← Book details My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 143

Sashe 62

My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

jawo hankula har asirinsa ya tonu. Wani irin duka ya kaiwa steri da arfi ganin sun acewa ganinsa. Sai kawai ya juya kan motar ya koma makarantarsu Meema domin auko. "Idan kin san wata, to baki san wata ba. Zan yi amfani da arki kuma rauninki, dole ki fito a duk inda kika uya!" Fa in Yasaar. Abokinsa da ke gefensa ya girgiza kai tare da fa in, "Ka yi wani abu yanzun nan idan ba haka ba wallahi asirinka ya gama tonuwa idan har ta koma gida ta kira Sabo da Kaza. Kuma hakan idan har ya ji kashinka ya gama bushewa. Wallahi kashe ka zai yi!" Tsaam Yasaar ya yi yana wani nazari a zuciyarsa. Can kuma ya saki murmushi tare da fa in, "Zan yi amfani da salon yaudarar da ta yi min har aka cafke ni na yi zaman gidan yari tare da rasa tagwainina abun aunata. Yanzu zan tura jami'an NDLEA gidan bayan na basu bayani akan abubuwan da ake aikatawa, sannan inyi wa Sabo da Kaza cunnensa har inda yake duk da na san ba za a jima ba zai ku uto, amma kuma zan cusa wata mummunar iyayyar Zeenatu a zuciyarsa. Ba zai ta a kawo ni ne na munafuncesa ba, Zeenah ce za ta zama first suspect insa. Kuma ba zai ta a kyaleta ba. Ka ga kenan na jefi tsuntsu biyu da dutse aya," yana gama fa in haka ya yi wasu an danne-danne a waya na kusan mintuna goma sannan ya juya kan mota zuwa makarantarsu Meema. A cikin motar Informer in Jawaad kuwa, mugun gudu suka sharara kamar za su bar garin Lagos sannan ya yi parking a gefen hanya ya kira Number in Jawaad. Laushi kuwa gaba aya ta ru e, hankalinta ya yi mugun tashin da ciwonta ya kusa motsawa. Hankalinta kacokam ya koma kan arta Meema, don ta san halin Yasaar, tunda bai same ta ba, kan arta zai koma. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! ata!! Na shiga uku. Meema, don girman Allah malam mu koma in auko ata, zai cutar min da ata wallahi. ata ita ce rayuwata! Ita ce duniyata, ita ka ai ce dangina. Don Allah ka mayar dani in auko ata," fa in Laushi tana kuka sosai. Gaba aya a kunnan Jawaad ta yi maganar saboda ya aga kiran Informer in nasa kenan ya jiyo sautinta tana wannan maganar. "Bata wayar," Jawaad ya fa i yana mai kumshe idanu don kukanta har cikin zuciyarsa ya ke jinsa. a mata wayar Informer ya yi tare da fa in, "Amshi, za ayi maki magana." Saurin warce wayar ta yi tare da karawa a kunne ta soma fa in, "Yasaar, na ro a da girman ubangiji kar ka cutar min da ata. ata ba tai maka komai ba, ni ce na yi maka laifi. Zan zo gare ka ka hukuntani amma kar ka cutar min da ata." "Nutsu!" Jawaad ya fa i a hankali yana lumshe idanunsa. Ya na iya hango tsagwaran tashin hankali da damuwar da take ciki a muryanta. Cak ta tsaya da kukan jin saukar muryan da ba na Yasaar in ba. Wani irin ajiyar zuciya tashin hankali ta saki tare da fa in, "Da wa nake magana? Wanene kai? Ku su waye?? Yasaar in ne ya turo ku? ata! Ina ata take?" A hankali ta arisa maganar tare da sumewa a jikin kujera. Da sauri ya tara hannu tare da ca e wayar da ke arin fa uwa asa saboda sake shi da ta yi ya ara a kunne tare da fa in, "Yalla ai ta suma fa!" "Kuna ina yanzu?" Jawaad ya fa i da tashin hankali a muryansa. "Ga mu a bakin babban hanyar fita daga Lagos." "Ka sauke glass asa domin iska ya shigo, sannan ka juya ka nemi aramin masauki ta waje-wajen Lagos in sannan ka koma can makarantar ka auko yarinyar. Zan kira ka zuwa anjima bari na arisa gida yanzu na kimtsa. Ni ma zan biyo jirgi na taho Lagos in yau in Sha Allah!" Yana gama fa in haka ya katse kiran. Sauke glass in ya yi kamar yanda Jawaad ya umarta sannan ya kunna matar ya juya. Ya an yi tafiya sosai sannan ya taras da masaukin baki dake kan hanya. Har cikin harabar ya yi parking sannan ya fita ya yi booking aki. Lokacin da ya dawo wajen motar, Laushi ta farfa o daga suman da ta yi, sai dai sai rizgar kuka take yi tana fa arta. Zagayawa ya yi ya shiga mazaunin driver ya zauna tare da fuskantarta ya ce, "Ki kwantar da hankalinki, in Sha Allah yanzun nan zan koma in auko maki arki. Babu abunda zai same ta. Yanzu ki sauka mu shiga ciki in nuna miki akin da za ki zauna sai in koma can in auko ta." "Mu tafi tare don Allah! Wallahi hankalina ba zai ta a kwanciya ba har sai na ga ata tukun. Ba ka san wanene Yasaar ba, wallahi zai iya yin komai domin ya ga ya cutar dani. Na shiga uku ni Zeenah! Sam bariki ba tai min riba