Sashe 127
My Destiny Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ba zaka iya sauke hakkinta ba, sai dai Allah ya yi maka taimako ya kuma ba ka dacewa . Imam Sajjad haka ya kasance mai kiyaye hakkin uwa, an taba tambayarsa me ya sa ba ka cin abinci tare da baabarka? sai ya ce: Ina jin tsoron kada in riga baabata daukar wata loma da ita take so, sai ya kasance na saba wa abin da take so da wannan! Imam Sadik (a.s) yana cewa; "Wani mutum ya zo wajen manzon Allah (s.a.w) sai ya tambaye shi ya ma'aikin Allah! Wane makusancina ne zan yi wa alheri? Sai ya ce: Baabarka. Ya sake tambaya: bayan nan? Sai ma'aikin Allah ya ce: Baabarka. Sai ya sake tambayaka a karo na uku. Sai ma'aikin Allah ya ce: Babarka. A karo na hudu Sai ma'aikin Allah ya ce masa: Babanka . Amma kada mu manta irin wannan girmamawa ba mai cancantar ta sai uwa da ta dauki nauyin shiryar da 'ya'yanta ta sha wahala wajen nuna musu hanyar daidai ba wacce ta wulakanta su ba ta watsar da su babu wani tausayi ko damuwa da abin da zasu iya kasancewa nan gaba. Yaron da bai samu soyayya da kauna daga uwa ba, zai taso tabbas cikin matsalolin rayuwa iri-iri na tunani, kuma a nan gaba zai iya kasancewa daga cikin wadanda ba zasu iya fahimtar ma'anar tausayi ga iyaye ko al'ummarsu ba, don haka iyayen da suka yi masa irin wannan tarbiyya suna kawo wa al'ummarsu wani bala'i ne. Game da girmama uba kuwa Imam Sajjad yana cewa: "Amma hakkin babanka ka sani shi ne asalinka kuma ba don shi ba, da babu kai, kuma duk wani abu da kake gani gareka da yake kayatar da kai, to ka sani babanka ne mafarin wannan ni'imar gareka, sai ka gode wa Allah, ka gode masa gwargwadon wannan. Babu karfi sai da Allah" . Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: "Addu'ar mutane uku tabbas abin amsawa ce; 1- Addu'ar wanda aka zalunta; 2- Addu'ar matafiyi; 3- Addu'ar Uba ga dansa ; Sannan akwai fadin Ubangiji game da iyaye da cewa: Ya hukunta kada a bauta kowa sai shi kuma a kyautata wa iyaye, suna manya ne ko kuma dayansu, Ubangiji ya hana a ce musu tir ko kaico, sannan ya yi umarni da a gaya musu magana mai girma da girmamawa. Kuma akwai bayanai da suke nuni ga cewa; wadanda suke cutar da iyayensu suna nesa da rahamar Allah kuma suna cikin azaba a lahira. Abu Walad Hannad ya tambayi Imam Sadik (a.s) game da ma'anar fadin Allah (s.w.t): "Ku kyautata wa iyaye"? sai Imam Sadik (a.s) ya amsa masa da cewa: "Kyautatawa a nan tana nufin ku yi musu kyakkyawar mu'amala, kada ku tilasta su su biya muku bukatunku koda kuwa masu kudi ne. Kuma ku kula da halayensu da matsalolinsu, shin Ubangiji madaukaki ba ya cewa ba zaku iya samun kyakkyawa ba har sai kun ciyar daga abin da kuke so? Sannan sai Imam Sadik (a.s) ya ce: "Koda kuwa sun tsufa kada ka sake ka yi musu mafi kankantar wulakantawa, sannan kada ka daga murya a kansu, wato koda sun bata maka rai kada ka wulakanta su, idan suka dake ka to kada ka yi kara a kansu, kada ka fadi magana mai zafi, ka gaya musu magana ta girmamawa; wato ka yi musu magana mai taushi da nuna kauna kamar ka ce musu Allah ya