← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 143

Sashe 48

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

baza ta tashi ba, sai kuma ta mi e ta nufi bayan kujeran inda ya ke a tsaye. "Mummynki za ta samu lafiya kin ji! Ciwon kai ne mai tsanani ya ke damunta. Kin san ta shiga damuwa mai tsanani lokacin da aka yi kidnapping in ki. Hakan ne ya haifar mata da damuwar da ta saka mata matsanaicin ciwon kai. Amma idan ta huta za ta tashi wasai. Wannan ba wani ciwo bane na tashin hankali." Hakanan Meema ta ji bata gamsu da maganarsa ba. Amma sai ta gya a masa kai kawai hawaye na zubo daga idanunta. "Zan fita inje in samo mata wani magani ta sha idan ta tashi. Ki kula da ita, kin ji?" a masa kai ta kuma yi a karo na biyu tare da komawa gaban kujeran inda Laushi ke kwance ta aura hannunsa a kan jikinta. Duk da Laushi bacci ta ke yi, amma lokaci-lokaci ta kan kai hannu kanta tana yamutsa fuska alamar kan yana matsa mata da ciwo ko a cikin bacci. Sabo da Kaza na ficewa daga gidan a cikin motarsa ya aga waya ya kira wata Number ya yi maganar mintuna biyu sannan ya yanke wayar. A ofar guess house in sa ya yi parking ba tare da ya shigar da motar ciki ba ya fito ya yi amfani da key in hannunsa ya bu e gidan ya shiga ciki. ofar akin ya yi knocking sau biyu, nan take Yasaar da shekaran jiya ya fito daga gidan yari ya taso ya bu e masa ofar tare da matsawa ya bashi hanya ya shigo ciki. Sai da ya yi balance a kan kujera three seater sannan ya kalli Yasaar ya ce, "Yasaar, wato abunda muke shirin aikatawa Laushi ba aramin illa zai wa rayuwarta ba. Tabbas za ka an samu relief akan abunda ta aikata maka. Wai ka san wani irin cuta take auke da shi a walwarta kuwa?" Girgiza kai Yasaar ya yi yana jiran arin bayani daga wajen Sabo da Kaza da ke aka dariyar mugunta. Sai da ya yi dariyarsa ma'ishi sannan ya ce, "Fusiform aneurysm ta ke fama da shi. Ina mai tabbatar maka aya daga cikin wa annan abubuwan zai iya faruwa da ita; shanyewar arin jiki, doguwar suma, ko kuma walwarta ta yi dameji. Infact za ta iya mutuwa ko wani irin lokaci. Kuma babban matsalar shine; masu irin ciwon nan sam basu bu atar tashin hankali don hawan jini yana aya daga cikin abinda ke haifar da ciwo." "Wani irin ciwo ne wannan haka? Ban ta a jin ko labarin sa ba," Yasaar ya fa i yana kallon Sabo da Kaza with confusion. "Fusiform anuerysm kumburi ne na duka magudanar jijiyar jinin da ke walwa," saboda da Kaza ya fadi murmushi bai bar fuskansa ba. Wani irin acin rai ne ya dabaibaye fuskan Yasaar. Cike da unar zuciya ya furta, "Yanzu ke nan ba za ta yi tsawon ran da za ta ani kwatankwacin ba in cikin da ta saka ni ba? Kullum da hoton tagwainina na ke kwana a irjina. an uwana bai ji ba bai gani ba ta yi sanadiyar mutuwar sa. Ba zan bari wannan ya tafi a banza ba. Idan har Laushi ta mutu da wuri, burina ba zai ta a cika ba na wula anta rayuwarta. aunar yarinyar nan ta mutu," Yasaar ya fa i hawayen ba in ciki na kwaranyo masa. Dafa kafa arsa Sabo da Kaza ya yi tare da fa in, "Kwantar da hankalinka, Yasaar. Ai ni ma ba zan bari haka ya faru ba. (sai ka ce rayuwarta a hannunsu ya ke ) zan ri a amso mata magani kamar yanda doctor William ya bani shawara tun a Paris. Ka san tun a can da ciwon ya soma nunawa na kai ta asibiti suka fa a min ciwon da ke damunta. Kuma ya fa a min idan tana shan pills in da ya fa a min za ta ri an improving, amma fa idan so ake ta warke duk da sun ce ba a ta a warkewa gaba aya, amma idan aka yi mata aya daga cikin wa anda za ta iya warkewa. Wato; Hunterian ligation, trapping, surgical bypass, and clip reconstruction techniques. Amma mafi yawanci sai an yi surgery kuma under risk ya ke." "Ni dai wallahi ban so ta mutu. Allah yasa sai na gama gwarata kamar kwallo, kuma ta mugun wula anta a duniya kamun ta mutu," Yasaar ya fa "Burinka zai cika," Sabo da Kaza ya fa i yana bugun bayansa ka an tare da mi ewa ya shiga cikin wani aki. Yana shiga aki wayarsa ta yi ara alamar shigowar sa o. Fiddo wayar ya yi daga aljihu sai ya ga sa o ne daga doctor William. _She should take the following; Calcium channel blockers, Antiepileptics, Antihypertensives, Analgesics, Antiemetics, Antacids, and Stool softeners. Also she should avoid taking the following medicines; Cipro (ciprofloxacin), Levaquin (levofloxacin), Factive (gemifloxacin) and Avelox (moxifloxacin). These medications may increase the risk of aortic dissections or ruptures._ Yana gama