kuma 'yar safarar miyagun wayoyi sannan bugu da ari yana da iya wacce ba da aure shi da matarsa suka haifa ba. Murmushi ya yi mai sauti lokacin da ya ke ji da kallon hirar da Abdul-Hameed ya yi da BBC in. Su Baffa shuru su kai tun sallamar farko da ya yi suka amsa sai suka samu waje suka zauna suna jiran ya kammala sauraran abunda ya ke kallo a TV Sun kwashi mintuna talatin suna zaune zaman jira kamun Babiyo ya mi a remote ya kashe TV yana murmushi sosai wanda ke nuni ga ya ji da i sosai da amsar da Abdul-Hameed in ya baiwa duniya. Juyowa ya yi ya shiga kallonsu aya bayan aya kamun ya sauke idanunsa a kan Meemah ko yaftawa babu. Meeman ma kallonsa take yi cikin idanu ganin kamannin wanda aka ce mata shine mahaifin mummynta tamkar ya yi kaki. Ita ta fara yin asa da kanta sannan cikin harshen turanci ta furta, "Good afternoon sir!" Jinjina kai kawai ya yi sannan ya mayar da kallonsa izuwa kan alhaji Haruna suka gaisa don ya sansa farin sani saboda Investor in shi ne na kamfaninsa wanda shine na aya kaf Nigeria don babu abunda kamfanin bai yi. Aizaad ma gaishe sa ya yi cike da ladabi kamar yadda iyayansa su ka yi da kuma su baffa. Sai dai idan ka cire Alhaji Haruna da matarsa kaf sauran da kai ya amsa masu gaisuwar yana ara mayar da idanunsa akan Meemah kamun ya furta, "Ita wannan kuma fa? Duk da na sani kuma ina ji a jikina zuri'ar gidan nan ce amma mai yasa na ganta babu kaya kuma har kuka iya kawota gabana a haka. Shin har lalacewar tawa ta kai haka?" Babiyo ya fa i yana mai mayar da idanunsa a kan su
Chapter 134 · 0% Book details