ba, ga shi yanzu na jefa mu ni da ata a cikin halaka. Wa ya san ko ma jinin mahaifina ne ke bibiyata," ta arisa maganar tare da fashewa da kuka. Tausayinta ne ya kama shi, an gyaran murya ya yi tare da fa in, "Babu yanda za ayi mu tafi tare, kin san dai ke ma farautar rayuwarki ake yi. Don haka ki ha uri ki zauna anan in, ni kuma in Sha Allah zan dawo miki da iyarki." Ba don ta so ba ta amince don ta san tabbas Yasaar ba zai ta a hutawa ba har sai ya ga ita da arta a hannunsa. Pass in da zai bashi damar auko Meeman ta bashi, don ko zai mutu baza a bari ya auki Meeman ba sai da shi. Bayan ya kai ta masaukin tare da yi mata order in abincin da ya san ba lallai bane ta iya cinsa, sannan ya kama hanyar cikin Lagos in domin auko Meema. _Yasaar_ Yana juya kan mota bai tsaya ko ina ba sai makarantar su Meema, kasancewar ya san sai da pass ake aukar ko wani alibi, tun kwana biyu kamun yau ya nemi sample na pass in ya buga exactly irin sa tare da sunan Meema a jiki. Shiyasa ko da ya isa bai sha wahalar samun Meeman ba bayan ya sharara masu aryar uwar tana fitowa daga makaranta yayin kawo Meeman ta gamu da hatsari mai muni kuma yanzu haka tana asibiti bata san inda kanta yake ba, shiyasa ya zo tafiya da Meeman. Sosai shugabar makarantar ta nuna jimami a kan haka tare da tausayawa Meeman, don ita ma ta san irin auna da sha uwar da ke tsakanin Meeman da mahaifiyarta, musamman ba dai Meema don duk labarinta ba ya wuce mummyna kaza, mummyna kaza. Har wajen motar Yasaar classroom teachern su Meema da shugabar makarantar ta rako Meema da ke wa Yasaar kallon ban sanka ba, sai dai ta yi shuru ne kawai ganin pass in da zai bada damar aukarta wanda mummynta ne kawai ke da shi a hannunsa, sannan kuma da cewar da aka mata mummyn ce ta ce a auko ta, sai dai ba su fa a mata aryar da Yasaar ya sharara masu ba gudun kada hankalinta ya tashi. Bayan ficewarsa da kamar mintuna ashirin da biyu, motar Informer in Jawaad ya yi parking a ofar gate in makarantar tare da fitowa daga cikin motar ya nufi gate in ya kwankwasa. Mai gadi ya bu e tare da tambayarsa lafiya, sai ya ce masa ya zo wajen shugabar makarantar ne. Hakan da mai gadi ya ji, sai ya bu e masa aramar ofar ya shiga. Kai tsaye office in shugabar makarantar ya nufa, cikin sa a kuwa ita ka ai ce a ciki. Sai ya nemi izinin shiga ya shiga ciki. Da hannu ta yi masa nuni da wajan zama a aya daga cikin kujerun da ke gaban teburin da ta aje hannunta biyu a kai fuskanta fa e da murmushi. Sai da ya zauna sannan ya gaishe ta cikin harshen turanci. Cike da sakin fuska ta amsa sannan ta tambayesa abunda ke tafe da shi. Dogon bayanin da ya mata akan abunda ke tafe dashi ne ya saka wani siririn zufa ya soma biyo bayan kunnanta zuwa wuyanta har cikin rigarta duk da kuwa Ac da ke aikin cikin kantameman ofishin. Hankalinta bai ure tashi ba, sai da ta ga ya ajiye mata plastic pass in Meeman a kan teburinta. auka ta yi ta shiga arewa pass in kallo hankalinta na tashi kuma a lokaci aya ta shiga ru u da kokwanta shin wani pass ne a ciki na gaskiya, wanda Yasaar ya kowa ko kuwa wannan da ke ri e a hannunta. Shi kuwa ganin irin kallon zargi da rashin amincewar da take masa, sai ya gyara zama tare da fa in, "Domin tabbatarwa, ki duba file alibar taki ki auko Number in mahaifiyar sai ki kira domin ki tabbatar." Sosai shugabar makarantar ta ji da in wannan idea in. Cikin sauri ta soma duba numbers in files dake cikin wani dogon drawer har ta kawo kan na Meema ta auko ta dawo ta zauna tare da kwashe number in a wayarta ta danna kira. Ringing biyu Laushi ta aga ganin kira daga makarantarsu Meeman. "Madam ke ce kika turo wani ya zo aukar arki a makaranta yanzu? Gashi nan a gabanmu yanzu haka," shugabar makaranta ta fa i cikin harshen turanci bayan kammala gaisuwar da suka yi. "Eh, ni ce. Don Allah ku bashi ita yanzu, don rayuwar yarinyar bai ciki tsaro," Laushi ta fa i cikin sauri. "Jesus Christ!" Fa in shugabar makarantar bayan ta mi e tsaye, kasancewarta Christian. Cikin tashin hankali Informer shima ya mi e da sauri yana kallonta. Laushi kuwa da ihun Jesus Christ ya sauka a dodon kunnenta, duk da bata san ainahin abunda ke faruwa ba, jikinta ne ya hau wani irin tsuma, nan da nan kanta ya sara, zazza i mai zafi ya shiga rufe jikinta........... (Hmmmmmm #Meemah #Laushi #Yasaar #Sabo da Kaza #Jawaad #My Destiny addarata #Matar Sayyadee 08128755583 [7/8, 8:43
Chapter 62 · 0% Book details