← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 143

Sashe 2

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ayan an sandan dake bayansa ne ya ariso wajen tare da fa in, "Wai me take fa a ne a wajen? Halan karuwa ce? Samin ita a mota yanzu!" Ya arisa maganar da an tsawa. Ja da baya ta an yi ka an jin abunda ayan police officer in ya ce tare da fa in, "Mai na yi da za'a saka ni a mota? Halan ba ku da mata ne a gida? Kuna ganin wannan hali da nake ciki baza ku tausaya min ba sai ka ce a saka maka ni a mota kamar wata criminal." Ta arisa maganar tare da ri e mararta ta kwantsama wani ihu tana mai age zanin jikinta wanda jini ke gangarowa daga jikinta har zuwa idon sahun afarta kuma hakan yayi daidai da hasketan da police in ya sake yi a karo na biyu. "Subhanallah! Baiwar Allah yi ha uri don Allah. Amma bai kamata a cikin wannan hali ki fito ke aya da. Gashi yanzu mota ta yi nesa da mu balle mu taimaka maki zuwa asibiti. Kofur anjuma akwai wani asibiti mafi kusa a nan!" Ya arisa maganar fuskansa unshe da tausayinta kasancewar a cikin irin wannan hali da take ciki mahaifiyarsa ta haifesa sannan ta koma ga Allah. "Gaskiya yalla ai babu asibiti kusa anan wajen. Sai ka yi tafiya sosai zuwa bakin titi kamun ka samu abun hawan da zai kai ka can asibitin, kuma ga shi yanzu dare ne sosai." Waigawa ta kuma yi a karo na uku duk da a du e take. Da hannu ta yi masu nuni tare da fa in, "Na kusa isa inda zani. Tafiya ka an ce za ta sada ni da gidan anwar mamata. Akwai babur a gidan za su kai ni asibiti idan na arisa." Da sauri police officer in ya ce, "Idan za ki iya tafiya muje sai muyi maki rakiya." Ya arisa maganar tare da waiwayawa ya yiwa kofur anjuma magana akan ya taho su tafi tare. Ba haka ta so ba, amma haka nan ta yi ta yin ingishin arya da ri e ciki har su ka yi tafiya mai nisa sannan suka iso wani gidan asa mai auke da aki aya tal a ciki sai ofar da ake jinginawa a rufe idan dare ya yi gudun barin gidan wagaga. "Yauwa nan ne gidan." Ta fadi tana mai kai hannu ta dafi bangon gidan tana mayar da numfashi. "Nagode." Ta fa i bayan ta waiwaya ta kallesu sannan ta maido da idanunta akan kofar tare da matsar da langa-langar yauran sannan ta shige ta mayar ta rufe. Haske gidan kofur anjuma yayi sosai ya na raya wani abu cikin ransa sai dai bai yi kuskuren furta ko kalma guda ba kasancewar ya san wacce take zaune cikin gidan. Don duk akai albashi rabin ku insa a wannan gidan yake arewa. "Muje kofur anjuma. Wannan mata ta yi namijin ari da har ta iya wannan tafiya mai tsayi kuma tana cikin halin na uda." "Gaskiya kam ta yi ari. Allah ya raba lafiya." Shine abunda kofur anjuma ya ce yana mamakin ta yaya Ladi katifa za ta kasance anwar mahaifiya ga wancan matar mai ciki bayan ko Ladin za ta girme ta bai fi da shekara aya ba ko su zo sa'annin juna ma." A hankali ta le o domin tabbatarwa shin sun wuce. Ganin sun wuce sai ta yi saurin shiga ainahin cikin gidan tare da soma jijjiga ofar akin Ladi katifa da arfi ta na kuma kiran sunanta kasancewarta mai mugun nauyin barci. Can cikin baccinta mai da i ta ji ana jijjiga ofa kuma ana kiran sunanta. Mutun biyu ne ta san za su iya mata hakan; Yahuza ko Laushi. Saukowa ta yi daga katifar bacci a idanunta tare da isa wajen ofar ba tare da ta bu e ba ta d'aure fuskarta tamau kana a kausashe ta ce, "Waye a wajen nan da daddaren nan?" Kasancewar ta uduri aniyar idan Yahuza ne sai ta shuka masa rashin mutunci. "Dalla matsa! Ki zo ki bu ofar maza yanzu kar jinina ya are, Laushi ce." Matar da ke ofar akin wacce ta kira kanta da Laushi ta fa i rai ace don gaba aya ta agu ta bu e mata ofar don hankalinta a tashe ya ke kasancewar yau ne ta fara kashe rai a iya tsayin rayuwarta kuma ta mahaifinta. Da sauri Ladi katifa ta bu ofar tare da fa in, "Laushi, ya na gan ki yanzu a wannan daren? Ko har kin kammala? Ina sar ar?" Ta watso mata tambayoyi. Babu ko aya daga cikin tambayoyin da Laushi ta amsa mata, sai ma ture ta da ta yi sannan ta shigo akin ta kunna hasken lantarki tare da kama asan zaninta ta yaga da arfi. "Inna lillahi! Laushi na uda kike yi? Yau mun bani. Kuma na udar jini." Fa in Ladi katifa a ru Harararta Laushi ta yi tare da fa in, "Sai kace yau kika fara ganin haihuwa. To ba haihuwar bace basaja na yi." "Basaja kuma?" Fa in Ladi katifa don sam bata fahimci mai awar tata take nufi ba. "Na ha u da masu ba