Sashe 57
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kun fi kowa sanin wanene Ar o Barkin o da kuma abunda zai iya aikatawa. Ke kumaMardiya nasiha ta a gare ki shine, ki kama kanki ki natsu a akin aurenki, kar ki kuskura ko da wasa inji labarin kin yi wa Halima kallon banza saboda kina ganin matsayinku aya da ita. Na san wacece Halima domin ubanta rainona ne. Ita in yarinya ce mai matu ar ha uri da kawas da kai. Ban ha a aurarku da Gi o domin ta gaza ba, a'a sam! Haka Allah ya rubuta tun farko ita in ce uwar ri on ki kuma daga baya ta zama abokiyar zamanki. Kuma na za e ki ne saboda ganin natsuwarki da hankalinki. Kar ki kuskura ki yi amfani da damarki ta matar mijinta ki ce za ki wula anta, ba zan auka ba. Kamar yanda kike ata, haka itama take. Ke Amatu, in Sha Allah baza ku wuce sati ba, za ki bi mijinki ku tafi Sweden can za ku zauna har sai na nemi mijinki. Ke kuma Khairiyya, ke ma za ki bi mijinki asar da zai je yin course na shekaru biyu kawai, bayan ya kammala kuma za ku dawo tare. Allah ya ba ku zaman lafiya!" Ya arisa maganar yana mi awa kowacce ma udan ku i a cikin envelope wanda sadakinsu ne da kuma gudunmawarsa matsayinsa na kakansu. Da hannu biyu suka amsa suna godiya. Mardiya dai sai danne kukan da ke neman cin arfinta ta ke yi. "Ku kai su cikin wajen Lauratu (Mamiyo)" Babiyo ya fa i yana ara gyara zaman gilashin idanunsa. A can akin Mamiyo kuwa, zaune take a kan kujerar da ke parlourn ta hannunta ri e da wasu ananan kwalaban turaruka. Guda biyu daga cikin, launinsu green ne, ayan kuma shi ba ba i ba, shi kuma ba kalar ruwan toka mai duhu ba. Wayar ce kare a kunnanta tana magana da wani. "Yanzu ka tabbata idan har ta yi amfani da wannan turaren a inda ka ce, mijin na sha a zai ji ya tsane ta ko?" "Kwarai da gaske ni na fa a miki wannan zancen. Kuma shi da gabansa ya mi e in dai a akin ya ke to har abada. Kuma duk abunda kika ce ba zai musa ba," fa in wanda ke kan wayar. "Ke nan ko bai kusance ta ba aka wayi gari kwarya a fashe, ba zai musa cewar bai kusance ta ba ko?" Ta kuma jefa masa tambaya. "Tabbas kuwa hajiya. Sai dai idan bai sha i wannan turaran ba," ya fa i yana dariya basawa. Yanke wayar ta yi tare da ajiyar a kan kujera sannan ta saka ko wani turare a cikin wani an akwati mai auke da awarwaro da an kunnen zinari. Kuma a daidai wannan lokaci akai knocking akinta. Da fara'a ta bu akin tana masu maraba kamar abun arziki. Bayan doguwar nasihar zaman aure, sai ta umarci amaren kawai da su mi e su bi bayanta zuwa cikin akin baccinta. Gaba aya suka mi e suka bi bayanta. Gyalen da suka lullu e jiki da shi ta saka suka warware, ta kan Amatul kareem ta fara, babu inda bata goga mata turaren ba. Tuni wani amshi mai azababben da i ya gauraye akin. Haka ta yi wa Khairat matar Jawad itama. Da tazo kan Mardiya, sai ta bu ayan turaren ta goga jikin wani farar auduga mai taushi sannan ta soma goga mata. Tun gogawar farko kan Mardiya ya yi wani duum, nan da nan turaran ya soma hawa kanta taji kamar za ta yi amai. Mamiyo kuwa sai da ta goga mata sosai a jikinta sannan ta mi awa kowacce kyautarta kamun ta fito da su parlourn aka wuce da su gidajan. _The Grooms_ Duk da auren ba haka suka so yazo masu ba, amma sun cakare babu wanda zai kalle su ya ce akwai wani abu a zuciyarsu. Su ukun nan sun yi anko cikin wata farar tattausar yadi mai layi-layi transparent don hatta singlet in jikinsu ana gani. Yadin yana da matu ar tsada da taushi. Abdul Hameed da ya kasance ba i a cikinsu, yadin ba aramin amsarsa ta yi ba ka ce shine angon. "Kai! Wai Jawaad lafiyar ka kuwa? Sai ka arar mun da turaren tukun za ka ji da i? Ni dai tun da na nuna maka turaran nan na shiga uku ai," fa in Abdul Hameed tare da kai hannu ya fizge kwalbar. "Oho dai, na dai fesa ma'ishi!" Jawaad in ya fa i yana masa gwalo. A jikin Abdul Hameed Jawaad ya soma jin amshin turaren *_DKNY Golden Delicious_*. Duk idan ka ji wannan amshin to babu shakka Abdul Hameed in ne a wajen. Shi kuma Jawaad sai Allah ya ora masa aunar turaren, don wani lokacin takanas bayan ya yi wanka ya shirya ya ke tafiya gidan Baffa o domin ya fesa turaren Abdul Hameed in. Bayan Abdul Hameed sun bar Ar o Barkin o ya yi neman turaren a Abuja, da wasu daga cikin asashen da ya ke zuwa bai samu ba sai shekara aya baya da ya je Sweden ya samo turaran a wani complex da yaje. "Ungo an wutan ciki! Kasancewar na