ba ku hakuri, wannan shi ne fadin alheri. Amma da Allah madaukaki yake cewa: Ka shimfida musu fukafukin rusunawa don tausayi da kauna, wato ka tausasa zukatansu da kallon tausasawa da tausayawa, kuma kada ka taba daga murya a kan tasu, kada ka sanya hannunka a kan nasu, kada ka shiga gabansu yayin tafiya" . A wata ruwayar Imam Sadik (a.s) yana cewa: "Me zai hana wani mutum musulmi ya kyautata wa iyayensa suna raye ne ko suna mace! Ya yi musu salla, ya bayar da sadaka don su, ya yi musu hajji da azumi, kuma ladan nan kamar yadda za a ba wa iyayensa shi ma fa haka nan za a ba shi, haka nan saboda wannan al'amari da yake ji na alheri ga iyaye Allah zai ba shi lada mai yawa. Kaunar batattun iyaye Mu'ammar dan Khallad ya tambayi Imam Ridha (a.s) cewa: Shin zai iya yi wa iyayen da ba bisa tafarkin gaskiya suke ba addu'a? Sai Imam ya ce: Ka yi musu addu'a kuma ka yi musu sadaka, kuma idan suna raye ba su san hanyar gaskiya ba to ka kyautata musu! Domin manzon Allah (s.a.w) ya ce: Ubangiji ya aiko ni da rahama ne da tausayawa, ba da tsanantawa da cutarwa da rashin kyautatawa ba . Kyautata wa iyaye yana daga alamomin sanin Allah madaukaki da girmansa, domin babu wata ibada da take gaggauta kusantarwa zuwa ga Allah fiye da kyautatawa iyaye, domin hakkin iyaye reshe ne na hakkin Allah madaukaki. Amma da sharadin kada iyaye su kautar da 'ya'yansu daga tafarkin gaskiya da shiriya, su ba su tarbiyya sahihiya mai amfani da inganci, kuma ba su canja yakinin 'ya'yansu da kokwanto ba, ba su damfara su da duniya ba maimakon Allah (s.w.t) da gudun duniya. Amma idan iyaye suka kauce wa tafarkin Allah madaukaki to saba musu zata kasance ibada ce, domin ba a saba wa Allah domin biyayya ga abin halitta, kamar dai yadda Allah madaukaki ya ce: "Idan suka tilasta maka ka yi shirka da ni da wani abu wanda ba ka san shi ba to kada ka yi biyayya garesu" . Daga nan zamu iya fahimtar cewa girmama uwa da uba dole ne ya kasance ba a cikin abin da ya saba wa Allah ba, domin babu biyayya a kan bata da sabon mahalicci madaukaki, amma kuma duk da haka ba a yarda da yi musu wulakanci da mummunan halaye ba, dole ne kuma a girmama su ko suna da imani ko ba su da shi. Kuma Imam Bakir (a.s) a game da haka ya kawo mana magana mai gaskiya abin gaskatawa da cewa; Ubangiji madaukaki bai toge kowa ba game da abubuwa uku: 1- Kiyaye amana ga kowa koda kuwa kafiri ne; 2- Cika alkawari ga kowa koda kuwa ga mutumin banza; 3- Kyautata wa iyaye koda kuwa na gari ne ko batattu ; A takaice muna iya fahimtar cewa; musulunci ya karfafa yin alaka da juna tsakanin 'yan'Adam kuma ta wannan hanyar ne zai kiyaye kasantuwar al'ummu a matsayin tsintsiya madauri daya, kuma ya samar da wata nau'in hadin kai tsakanin al'umma gaba daya da kara mata dogaro da juna. Sabanin al'ummar da babu koyarwar addini a cikinta da dan'Adam ba shi da wata kima, a nan ana daukar dan'Adam kamar wani kaya ne da za a yi amfani da shi domin cimma burace-buracen duniya kawai, sannan kuma babu batun maganar kimar dan'Adam balle maganar dogaro da juna. A irin wadannan