in kayan nan ne a hanyata ta zuwa nan gidan har aya daga cikin su ya ke fa in wai a saka masa ni a mota. Shine cikin dabara na karci tsokar cinyata da arfi jini ya alle domin su yi tunanin na uda na ke yi." Ta arisa maganar tana mai ulle cinyarta da kyallan da ta yanka a jikin zaninta. Ajiyar zuciya Ladi katifa ta yi tare da fa in, "To yanzu Laushi ya ake ciki? Ki fa i min dalilinki na dawowa nan in bayan ga abunda muka tsara." Laushi ba tare da ta yi magana ba ta sama hannu cikin rigarta ta zaro wata sar a da ankunne tana murmushi. "Ba wannan shine burinmu ba? To na auko. Zaman mai kuma zan yi cikin gidan?" Waro idanu Ladi katifa ta yi tare da fa in, "Tabbas babu sauran zama a gidan. Amma tambayata shine; ta yaya kika auko wannan sar ar da ankunnen a yau har kuma kika fito babanku bai gan ki ba? Sannan na san mamarku da tsinannan wayau, don ita kika auko a ankaran wayau wallahi." "Katifa!" Laushi ta yi kiran sunata. "Na'am Laushi." Ladi ita ma ta yi kiran na ta sunan. "Ki adana tambayoyinki a yanzu don ba su da wani mahimmanci. Da asubar fari za mu bar gidan nan mu tafi Legas (Lagos). Idan ba haka ba kuma, to ina mai tabbatar miki zamu are rayuwarmu a magar ama." Sai ta kalli tirnitsetsen cikin da ke jikinta tare da shafawa sannan ta ce, "Kuma ni ban shirya hakan ba don ina da burika da dama." Hankali tashe Ladi katifa ta ce, "Laushi mai kika aikata haka?" A zafafe Laushi ta ce, "Na ce maki ki adana tambayoyinki ba su da mahimmanci a yanzu! Kawai abunda za ki yi shine; Ha a duk wani abunda kika san masu mahimmanci ne ki ulle su domin asubar fari za mu bar gidan nan tun da dama ai kin riga kin sayar tun jiya." Shuru Ladi katifa ta yi tana kallon awarta na tsawan sakonni tare da soma ha a duk wani kayanta masu mahimmanci cikin jaka. Don idan ta kalli kwayar idanun awar tata sai taji hankalinta ya tashi. Don Laushi babu abunda ba za ta iya ba akan ku Laushi na kallonta ta gefen idanu. Kuma tana lure da irin halin da Ladi katifa ta ke ciki kasancewar ta hango tsoro aro- aro a cikin idanunta. Murmushi ta yi tare da fa in, "Ki kwantar da hankalinki Katifa. Ni babu wani abunda na yi na kuskure. Na amshi wannan sar an zinarin ne ta yanda ya kamata. Mahaifiyata da kanta ta dam amin wannan sarkan bayan karanto mata anzon kurege. Na yi amfani da awazuci da kuma makauniyar soyayyar mahaifiya na amshi wannan sar an. Shi kuma babanmu, yanzu haka ina mai tabbatar miki yana kwance yana bacci cikin salama da kwanciyar hankali. Sai dai fa ina mai tabbatar miki idan har gari ya waye mana a wannan garin kashin mu ya gama bushewa. Shiyasa na ke so asubar fari mu bar garin nan." Sai a wannan lokacin Ladi katifa ta an jin sanyi cikin zuciyarta tare da fa in, "To ai ke in ce akwai tsoratar da mutum. Kuma sanin da na yi maki babu abunda ba za ki iya aikatawa ba akan ku Murmushi Laushi ta yi tare da fa in, "To ki kwantar da hankalinki babu wani abun da na aikata mara kyau. Ki na da ragowar sigari?" Hanka a filo Ladi katifa ta yi tare da auko kwalin sigari mai suna *_Aspen_* ta mi a mata tare da lighter. Amsa Laushi ta yi tare da bu e kwalin ta auki sigari aya ta saka a baki sannan ta kunna lighter ta shiga zu ar sigarin cike da kwarewa ta na fesar da haya in. Hakan ne ya yun urowa Ladi katifa da sha'awar shan sigarin ita ma. Hannu ta kai ta zari aya tare da kunna masa wuta ita ma ta shiga zu a ta na fesar da haya i. A cikin su babu wacce ta rutsa har alfijir ta fito. Ana shiga masallaci suka yi sa af-sa af suka fice daga gidan suka nufi tasha. Ko kamun takwas motarasu ta aga zuwa garin Legas. Tafiya ce su kai mai matukar tsayi a cikin wannan mota. Laushi ta gyara zama yafi sau shurin masa i kasancewar wannan shine karonta na farko zuwa garin Legas (Lagos). Sun zaunu iya zaunuwa. Amma a wajen Ladi katifa hakan ba komai bane don wannan ba shine zuwanta na farko ba. Cikin dare suka sauka. Abunda yayi matu ar baiwa Laushi mamaki shine; ganin jama'ar garin nata zirga-zirga kamar rana, masu cin kasuwar dare na yi, haka an shaye-shaye da masu sana'a irin ta su. "Katifa, wannan wani irin gari ne haka kika kawo ni? Wallahi duk iskancina a tsorace nake. Kalli yanda wancen tsohon ke mana wani irin kallo." Fa in Laushi tana mai dam ar hannun Ladi Katifa. Murmushi Ladi katifa ta yi tare da fa in, "Tsarguwa ce kawai. Amma nan garin da kike gani ka
Chapter 2 · 0% Book details