karanta ya tura masa thanks tare da jefar da wayar a kan gado sannan ya fa awa toilet. angaren Laushi kuwa, wannan matsanancin ciwon kan ba aramin uzzurawa rayuwarta ya ke ba ko cikin bacci. Meema kuwa ko gusawa daga inda ta ke ba ta yi ba tana nan ta zabga tagumi tana kallon Laushi. Wani lokacin kuma sai ta fashe da kukan musamman idan Laushin ta kai hannu bibbiyu ta dam i kanta ta shiga jujjuyawa. "Mummy, mummy, mummy can you hear me?" Meema ta fa i tana kallon fuskan laushin da ya an soma kumbura ka Laushi kuwa bata ma san duniyar da take ba balle ta jiyo muryan iyar tata. Mi ewa Meema ta yi ta kwasa da gudu ta shiga bedroom in Laushin tare da auko wayarta ta lalubo Number in Ladi Katifa ta danna mata kira. Sai da wayar ta kusa tsinkewa sannan Ladi ta aga kiran tare da fa "Har an gama cin uwar sabadar kenan? Ya wuce ne?" "Aunty Ladi ki zo da sauri don Allah, mummyna za ta mutu," da kuka Meema ta arisa maganar. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Gamu nan zuwa ni da Salma nice yanzu," tana gama fa in haka ta katse wayar. Parlour Meema ta dawo ta zauna tare da ri e hannun Laushi saboda wannan karan bugun kan take da arfin tsiya. Yanzu hakan ma sai da ta saka arfinta duka sannan ta iya ri e hannunta kuma don har yanzu allurar anesthesia da Sabo da kazan ya mata yana aiki a jikinta, don a hakan ya rage mata ra in azabar ciwon kan da take fama da shi. Cikin awa guda, Ladi da Salma nice suka shigo gidan hankali tashe lokacin allurar anesthesia ya soma sakin jikinta sai sai haukan buga kai da kujera take. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un, ni Salmanu jikan Iya! Wannan wani irin ciwo ne kamar na hauka?" "A'a dawanau ne na Kano ko kuma Barnawa a kanta. Ya muna masifar tashin hankalin nan za ka da a mana wani a kai! In Sha Allah, Laushi ba za ta ta a hauka ba a kaf rayuwarta," Ladi ta fa i tana kuka. Kamar an tsikari Laushi ta tashi a razane tare da kwan ama wani irin mahaukacin ihu tana buga kanta a jikin kujera, Ladi Katifa ta yi iya kacin arin wajen ganin ta ri e ta kada ta jima kanta ciwo amma ta kasa. Hatta Salma nice sai da ya ajiye daudu a gefe ya saka dukkanin arfinsa amma ya kasa ri e Laushi. Meema ganin haukan buga kan da mummynta take yi yafi na azu lokacin da Sabo da Kaza ya ke nan sai ta hau kuka har numfashinta na wani irin aukewa. Sai jin fa uwarta tim suka yi a asa. "Tabbat yada habi lahabin wa Tabba, Inna a'a aina kalkauthar, Li'ilafi quraishin! Ya Allah kai ka ai ne Lam yalid walam yulad, walam yakul lahu kufwan ahad, ka rufa mana asiri ka tashi kafa un wannan baiwar taka. Allah astagfirullah mun tuba billahil lazhi la'ilaha illahuwa. Allah kafi kowa sanin ni in ba kowa bane face Salmanu jikan Iyan mai danko. Allah mun tuba ka yafe mana," fa in Salmanu bayan ya aga hannunsa biyu sama har da wallarsa. Ladi ru ewa ta yi ita ma ta fashe da kuwa kuma ta rasa inda za ta nufa, wajen Meema domin bata taimako ko kuwa wajen Laushi da duk ta gama fashe kanta sai tsiyayar da jini yake. "Salma fita ki nemo mana......." Saurin katse Ladi da ta soma magana ya yi cikin kuka tare da fa in, "Wallahi Allah ya isa kika kuma tura ni jinsin an mata. Mai kuma ya ha ani da jinsin mata ni ba irji da mazaune ba. Ko kin ganni da bireziya ne a jiki. A'a wallahi idan ma don wannan kallabin da ke aure a kaina ne to billahil lazhi na cire shi na yar. Gobe-goben nan zan je kasuwa in nemo hula shafa kaji hadisi da kuma carbi in ri e a hannu ina ja. Kar ki kuma kai ni jinsin mata!" Da iyakacin gaskiyarsa ya ke fa in haka bayan ya cire duk wani abu da ya danganci mace a jikinsa ya wurgar a asan aki. Da Ladi Katifa cikin hayyacinta take, to babu abunda zai hana ta dariya har da kwanciya a asa saboda yanda gaba aya Salmanu an daudu ya firgice yana fa in maganganu. "Dalla fita ka nemo mana taxi kar ayi gawa biyu a cikin gidan nan!" Ladi Katifa ta fa i da arfi. Har Salmanu ya aga afa aya sai ga Sabo da Kaza ya shigo hannunsa ri e da wata ledan mai tambarin wata babbar pharmacy da ke Lagos. Da kallo ya bisu kamun ya sauke idanunsa a kan Laushi da gaba aya jikinta ya aci da jinin da ke zuba a kanta. "Tsayuwar me kuke yi kamar wasu sojojin gadi kuna kallon halin da take ciki kuma a hakan kuke kiran kanku abokanta?" Saboda da kaza ya fa i cike da fushin da ba daga zuciyarsa ta fito ba. "Yanzu muke arin kiran taxi domin kai ta asibiti," Salmanu an daudu ya fa i don ita Ladi kallo aya
Chapter 48 · 0% Book details