wuraren babu maganar kimar kyawawan halaye kamar kyautata wa iyaye da sadaukar da kai, da zabar wani a kanmu, da kunya, da kame kai, da sadar da zumunci, da mutuntaka, da daukakar rai. Sanin Hakkin Iyaye Godiya ga wanda ya yi mana ni'ima wani al'amari ne na dabi'ar halittar mutum, kuma hankali ya karfafe shi, don haka ne ma Allah madaukaki ya umarci 'ya'ya da su yi godiya ga wahalhalun da iyaye suka yi na dawainiyarsu a fagage daban-daban, Allah madaukaki yana cewa: "Mun yi wasiyya ga mutum da iyayensa, babarsa ta dauki cikinsa cikin rauni a kan rauni, kuma yayensa cikin shekaru biyu, (don haka) ka gode mini da iyayenka zuwa gareni zaku koma" . Kuma akwai aya mai tsawo a cikin Kur'ani da ta yi magana kan hakan a surar ahkaf wacce take nuni da wasiyyar da aka yi wa mutum na kyautata wa iyayensa, sakamakon irin wahalhalun da suka sha kansa. Sanyaya Halaye Ga Iyaye Kallon iyaye da tausayawa yana daya daga cikin abubuwan da shari'a take ganinsu a matsayin ibada, manzon rahama (s.a.w) yana cewa: Kallon fuskar iyaye ibada ne . A wani hadisin mai girma da daukaka yana cewa: Babu wani mutum da zai kalli iyayensa da soyayya da kauna da tausayawa sai Ubangiji ya ba shi ladan hajji karbabbe a kowane kallo da ya yi, sai aka tambayi manzon Allah (s.a.w)! Idan da mutum zai kalli fuskar iyaye sau dari yana da wannan ladan kuwa? Sai ya ce: Haka ne, idan ya yi hakan sau dari a rana yana da ladan hajji dari da zai samu . Nisantar Tsanantawa Ibrahim dan Mahzam yana cewa: Wata rana na fito daga wajen Imam Sadik (a.s) a madina na tafi gidana, babata tana rayuwa tare da ni, sai ta yi jayayya da ni kan wani al'amari kuma na gaya mata magana maras dadi da ba ta dace ba. Wayewar garin wannan ranar bayan sallar asuba sai na sake zuwa wajensa (a.s). Yayin da nake shigowa ba tare da na ce komai ba sai Imam (a.s) ya ce da ni: Ya kai dan Mahzam! Daren jiya ka yi magana mai zafi mai kaushi ga babarka, shin ba ka sani ba cewa cikinta ne ya zama gidanka tsawon lokaci, da goyonka da ta yi, kirjinta ya zama abincinka, saboda me kake yi mata magana mai zafi, kada ka sake yin hakan ! Godiya Ga Iyaye 'Ya'ya na gari kodayaushe suna kokarin ganin sun gode wa iyayensu, kuma wannan aiki ne mai matukar muhimmanci da amfani. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: Hutu a kan gado saboda hidima da kyautata wa iyaye wanda yake sanya su farin ciki, da kuma haduwa da su da fuska mai walwala ya fi yaki da takobi a tafarkin Allah idan wani ya bakanta wa iyayensa to sallarsa ba za a karbe ta ba. Haka nan Imam Sadik (a.s) ya ce: Idan kana son ka samu tsawon rayuwa to ka faranta wa iyayenka. Kiyaye Mutuncin Iyaye Kiyaye mutuncin iyaye yana daga cikin hakkokin iyaye kan 'ya'yansu, wani lokaci wasu 'ya'yan sukan yi aikin da zai sanya cin mutunci da zagi ga iyayensu a cikin mutane, kuma wannan yana jawo wa iyayen jin bakin ciki da zubar mutunci. Don haka ne 'ya'ya su guji abin da zai kawo wulakanci ga iyayensu, a kan haka ne manzon rahama (s.a.w) yake cewa: Mutum ya zagi iyayensa yana daga manyan zunubai. Sai aka ce ya