san kana aunar turaren na sayo maka shi matsayin gift na aurenka." Fa in Abdul Hameed bayan ya saka masa a hannu. Rungumesa Jawaad ya yi tare da fa in, "That's why I love you my Hamma Hameed." "To ni ina nawa kyautar?" Habib ya fa i kana kallonsa kasan akwai sauran rashin lafiya a jikinsa musamman ma azu da ya le a gidansu ya ci karo da annansa sai rusa kuka suke da suka ji aurar da Babiyo ya yi wa Baffan. "Ungo kai ma, ni muje in kai ku gidajanku joo. Kuma kun san dai sai mun fara zuwa wajen Babiyo." Bayan few minutes suka kammala sannan suka hau mota zuwa gidan Babiyo. Yana nan parlourn zaune, sai dai wannan karon furarsa ya ke sha, Mamiyo na gefensa tana an jefa masa zance zuciyarta wasai. "Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuhu!" Gaba aya suka fa i kasancewar sun san halin Babiyon ya fi son cikakkiyar sallama. Yana aga kai da Abdul Hameed ya fara arba, hakan ne ya saka ya amsa sallamar fuska fa e da fara'a. Zama su kai a asa daidai wajen afafunsa sannan suka gaishe sa shi da Mamiyo. Mamiyo kasa amsawa ta yi sai kallon da ta bi Abdul Hameed in da idanu tana jin kamar ta tashi ta sha ar shi ya mutu nan take. Sosai ta yi nisa a tunaninsa don bata ji duk abunda Babiyo ya ke cewa ba, ta dai tsinci maganarsa na arshe, "In sha gaba aya rana ita yau za ku bar asa. Sai dai ku sani, dukkan ku za ku dawo idan lokacin ka uri'a ya yi domin ku za an uwanku kuma abokinku, Abdul Hameed." "In Sha Allah, Babiyo. Mun gode da nasiha, Allah ya saka da alkhairi ya ara girma." Duk suka fa Da ameen ya amsa sannan su kai masu sallama, Mamiyo da kai kawai ta iya amsawa. Don idan ba gizo idanunta suke mata ba, sai taga kamar Abdul Hameed harararta ya ke yi. Habibu ya fara saukewa a harabar gidansa tare da mi a masa ledan kaza da yoghurt tare da fa in, "Aci amarci lafiya!" Sai da suka an tsaya na mintuna biyar suka zaulayi juna kamun Abdul Hameed in ya juya kan mota ya sauke Jawaad in shima yana masa tsiya. Kai tsaye ke an gidansa ya nufa domin ya huta gajiya. Parking ya yi tare da fitowa daga motar ya doshi cikin gida, sai dai bai yi ko taku hu u ba yaji wani mahaukacin azaba a kyeyarsa sakamakon sauke masa wani mur arfe a wajen. Wani irin jiri ya soma gani ga jinin da ke zuba a yeyarsa kamar an bu e fanfo. Yaraf ya fa asa yana shure-shure kamun if ya tafi. Wanda ya kwa a masa karfen kuwa, kansa ya zo ya tsaya tare da tatta asa domin tabbatarwa shin ya mutu. Jin babu numfashi sai ya saki wata dariya tare da janya gefe sannan ya bar gidan da sauri... A can gidan Baffa Gi o kuwa, ana shigar da Mardiya cikin akinta ta yi saurin fa awa ban aki saboda wannan turaren da Mamiyo ta saka ba aramin aga mata hankali ya ke ba. Burinta kawai ta sake yin wanka domin wanke amshin turaren ko za ta ji dama-dama.... _ZEENATU LAUSHI_ Ciwo ya hana ta sukuni. Duk da ba ta buge-buge amma kanta ji take kamar ba na ta ba. Gashi gidan yanzu ya zama tamkar na an ta'adda, don kwana suke idan sun kawo kaya. Abu ya zama mata goma da ashirin. Yanzu za ayi abu da ita, yanzu ta manta shi kwata-kwata. Ga wani irin shuru-shuru da ta koma. Idan kuwa ka yi kuskuran bu ofa ya yi ara yanzu za ta fita hayyacinta. Ko arar cokali bata son jin idan ana cin abinci don a cikin ma iganta take jinsa. Tafiya, cin abinci da magana ya zama cikin takatsantsan saboda condition in ta. Meema kuwa, yaran spanish in da ake koya mata ya soma zame mata tamkar yaran Hausa. Ta an fara sakewa da Yahuza saboda kullum suna tare. Shi ke kai ta makaranta ya dawo da ita. _YASAAR_ "Kana jina ko, ni wallahi gani nake Oga raina min wayau kawai ya ke yi. Daga ni har Zeenah amfani ya ke damu domin cika burinsa. To gaskiya an kawo ni karshe! Ban san mai yasa mutanen da na amince da su suke min haka a rayuwa ba. Don haka na gama yanke hukunci. Zan aikata abunda na ce maka zan yi, zan nunawa Sabo da Kaza ba shi ka ai ya iya playing game ba, ni ma na koya daga gare shi. Don haka zan riga shi auke Meema, ni Colombia zan tura ta wajen Adalberto ya tura min ku inta kawai, ita kuma uwar na san yanda zan yi da ita............" #Abdul Hameed #Jawaad #Habib #Mamiyo #Babiyo #Baffa Gi #Mardiya #Mama Halima #Sabo da Kaza #Yasaar #Meema #Colombia #My Destiny #Matar Sayyadee 08128755583 Rahamanatu: *_MY DESTINY_* ( ~ addarata~) *Zulfa'u Sa'eed Ibrahim* _Matar Sayyadee_ _Wattpad @Matar_Sayyadee_ Arewabook@Matarsayyadee *ZAFAFA WRITER'S